12/04/2025
Shehu Usman Ɗanfodio Kira Yayi A Dawo Tafarkin Allah Sheikh Zakzaky Shima Kira Yake A Dawo Kan " La'ilaha Illallah Muhammad Rasulallah"
- Cewar Sheikh Muhammad Abbare Gombe.
Babban Taron Mu'utamar Na Ƙasa Da Ƙasa "International Conference" Ya wanda Harkar Musulunci Ƙarƙashin Jagorancin Sheikh Zakzaky (H) suke gudanarwa a garin Kano wanda aka masa take da "Nigeriya Ina Mafita" ya cigaba da gudana a yau Juma'a 11 ga watan Afrilu 2025.
A yau Juma'a an fara taron ne da bude taro da addu'a k**ar yadda aka saba kullum wanda Sheikh Rabi'u Funtuwa ya Gabatar sannan karatun Alkur'ani Mai Girma da aka saurara.
An Gabatar da Dr Sunusi Abdulƙadir wakilin Ƴan uwa na Kano domin ya gabatar da jawabin maraba da baki wanda ya fara da cewa, wannan itace rana ta biyu kuma rana ce mai muhimmanci ga dukkan musulmai da ta kasance ranar Juma'a.
Yace, shi wannan Mu'utamar zai fitar da yananin da ake ciki ga halin da al'umma suke ciki, to ! Menene mafita? Wannan mafita da muke magana akai shine su waye zasu kawo ta ? Kuma a ina za'a same ta ? Don haka wannan taro muna fatan cewa zamu saurari jawabai daga malamai domin mu san ina mafitar take sannan su waye zasu kawo mafita ga Al'umma k**ar yadda Maulan mu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) kullum yake kokari kawo wannan mafita ga Al'umma baki ɗaya.
Mau'du'in Farkon bayan jawabin Dr. Sunusi Abdulƙadir shine "Jihadin Shehu Usman Ɗanfodio Da Kiran Malam (H) wanda Sheikh Muhammad Adamu Abbare Wakilin yan'uwa na garin Gombe, cikin jawabinsa yace, Zai fara da bayani akan jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo, Allah madaukakin sarki yayi ma wannan al'umma tagomashi da wannan bawan Allah Shehu Usmanu Danfodiyo, mahaifinsa masani ne sosai har ance in aka cewa mutum Fodio wato wanda ya gaji sani a wajen iyayensa.
A lokacin da Shehu Usmanu Danfodiyo yazo ya tarar da mutane kala-kala akwai maguzawa da kiristoci da kuma Musulmai wanda suke da ilimi na addini musulunci. A wannan lokaci abin da aka rasa shine al'umma tana hannun wasu Mutane azzalumai, wannan ya haifar da lalacewar al'umma sata ne , kisa ne , da kuma k**a karya. A lokacin Shehu Usmanu Danfodiyo sai yayi kira da a dawo musulunci, saɓanin yadda ake cewa jihadi kawai yayi da takwabi.
Shehu Usmanu Danfodiyo yayi gwagwarmaya irin ta dukkan Annabawa irin na Annabi Ibraheem Annabi Musa da Annabi Muhammad (Saww) wanda ya tarar da mugayen shuwagabanni suna zaluntar Al'umma da azabtar da su, ya tashi tsayin daka wajen yin da'awar a dawo hakiƙanin musulunci. Daga cikin Almajiran Shehu Usmanu Danfodiyo sun samu tarbiyya daga wajen sa wanda a karshe da su ne yayi Amfani wajen kawo gyara.
A irin wannan halin da muke ciki menene mafita ? Itace kiran da Maulan mu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) kuma mahanga irin na Shehu Usmanu Danfodiyo irin tane na Maulanmu Sayyid Zakzaky (H), su Malam sun ɗaga tutar " La'ilaha Illallah Muhammad Rasulallah" wato ya tsaya akan "Babu Hukuma Sai Ta Allah". Wannan abin da Maulanmu Sayyid Zakzaky (H) yayi shine ya daga hankalin mahukuntar wannan ƙasa, s**a tashi haiƙan tun a farkon wannan gwagwarmaya domin suga sun kawo karshen wannan kira . Manufar Malam shine a dawo zuwa ga Allah a koma ga Musulunci.
Sheikh Muhammad Abbare ya rufe jawabinsa ne da cewa, "Shehu Usmanu Danfodiyo Ya Tafi Shehu Usmanu Ya dawo Shine Malam (H)" mu kuma aikin mu shine kawar da Ɓarna da zalunci, shi yasa aka ce mana muna sallah, muna azumi muna sada zumunci, muna aikata aiki na Alkhairi, ko da baka kai ga Shahada ba to zaka koma gaban Allah tsaf. Saboda yanzu zamani ne na fata , ko mutum yazo anyi gwagwarmayar nan dashi ko mutum ya zame wannan gwagwarmayar sai ta tabbata, kuma ko anƙi ko an so wannan da'awa sai ta tabbata, kuma za'a kai ga Nasara.
KanoConference2025
11-April-2025.