14/10/2025
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya halarci zaman majalisar wakilan tarayya a ranar Talata domin shaida yadda wasu ‘yan majalisar jam’iyyar PDP uku s**a koma jam’iyyar APC. Wadanda s**a sauya sheka su ne Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da Sadiq Ango Abdullahi. Kakakin majalisar, Abbas Tajudeen, ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar.
Majalisar ta dakatar da wasu ayyuka nata domin ba gwamnan damar halartar zaman, inda daga bisani ya jagoranci sabbin ‘yan jam’iyyar APC wajen gaisawa da kakakin majalisar tare da daukar hoto. Wannan lamari ya ja hankalin ‘yan majalisar da dama da ke cikin zauren.
Sai dai jagoran ‘yan adawa a majalisar, Kingsley Chinda, ya soki wannan sauya sheka, yana mai bukatar kakakin majalisar ya bayyana kujerun mutanen a matsayin babu mai rike da su bisa tanadin sashe na 68 na kundin tsarin mulkin kasa.