New media 24

New media 24 New media 24
Tasha ce da take kawo muku sahihan labarai, tare da tsage gaskiya ba tare da son rai ba. Idan kuna da labari ku turo mana a 07038603678

“Da yardar Allah, talakawa za su zaɓi APC.” — Sanata Aliyu Wamakko, tsohon Gwamnan Sokoto, a wata hira da RFI Hausa.
27/08/2026

“Da yardar Allah, talakawa za su zaɓi APC.” — Sanata Aliyu Wamakko, tsohon Gwamnan Sokoto, a wata hira da RFI Hausa.

Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta ce har yanzu ba ta yanke shawarar ɗan takarar da zai yi mata takarar gwam...
27/08/2026

Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta ce har yanzu ba ta yanke shawarar ɗan takarar da zai yi mata takarar gwamnan Jihar Kaduna a zaɓen 2027 ba, duk da ikirarin da wasu ’yan takara ke yi.

New Media 24 ta rawaito cewa, wannan na cikin bayanan da Shugaban NDC na Jihar Kaduna, Evangelist Mordecai Ibrahim, ya bayyana a wani taron manema labarai da ya gudanar a Kaduna.

Mordecai ya ce har yanzu ba a yanke shawara tsakanin tsohon Sanata Danjuma La’ah da Lauya Mohammed Sani Abbas ba, yana mai cewa babu ɗayansu da jam’iyyar ta amince da shi a hukumance a matsayin ɗan takararta.

Ya ce batun ɗan takarar jam’iyyar har yanzu yana nan daram ba tare da an warware shi ba a matakin jiha da na ƙasa, bayan da shi kansa ya janye daga takarar gwamna.

A halin yanzu, La’ah da Abbas na ci gaba da ikirarin cewa su ne halastattun ’yan takarar NDC a Kaduna, lamarin da ya jefa jam’iyyar cikin takaddama kan tikitin takarar gwamna na 2027.

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce rashin kwarewar wasu daga cikin jami’an da ke aiki a gwamnatin Shuga...
27/08/2026

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce rashin kwarewar wasu daga cikin jami’an da ke aiki a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janyo wa shugaban ƙasar matsaloli da kuma abin kunya.

New Media 24 ta rawaito cewa, Ndume ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na Arise TV, inda ya ce wasu daga cikin mutanen da ke kusa da shugaban ƙasar ba su da cancantar mukaman da suke riƙe da su.

Sanatan ya yi gargadin cewa idan Shugaba Tinubu bai ɗauki kwakkwaran mataki kan irin waɗannan jami’ai ba, za su ci gaba da jefa gwamnatinsa cikin matsaloli. Ya danganta kalamansa da gano wasu hukumomin bogi da s**a yi ikirarin aiki a ƙarƙashin gwamnatin tarayya.

Ndume ya ce da a ce akwai ƙwararrun mutane a wasu muhimman wurare na gwamnati, da ba za a samu irin wannan lamari na hukumomin bogi yana faruwa ba.

Ya kuma bukaci shugaban ƙasar da ya sake duba waɗanda ke taimaka masa wajen tafiyar da gwamnati, domin tabbatar da cewa ƙwararru da mutanen da s**a dace ne ke riƙe da muhimman mukamai.

“Idan Hon. Abdulmuminu Kofa ne yake ba da mulki, ba ma son ya ba mu.”
27/08/2026

“Idan Hon. Abdulmuminu Kofa ne yake ba da mulki, ba ma son ya ba mu.”

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), Ibrahim Musa Gusau, ya tabbatar da yin murabus daga matsayinsa na shuga...
27/08/2026

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), Ibrahim Musa Gusau, ya tabbatar da yin murabus daga matsayinsa na shugaban hukumar.

New Media 24 ta rawaito cewa, Gusau ya tabbatar da murabus din nasa ne a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Alhamis 27 ga Agusta 2026, lamarin da ya kawo karshen jagorancinsa na NFF.

Murabus din ya zo ne a yayin da ake fuskantar matsin lamba kan shugabancin NFF sakamakon koma-bayan da kungiyoyin kwallon kafa na Najeriya s**a samu, ciki har da rashin samun tikitin shiga gasar Kofin Duniya ta mata ta 2027 da kuma rashin Super Eagles a gasar Kofin Duniya ta 2026.

