10/12/2024
JAN HANKALI GAME DA SALLAR ASUBAH .... KARANTA ✍️
• Sallar Asubah itace Mafi Alkhairi Fiye da Bacci , Mu rage Bacci Don Mu ribanta da Goben mu,
• Bacci Amsawar Zuciya ne Ita Kuwa Sallah Amsawar kiran Ubangiji ne
• Shi Bacci mutuwa ne Ita Kuwa Sallah Rayuwa ce
• Shi Bacci Hutu ne na gangar Jiki Sallah Kuwa hutu ne na Ruhi
• Bacci da Mumini da kafiri Duk Suna Yinsa Ita Kuwa Sallah Musulman kwarai sune Kadai ke yinta.
Masu tashi lokacin ketowar Alfijiri sun Rabauta, Fuskarsu kuma ta Haskaka Goshinsu kuma Yayi Haske da Kyalli , Lokacinsu kuma yayi Albarka, idan Kana cikinsu toh Ka godewa ALLAH da Ya Fifita ka, Idan Kuwa baka cikinsu toh Ka Roki ALLAH Ya saka Cikin su,
MENENE YAFI ALFIJIR KYAU ?
• Farillarsa {Sallar Asuba} zata Saka ka Acikin Kulawar Ubangiji
• Sunnarsa (Rak'ataanil fajr) tafi Duniya da Abinda Ke Cikinta {Hadeeth}
•️ Ita Sallar Asubah da Mala'iku masu aikin dare da Mala'iku masu aikin safe duka suna Halartar ta,
Ya kai Dan'uwa, Ya ke Yar'uwa musani Duk Wanda Ya rayu Akan wani aiki toh akansa zai Mutu, Wanda Ya Mutu kan wani Aiki kuma Akansa za'a tashe shi.
Idan ka Karanta wannan sako kuma kayi aiki Dashi zaka samu Ladan Aikin ka, idan kuwa katura ma wasu suma sukayi Aiki Dashi toh Ladanka zai ninku A Wurin ALLAH in shaa ALLAH.
Kada ka 6oye ilimi, ka Bayyana shi, Zaka Samu Kyakkawan Sakamako,
Kuyi murna ya ku Masu Sallar Asubahi