14/10/2025
SABON KUDIRIN DOKAR ZABE: ZA A GUDANAR DA ZABEN 2027 A WATAN NUWAMBA 2026, AN RAGE LOKACIN SHARI’AR ZABE
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da sabon Kudirin Dokar Zabe (Gyara) na 2025, wanda ke nufin gudanar da babban zaben kasa a watan Nuwamba 2026, kafin karewar wa’adin gwamnati a ranar 29 ga Mayu, 2027.
Rahoton da jaridar The Historica Nigeria ta wallafa ya bayyana cewa, wannan sabon kudiri yana da nufin bai wa kotunan sauraren karar zabe damar kammala dukkan shari’o’in da s**a shafi zabubbuka kafin ranar rantsuwar sabuwar gwamnati.
Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na gwamnoni kafin kwanaki 185 da karewar wa’adin gwamnati, wato a kusan watan Nuwamba 2026.
An rage wa’adin sauraren karar zabe daga kwanaki 180 zuwa 90 ga kotunan farko (Tribunal).
Haka kuma an rage lokacin daukaka kara daga kwanaki 90 zuwa 60, wanda ke nufin dukkan karar zabe za su kare cikin kwana 185
Sabon kudirin dokar ya kuma kunshi sabbin abubuwa k**ar haka:
Zaben Farko (Early Voting) ga jami’an tsaro, ma’aikatan INEC, manema labarai da masu sa ido, kafin kwanaki 14 da ranar zabe.
Tura sak**akon zabe ta hanyar lantarki (electronic transmission) tare da tabbatar da tsaro da gaskiya.
Hukunci mai tsanani ga duk wanda ya raba takardar zabe ko sak**akon da ba shi da tambarin hukuma.
Ana kuma kokarin daidaita lokaci domin gudanar da zaben shugaban kasa, gwamnoni da majalisu a rana guda.
Masu gabatar da kudirin sun bayyana cewa gyaran dokar zai taimaka wajen:
Kare jinkirin shari’ar zabe da ke ci gaba bayan rantsuwar gwamnati.
Samar da ingantaccen tsarin gaskiya ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Rage kudin gudanar da zabe ta hanyar hada dukkan zabuka a lokaci guda.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta hannun Farfesa Abdullahi Zuru, ta nuna goyon bayanta ga bangaren da ya shafi amfani da fasahar lantarki wajen tura sak**ako.
Sai dai masana sun yi gargadin cewa wannan sabon tsarin zai bukaci cikakken shiri daga INEC da kotuna, musamman wajen kayan aiki da horar da ma’aikata, domin tabbatar da adalci.