Rahotanni sun kuma ce wasu mambobin kwamitin zartarwa na NFF sun ajiye mukamansu, yayin da ake ci gaba da fuskantar tambayoyi kan yadda aka tafiyar da kudaden da gwamnatin tarayya ta bai wa hukumar.

Sai dai bayanan da s**a fito ya zuwa yanzu ba su yi cikakken bayani kan dalilan da Gusau ya bayar na yin murabus din ba, yayin da matakin ya kara jefa shugabancin kwallon kafar Najeriya cikin wani sabon yanayi.

Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya ta zargi tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atik...
27/08/2026

Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya ta zargi tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, da rikitar da matsayinsa kan shirin dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

New Media 24 ta rawaito cewa, wannan na cikin kalaman Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, wanda ya ce cikin mako guda an ji bayanai daban-daban daga ɓangaren Atiku kan yadda zai tafiyar da batun tallafin man fetur.

Onanuga ya ce Atiku ya kamata ya yi wa ’yan Najeriya bayani dalla-dalla kan abin da yake nufi da “tallafi na musamman”, musamman yadda za a aiwatar da shirin, waɗanda za su amfana da shi da kuma adadin kuɗin da zai ci.

Ya kuma kalubalanci ɗan takarar ADC da ya bayyana inda kuɗin shirin za su fito, da kuma irin tsarin da zai tabbatar da cewa tallafin bai sake zama nauyi ga baitulmalin gwamnati ba.

Atiku ya dage kan cewa matsayinsa bai canza ba, yana mai cewa zai dawo da “tallafi na musamman” idan aka zaɓe shi a 2027, domin rage tsadar rayuwa da dawo da ƙarfin sayen ’yan Najeriya.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya gargadi shugabannin jam’iyyar APC da su koyi darasi daga kuskuren ...
26/08/2026

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya gargadi shugabannin jam’iyyar APC da su koyi darasi daga kuskuren da PDP ta yi kafin zaɓen 2015, yana mai cewa kada jam’iyyar ta ɗauka cewa nasarar zaɓen 2027 ta riga ta tabbata.

New Media 24 ta rawaito cewa, Shekarau ya bayyana cewa a wancan lokaci PDP ta yi imanin cewa za ta ci gaba da mulkin Najeriya na dogon lokaci, duk da cewa tana da gwamnoni sama da 20 kuma ta shafe shekaru 16 tana mulki.

Ya ce duk da wannan ƙarfin da PDP ke da shi, ’yan Najeriya sun juya mata baya a zaɓen 2015, lamarin da ya ce ya kamata APC ta yi la’akari da shi wajen shirye-shiryenta na tunkarar zaɓen 2027.

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa ikon zaɓar shugabanni yana hannun talakawa, don haka babu wata jam’iyya da ya kamata ta ɗauka cewa za ta ci gaba da mulki saboda ƙarfinta ko yawan masu riƙe da mukamai.

Shekarau ya kuma yi kira ga jama’a da su fito da yawa domin kaɗa ƙuri’a, tare da duba cancanta, halaye, ƙwarewa da tarihin ɗan takara maimakon jam’iyya kawai, yana mai cewa rashin fitowar masu zaɓe na iya bai wa masu neman yin magudin zaɓe damar sauya sakamakon zaɓe.

“Ni ne na fara cewa Rarara ya yi digiri, kuma wallahi karya nake yi. Ko firamare bai yi ba.”
26/08/2026

“Ni ne na fara cewa Rarara ya yi digiri, kuma wallahi karya nake yi. Ko firamare bai yi ba.”

Hotunan zagayen Maulidin Annabi S.A.W a Kano, bisa jagorancin Sheikh Abdulgaffar Nasir Kabara.📸 Hoto: Bashir Musa Musdaf...
26/08/2026

Hotunan zagayen Maulidin Annabi S.A.W a Kano, bisa jagorancin Sheikh Abdulgaffar Nasir Kabara.

📸 Hoto: Bashir Musa Musdafah

“Shugaba Tinubu waliyyin Allah ne.” — Kwamared Ibrahim Wayya
26/08/2026

“Shugaba Tinubu waliyyin Allah ne.” — Kwamared Ibrahim Wayya

Address

Zoo Road
Kano
1122

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when New media 24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share