
17/06/2025
|RAN TANA CIKIN ƘASASHE 10 DA A DUNIYA BAZAKA TABA IYA MAMAYAR SU BA
Ga Dalilan Da S**a Yasa;
🎯 Geographical Position (Inda Allah Ya Ajiye Ƙasar)
Iran kusan zagaye take da tsaunuka, hamada, da kuma yanayin ƙasa da zaiyi wahala ka iya kutsawa ko mamayar ƙasar.
Ba irin su Iraq bace ko Libya ba ce. Ba za ka iya shiga ta sauƙi ba cikin ƙasar, za ka makale ne cikin tsaunuka da yanayin hamada da bazai bawa tankar yaƙi iya sarrafuwa ba.
"Ƙaddara ma ka wuce cikin Ƙasar Iran ɗin, toh kuma zaka haɗu ne da abu na biyu"
🎯 Yawan Sojoji Da Yan Sa Kai (Sojoji Da Yan Sa Kai Miliyan 20 Za Su Tashi Cikin Kwana Daya)
Iran na da rundunar soja mai yawa, amma mafi hatsari ita ce (Basij), wata rundunar soji ce ta fararen hula da za su iya fara aiki daga duk inda suke.
Su wannan rundunar na horar da su a salon yaƙin kwantan bauna, shiyasa duk ƙasar da take tunanin mamayar Iran toh bawai da iya sojin ƙasar da gwamnatin take faɗa ba. A'a gabaki daya mutanen ƙasar ne.
"Mu ƙaddara shima wannan ɗin bai zama matsala ba, toh muje zuwa na uku"
🎯 Asymmetric Warfare Masters (Suna da tsananin kwarewar gaske a salon iya yaƙi da waɗanda s**a fisu ƙarfi)
Iran sun kwana da sani ba za su iya fafata da ƙasashen turawa (NATO) kai tsaye ba, don haka sun haka ne tun kafin lokaci ya ƙure musu s**a horar da sojin su a salon yaƙin sari ka noƙe, da electronic warfare da fasaharamfani da drones.
Za su iya kutse su katse gabaki daya yanar gizon ku kamar yadda s**ayi jiya, su sauke satellite na duk ƙasar da s**a ga dama, da sauran dabarun saƙin kwantan bauna.
"Mu bar sa duk wannan bai zama matsala ba, toh mu tafi abu na huɗu"
🎯 Ba Kamar Yan Nigeriya Bane Da Bamu Da Wata Kaunar Ƙasa, Su Suna Da Ƙaunar Ƙasa Da Matsanancin Riƙo Da Aƙida Na Bala'i
Su fa ba wai suna kallon abin bane ma a iya kare mutuncin ƙasar suna kallon hakan a matsayin dole ne ma a addini, sannan idan kayi attacking na Gwamnatin su kamar kayiwa áddinin su na islama ne. Ya kake tunani yin yaƙi da ƙasar da malamai ne ke jagorantar