ASB Hausa

ASB Hausa ASB Hausa
Sahihan labarai, cikin daidaito. Labarai | Rahotonni | Wasanni

Wata kotu a Ghana ta yanke wa wani matashi mai shekaru 26 hukuncin daurin wata guda a gidan yari, bayan da ya amsa laifi...
22/07/2026

Wata kotu a Ghana ta yanke wa wani matashi mai shekaru 26 hukuncin daurin wata guda a gidan yari, bayan da ya amsa laifin yunkurin satar wata motar sulke ta 'yan sanda.

An ce Ebenezer Frimpong ya shiga motar ne ya tuka ta bayan direban motar, Lance Corporal Joshua Denkyi, ya bar ta a gefen hanya domin shiga wani kantin magani a watan Afrilun wannan shekara.

Bayan wani ɗan gajeren farautar motar, jami'an tsaro sun k**a Frimpong tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin yunkurin satar motar.

Da farko, kotun ta bayar da umarnin a yi wa wanda ake zargin gwajin lafiyar kwakwalwa domin tabbatar da cewa yana cikin hayyacinsa kuma zai iya fuskantar shari'a. Bayan samun sak**akon gwajin, Frimpong ya amsa laifinsa.

Alƙali Jephtha Appau ya yanke masa hukuncin wata guda a gidan yari, yana mai cewa ya yi la'akari da shekarun matashin da kuma yadda ya amsa laifinsa ba tare da ɓata lokacin kotu ba.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na iya ƙaddamar da ƙarin hare-haren soji kan Iran a daren Laraba, bayan har...
08/07/2026

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na iya ƙaddamar da ƙarin hare-haren soji kan Iran a daren Laraba, bayan hare-haren da ɓangarorin biyu s**a kai wa juna a ranar da ta gabata.

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a taron ƙasashen ƙawancen NATO da ke gudana a Turkiyya, inda ya ce: "Zan ba da ɗan gargaɗi kaɗan: Za mu kai musu mummunan hari a daren yau."

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ke ƙara tsananta, lamarin da ya tayar da hankulan ƙasashen duniya tare da haifar da fargabar ƙarin tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, Iran ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan sabon barazanar da shugaban Amurkan ya yi ba.

Me za ku ce?

Babbar Hedikwatar Sojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta yi gargaɗin cewa duk wata ƙasa ko wuri da zai bai wa sojojin Amurka ...
08/07/2026

Babbar Hedikwatar Sojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta yi gargaɗin cewa duk wata ƙasa ko wuri da zai bai wa sojojin Amurka goyon baya a duk wani hari da za su kai kan Iran, za a ɗauke shi a matsayin halastaccen wurin kai hari.

Sanarwar, wadda kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya wallafa, ta ce rundunar sojin Iran za ta kai hari kan duk wani tushen da ake amfani da shi wajen tallafa wa hare-haren da Amurka ke kai wa kan yankinta da kuma ikon mallakar ƙasarta.

Kalaman na zuwa ne yayin da rikici tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da ƙamari, lamarin da ya ƙara tayar da fargabar faɗaɗar rikicin zuwa sauran ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Kafofin yaɗa labarai na Iran sun ce ƙasar ta kai hare-haren ramuwar gayya kan wasu wurare a Bahrain da Kuwait, a matsayi...
08/07/2026

Kafofin yaɗa labarai na Iran sun ce ƙasar ta kai hare-haren ramuwar gayya kan wasu wurare a Bahrain da Kuwait, a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ta kai a yankunan Hormuz da Bandar Abbas.

Tun da fari shugaban Majalisar Wakilan Iran,
Mohammad Bagher Qalibaf, ya ce ƙasar a shirye take ta maida martani ga Amurka, kuma ba za ta amince da abin da ya kira barazana daga Washington ba. Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Kafofin yaɗa labaran Iran sun kuma rawaito cewa an ji ƙarar tashin bama-bamai a biranen Bandar Abbas, Qeshm da Sirik. A nata ɓangaren, Amurka ta ce ta kakkabo mak**ai da ƙananan jiragen ruwa na yaƙi mallakin Dakarun Juyin Juya Hali na Iran.

