Sautus Sunnah

Sautus Sunnah Islamic Videos, reels, and hadith

CIKAKKEN BAYANI KAN WASIKAR SHEIK JA'AFAR Daga, Zainab Ja'afar Mahamud" Allahu Akbar...!Wata Wasika Mai Kwanan Watan 3\2...
02/12/2025

CIKAKKEN BAYANI KAN WASIKAR SHEIK JA'AFAR

Daga, Zainab Ja'afar Mahamud" Allahu Akbar...!

Wata Wasika Mai Kwanan Watan 3\2\2002 da Marigayi Sheikh Ja'afar ya rubutawa, yarsa Zainab ja'afar Mahmud, a lokacin da yake karatu a sudan. Ga abunda ita zainab ta rubuta a shafin ta ku karanta.

Shekaru 19 kenan da watanni mahaifina ya rubuto min wasikar nan daga qasar Sudan, lokacin yana karatun shi na masters degree a can.
Yau babu zato babu tsammani na ci karo da ita cikin wasu tsofaffin littafaina, ina karantawa sai na ke jin ina ma ina da damar da zan sake samun irin wannan wasika daga gareshi yanzu amma inaa!! Sai nake jin kamar yanzu ne ya rubuto min ita saboda gamammun sakonnin da ke cikinta da zansu amfane ni tsawon rayuwata.

Ina karantawa cike da tunanin irin yadda rayuwata ta kasance da shi a wancan lokutan, na yi rayuwa mai cike da kulawa, gata, tarbiyyantarwa, bada kariya, ilimantarwa, uwa uba kuma kauna ta musamman daga gareshi wadda ba zan taba mantawa da ita ba har na koma ga Allah😭😭

Ga Wasikar Malam \

Assalamu alaikum wa rahmatullah

Dafatan kina lafiya, yaya karatu? Ina fatan komai yana tafiya Kamar yadda ake fata,

Ina farin cikin sanar da ke cewa na isa Sudan cikin aminci da koshin lafiya, Amma kuma zan sake komawa Saudiyyah a karo na biyu domin yin aikin hajji,

Ina yi miki Wasiyya da TSORON ALLAH, a sarari ko a boye, ina kuma yi miki Wasiyya da yawaita TULAWAR AL'QUR'NI. Tare da kiyaye SALLOLIN FARILLAH, a kan lokaci, da kuma HIMMA wajen neman ILIMI da kuma HARDAR AL'QUR'NI

Haka nan kuma ina yi miji nasiha da BIYAYYA ga MAHAIFIYARKI da hakurin mu'amala da kannenki

Insha allahu zan dawo gida bayan aikin hajji

Na barki lafiya

Mahaifinki
Ja'afar Mahamud Adam
Khartoum Sudan.

Lallai rashin mahaifi babban gibi ne da babu mai iya cike wa mutum shi har abada!!!

Ubangiji Allah Ka ji kan mahaifanmu da suka rasu Ka sanya Aljanna ce makomarsu,

wadanda suke raye kuma ka kara musu lafiya da imani da tsawon kwana mai amfani amin.

Copied.

13/10/2025

Yadda Zaman Shura da Mallam lawal. Triumph
Ta Kaya.A Yau jihar kano.

16/09/2025

RAHIMAHULLAH 🤲🤲

15/09/2025

Allah Yasa Mudace🤲

15/09/2025

Tabbas Babu Wanda Yasan ghaibu Sai Allah ☝️

04/06/2025
01/06/2025

Allah yasa mudace 🤲🤲

01/06/2025

Allah ya jikan mallam 🤲🤲

Address

Naibawa
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sautus Sunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share