10/09/2025
Wane ne BATIJJANE
Shine Wanda ya karbi wuridin Dariqar Tijjaniyya a hannun muqaddami Tijjaniyya mai izini Yake kumayi kamar yadda tazo daga Shehu Tijjani Abul Abbas [RTA] daga manzan Allah [SAW]
Kiyaye Sharuɗanta Wajibine Ga Duk mai kiran kansa Batijja ne Dola ne Asameshi yanayin riko da wuridinta
Lazimin Safe da na yamma Istighfari 100, Salatin Annabi 100, La ilaha Illallahu 100
Sai Wazifa ita kuma sau daya akeyi kullum a Cikin jama’a ma'ana sharadi ne.
Zikirin juma'a sau daya Asati Bayan La'asar Ranar juma'a
Duk wadan nan zasuzo ne Bayan
Kaga batar da Sallolin Farilla a Cikin jam'i
Yawaita karatun Alqur'ani mai girma
Bin iyaye tare da kyautata musu
Sada zumunta sharadi ne
Nisantar duk abun da aka haramta. da kusantar duk abinda aka yi Umarni dashi
Wanda ya riki wannan shine Cikakken Batijjane Wanda ko Ya Watsar da wadan nan sharadi to ya sani ya ajiye Carbin Shehu Tijjani [RTA]
SHEHU Ibrahim Niasse [RTA] Yana Cewa:-
Ya kai muridi mai Neman shiga hadarar Ubangiji kayi Ladabi zahiri da badini da domin da shine Ake Hauhawar da mutum zuwa muqaman hadarar ubangiji da walittaka
Ka halarto da Shehinka Wanda kasami wusuli awajansa awajin Wuridinka Hakanan Shehinsa Shehu Tijjani RTA Hakanan Khalifansa Batare da kokwanto ba
Kalizimci huduri Cikin Allah da natsuwa hakanan kadaita daga barin Mutane nadan wani lokaci
Kanemi wanda zai tarbiyyanka Mai girma Mai nasiha Mai cikakken sanin Allah Sannan Shugaba na gari
Idan kasami shehi mai irin wadanchan halayan to Kamallaka Masa kanka kada kabada baya kazamo kamar matacce har abada zaka rabauta
Allah ya mana arzikin zama tijjanawa yan Faila na Gaskiya domin Albarkar manzan Allah da Shehu
Abba na Niasse Assufi
SHEHU Ibrahim Niasse Fardun nee