SHEIK ja'afar masjid tiga

SHEIK ja'afar masjid tiga MAJMI'UL HIJIRATI LITTAHAFIZUL QUR'AN WASSUNNATI NABAWIYYA TIGA

16/09/2025
12/09/2025

. "Rayuwa ba ta girmama masu korafi, sai masu tashi su kirkiro mafita."

08/09/2025
06/09/2025

Ku kasance da Shafin Facebook na Tashar Africa TV3 domin kallon kaitsaye (Live) jeron gwanin laccocin nan duk Ranar Lahadi

Kungiyar Izala ta tara sama da miliyan ɗari da saba'in (N170,974,512.50) sakamakon fatun layya.Kungiyar Izala ta tara sa...
06/09/2025

Kungiyar Izala ta tara sama da miliyan ɗari da saba'in (N170,974,512.50) sakamakon fatun layya.

Kungiyar Izala ta tara sama da miliyan ɗari da saba'in (N170,974,512.50) sakamakon fatun layyan data gabata. A safiyar asabar ɗinnan Shugaban kungiyar Izala Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau, ya karɓi sakamakon kwamitin tattara fatun layya na shekarar 1446/2025, wanda shugaban kwamitin Malam Lamara Azare da Yan majalisar sa s**a miƙa a lokacin da ake gudanar da meeting na majalisar ƙasa a ɗakin taro na JNI a birnin Kaduna.

Ga yadda jadawalin ko wace jaha ta samar na fatun layya.

Kuɗin Fata da resiti .......

1-Kaduna N23,000,400
2-Kebbi N21,127,900
3-Sokoto N18,402,150
4-Bauchi N12,119,082.50
5-Zamfara N10,554,650
6-Adamawa N10,173,800
7-Niger N9,497,000.00
8-Katsina N8,465,700
9-Taraba N7,721,000.00
10-Abuja FCT N6,209,800.00
11-Nasarawa N5,927,550.00
12-Kano N5,544,500.00
13-Jigawa N4,935,825.00
14-Gombe N4,848,600.00
15-Lagos N4,449,587.00
16-Borno N3,094,300.00
17-Kogi N2,812,400
18-Oyo N2,490,565.14
19-Plateau N2,278,750.00
20-Kwara N1,787,169.56
21-Benue N1,721,959.00
22-Yobe N1,152,605.00
23-Ogun N639,622.40
24-Rivers N421,200.00
25-Delta N300,000.00
26-Ondo N235,250.95
27-Enugu N156,800.00
28-Edo N156,000.00
29-Osun N221,774.80
30-Anambra N108,500.00
31-Bayelsa N106,200.00
32-Ebonyi N100,000.00
34-Abia N50,000.00
35-Akwa Ibom N35,000.00
36-Imo N29,000.00
37, Cross Rivers N15,000.00

Jimilla N170,974,512.50.

Jibwis Nigeria

05/09/2025
05/09/2025
05/09/2025
05/09/2025

Annabi ﷺ ya ce:
"Mafi falalar ranaku ita ce ranar Juma’a. A cikinta ne aka halicci Ādam, a cikinta aka shigar da shi aljanna, a cikinta aka fitar da shi daga aljanna, kuma ba taɓa zuwa sa’a (ƙiyama) sai a ranar Juma’a."
📚 (Muslim, Abu Dawud, Nasa’i)
_______________________
DAGA MASJIDUL SHEIK JA'AFAR TIGA ✍️✍️

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah Imam Dokta Abdullahi Bala Lau , Shugaban majalisar malamai...
04/09/2025

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah Imam Dokta Abdullahi Bala Lau , Shugaban majalisar malamai Dokta Ibrahim Jalo Jalingo da daraktan ‘yan agaji Injiniya Mustapha Imam Sitti na farin cikin gaiyatar jama’a zuwa wa'azin ƙasa a garin kaduna tare da gagarumin taron gabatar da fassarar littafin WHERE I STAND “nan ne matsaya ta” da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya wallafa da Dokta Ibrahim Jalo Jalingo ya fassara zuwa Larabci. Sai littafin AL’AKIDATUS SAHIHA, AHALARI, IZZIYYA, RISALA da ISHMAWI da Dokta Jalo ya juya daga zube zuwa wake.

Za a gudanar da gabatarwar ranar asabar 6 ga watan nan na Satumba 2025 da karfe 9am a dakin taro na Umaru Musa ‘YAR’ADUA HALL da ke Murtala Muhammed Square Kaduna.

Babban bako na musamman, mai girma shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu GCFR

Mai masaukin baki, Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani

Iyayen taro mai alfarma Sarkin musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar da mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli

Babban mai gabatarwa Sanata Dokta Abdul’aziz Yari

Mai bitar littattafan babban limamin masallacin Sultan Bello Sheikh Muhammad Sulaiman.

Sai Dokta Ahmad Gumi zai yi magana a madadin iyalan marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Manyan baki gwamnoni, shugabannin kamfanoni, tsoffin gwamnonin jihar Kaduna Dokta Ahmed Muhammad Makarfi, Dokta Ramalan Yero da Malam Nasiru Elrufai sai kuma almajirai da daliban marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Kazalika, kungiyar na gaiyatar jama’a zuwa taron karawa juna ilimi da tambayoyi da amsoshi kan illar masu ikirarin bin Kur’ani zallah wato ‘yan Ƙala ƙato da za a gabatar a dakin taro na Umaru Musa ‘Yar adua da ke Murtala Square Kaduna ranar Jumma’a 5 ga watan nan na Satumba 2025 daga bayan sallar la’asar.

Dokta Ibrahim Disina zai jagoranci taron da kulawar shugaban bita da taruka na kasa Dokta Abubakar Abdulsalam Baban Gwale. Masu jawabi sun hada da Sheikh Lawal Shu’aib Triump, Sheikh Abubakar Mazan Kwarai da Sheikh Musa Muhammad Dankwano.

Gabanin nan kwa

03/09/2025

Yadda Makaje Sallar Asubah Da Sauran Bacci A Idonmu Saboda Allah!
ilahu Ya Karɓi Buƙatunmu Cikin Sauƙi Aamin.🙏🏿🤲🏿

01/03/2025

Alhamdulillahi masallaci Yana Kara samun ci gaba .

ansiyar da shagon da aka mallakawa masallaci #200,000

Sannan masallaci ya mallaki ginin da yake gefensa ta bangaren arewa Alhamdulillahi wannan ba karamin ci gaba bane Muna Kara godewa Allah da wannan ni'ima da yayi mana .. sannan Muna godiya GA wannan kungiya da take iya bakin kokarinta wajen ganin ta kawo mana ci gaba Allah ya karfafi gwuiwoyinsu ameen........ sheikh ja'afar tiga

Send a message to learn more

Address

JOS Road
Kano
70010

Telephone

+2348148734165

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SHEIK ja'afar masjid tiga posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share