Masu sa ido na cewa sabon tashin hankalin na iya kawo cikas ga ƙoƙarin tsagaita wuta da tattaunawar yarjejeniyar nukiliya tsakanin Amurka da Iran, waɗanda aka ce an dakatar da su har sai bayan jana'izar Ayatollah.

Rahotanni daga wasu kafafen yaɗa labarai na Asiya sun ce Amurka da Iran na tattaunawa kan wata yarjejeniya da za ta sa T...
25/05/2026

Rahotanni daga wasu kafafen yaɗa labarai na Asiya sun ce Amurka da Iran na tattaunawa kan wata yarjejeniya da za ta sa Tehran ta sake buɗe mashigar ruwan Hormuz na tsawon kwanaki 30 bayan cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikici.

Rahoton ya ce shirin yarjejeniyar zai haɗa da dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar, wadda ke daga cikin muhimman hanyoyin safarar man fetur a duniya.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga Amurka ko Iran da ta tabbatar da cikakken cimma yarjejeniyar.

Yadda Jagoran Jam'iyyar NDC na Kano Engr. Rabi'u Musa Kwankwaso ke ganawa da ƴan takarar Jam'iyyar na shiyyar Kano ta ku...
24/05/2026

Yadda Jagoran Jam'iyyar NDC na Kano Engr. Rabi'u Musa Kwankwaso ke ganawa da ƴan takarar Jam'iyyar na shiyyar Kano ta kudu a yau Lahadi.

📸 Hon. Saifullahi Hassan

Tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar-Adamu, ya ƙi amincewa da sak**akon zaɓen fidda gwani na j...
24/05/2026

Tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar-Adamu, ya ƙi amincewa da sak**akon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, wanda ya bai wa Sanata Aliyu Ahmed-Wadada nasara.

Adamu ya zargi cewa an tafka maguɗi da rashin gaskiya a zaɓen, yana mai cewa akwai wuraren da ba a gudanar da zaɓe ba amma aka cika sak**ako.

Ya kuma bukaci shugabannin APC da su binciki yadda aka gudanar da zaɓen, tare da gargadin cewa zai sanar da matakin siyasar da zai ɗauka idan ba a yi masa adalci ba.

Fitaccen jarumin Kannywood, Isah Feroz Khan, wanda aka fi sani da Presdo a cikin shiri mai dogon zango na Labarina, ya a...
24/05/2026

Fitaccen jarumin Kannywood, Isah Feroz Khan, wanda aka fi sani da Presdo a cikin shiri mai dogon zango na Labarina, ya angwance a yau Lahadi.

Rahotanni sun ce an gudanar da ɗaurin auren ne cikin farin ciki tare da halartar iyalai, abokai da masoyan jarumin.

Presdo na daga cikin fitattun jaruman da s**a shahara a shirin Labarina, wanda ya samu karɓuwa sosai a tsakanin masu kallon fina-finan Hausa.

Masoya da abokan arziki sun ci gaba da taya jarumin murnar shiga sabuwar rayuwa ta aure tare da yi masa fatan alheri.

Tsohon ministan sufurin Najeriya ya bayyana hakan ne yayin da yake nuna damuwa kan ci gaba da tsare tsohon gwamnan na Ka...
24/05/2026

Tsohon ministan sufurin Najeriya ya bayyana hakan ne yayin da yake nuna damuwa kan ci gaba da tsare tsohon gwamnan na Kaduna Nasir El-Rufai.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan shari’ar El-Rufai da kuma rahotannin hana wasu jiga-jigan jam'iyyar ADC ganinsa.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya bayyana haka yayin da yake magana kan shirye-shiryen jam’iyyar ADC gabanin zaɓen ...
24/05/2026

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya bayyana haka yayin da yake magana kan shirye-shiryen jam’iyyar ADC gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ASB Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category