27/09/2025
*SHIN YA HALATTA A SIYARDA KAYAN MARIGAYI DOMIN A BIYA MASA BASHI*
*TAMBAYA*❓
Assalamualaikum barka da warhaka fatan malam Yana cikin koshin lfy Allah yasa haka. Amin malam tambaya na shine yahalata a seyarada kayi maragayi Dan abiya Mai bashi tambaya na 2 ya halata maman maragayi yayi yauta da kayashi kamar waya
*AMSA:*‼️
Wa alaikumus salam wa rahmatullah.
*TAMBAYA TA 1:*
Ya Halatta a sayar da kayan marigayi domin a biya bashinsa.
Manzon Allah (SAW) ya ce *“Ruhin mumini zai yi tsayin daka har sai an biya bashinsa.”* (Tirmidhi). Kuma bashi yana da fifiko akan gado, dole ne a biya kafin a raba gadon.
*TAMBAYA TA 2:*
Ba ya halatta maman marigayi (ko wani daga cikin ’yan uwa) ta yi kyauta da kayan marigayi kafin a raba su bisa ga shari’ar gado.
Dukiyar marigayi bayan an cire bashi da wasiyya ta zama ta magada ne gaba ɗaya, ba mallakar uwa ko wani ɗaya daga cikinsu kawai ba. Allah ya ce: *“Maza suna da rabon da iyaye da ’yan uwa s**a bari, haka ma mata suna da rabon da aka bari…”* (An-Nisa’i ayata 7). Don haka ba za a yi kyauta da ita ba sai da yardar sauran magada.
*Wallahu ta'ala aalam*