
09/05/2025
Kano State Youth and Women HoR/HA Candidate Forum ta bayyana rashin amincewarta da umarnin da mai girma Gwamnan Jihar Kano ya bayar na cewa kananan hukumomi su cire makudan kudade domin yin karo-karon siyan motocin alfarma ga sarakuna alhalin jihar na fama da manyan matsaloli na tattalin arziki da tsananin rashin ruwa, tabarbarewar kiwon lafiya, da yaduwar cututtuka musamman na zazzabin cizon sauro.
A matsayarmu na kungiyar da ke tsayawa tsayin daka wajen kare muradun matasa da mata, muna ganin wannan a matsayin rashin adalci, musamman a lokacin da ruwa ya gagara a sassa da dama na jihar. Cutar cizon sauro (maleriya) ke yawan kashe mutane fiye da adadin da ake bayyanawa. Makarantu ke bukatar gyare-gyare Malamai suke bukatar kayan koyarwa. Matasan da s**a dogara da gwamnati ke cikin damuwa saboda rashin guraben aikin yi.
Muna kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta sake duba wannan matsaya ta sauya akala zuwa abubuwan da s**a fi dacewa da rayuwar al’umma baki ɗaya. Muna ganin bai kamata a fifita jin daɗin wasu tsiraru ba akan rayukan dubbannin talakawa da ke cikin kunci da fargaba.
Muna fatan Gwamnatin Jihar Kano za ta ji kukan jama’a kuma ta mayar da hankali kan abubuwan da za su fi tasiri ga rayuwar al'umma da ci gaban jihar baki ɗaya.
Kano State Youth and Women HoR/HA Candidate Forum
09-05-2025