26/10/2025
                                            Duk Lokacin da Kayi Shiru, Ka Buɗe Kofar Zalūnci.
Dan Bello Yace:
“Duk lokacin da ba ka yi magana ba, wani mai karya ya na amfani da shirunka domin son zuciyarsa.”
Wannan ba lokacin natsuwa bane; wannan lokaci ne na tunanin da yake k**a da hauka amma a kan gaskiya. Najeriya na ƙonewa, sai dai waɗanda ke cin moriyar wutar su ne suke cewa “komai lafiya lau.”
Talaka ya gaji da yin haƙuri, amma gwamnati bata gaji da yi masa karya ba.
Duk lokacin da jama’a s**a fara fahimtar cewa zaman lafiya ba shi da amfani idan ana rayuwa cikin ƙasƙanci, to lokacin ne sauyi da sauƙi za su zo.
Mu tambayi kanmu:
Idan abinci ya fi gaskiya tsada, idan kalmar “canji” ta zama barkwanci, idan aka tsare wanda ya faɗi gaskiya, to menene nufin “ci gaban ƙasa”?
✊🏽 Wanda ya gaza jin haushi a irin wannan lokaci, to zuciyarsa ta mutu kafin jikinsa.