KBC News Hausa

KBC News Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from KBC News Hausa, Media/News Company, Kano.

DA DUMIN SA:Iran ta ce za ta hana Samsung shiga kasar bayan China ta tabbatar da Isra’ila na saka na’urorin leƙen asiri ...
18/11/2025

DA DUMIN SA:Iran ta ce za ta hana Samsung shiga kasar bayan China ta tabbatar da Isra’ila na saka na’urorin leƙen asiri da ba za a iya cirewa ba a wayoyinta.

Gwamnatin Iran ta bayyana cewa tana shirin dakatar da shigo da dukkan wayoyi, kwamfutoci da na’urorin lantarki daga kamfanonin da ake zargin suna da alaƙa da Isra’ila.

Hukumar tace wannan mataki na da nufin kare tsaron cikin gida da kuma rage tasirin kamfanonin da ake zargin suna gudanar da ayyukan leƙen asiri ta hanyar na’urorin zamani.

Me Zaku Ce?

Najeriya ta kara jaddada kudurinta na bayar da duk wata gudummawa da ta k**ata domin gina iyakoki masu nagarta a kasashe...
18/11/2025

Najeriya ta kara jaddada kudurinta na bayar da duk wata gudummawa da ta k**ata domin gina iyakoki masu nagarta a kasashen Afrika domin bayar da cikakkiyar damar gudanar da harkokin kasuwanci da ci gaba tattalin arziki ba tare da samun wani cikas ba.
Shugaban ya tabbatar da hakan ne jiya Litinin a birnin Abuja yayin da yake bude babban taron hadin gwiwar kasuwanci na hukumomin kwastam na kasashen Afrika.
Shugaban na tarayya wanda ya sami wakilcin mataimakinsa Sanata Kashim Shettima ya ce, Najeriya a shirye take wajen ganin nahiyar Afrika ta ginu ta hanyar cinikayya bisa tsari, inda ya ce, duka wannan yana samuwa ne a yanayin da aka sami ingantattun iyakoki domin dai saukaka shige da ficen hajoji, inda ya kara tabbatar da cewa, zai yi wahala masana’antunmu su sami murmurewa sosai muddin dai harkokin kasuwanci sun ci gaba da tafiya babu tsari.
Ko da yake k**ar yadda shugaban ya bayyana yanzu kasashen Afrika sun riga sun dauki matakai na kaiwa ga nasarar bunkasuwar tattalin arzikinsu bayan amincewa da s**a yi da tsarin cinikayya mara shinga a tsakaninsu, amma dai abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne yadda za a aiwatar da shirin, inda ya yi fatan wannan taro zai kasance silar samun bude.
“Auna nasarar wannan taro ba zai tsaya kawai kan bayanin bayan taro da za a fitar ba, akwai bukatar a gani a zahirance k**ar tabbatar da gajarta lokacin ketara iyaka, tabbataccen tsarin amfani da nau’ikan kudi na bai daya da kuma kyautata tsarin jigilar kayayyaki a daukacin iyakoki na kasa da kuma tasoshin ruwa.” (Garba Abdullahi Bagwai)
[email protected]

DA DUMI-DUMI: Mai ba da shawarar tsaron Kasar Iraki, Qasim al-Araji, ya gana da manyan jami’an Iran a Tehran.
23/10/2025

DA DUMI-DUMI: Mai ba da shawarar tsaron Kasar Iraki, Qasim al-Araji, ya gana da manyan jami’an Iran a Tehran.

Falasɗinawa sun gudanar da jana'izar Gawarwakin da Isra'ila ta kashe a hannunta.Jana'izar ta gudana ne a Deir Al Balah d...
23/10/2025

Falasɗinawa sun gudanar da jana'izar Gawarwakin da Isra'ila ta kashe a hannunta.

Jana'izar ta gudana ne a Deir Al Balah domin yin bankwana da gawarwakin Falasdinawa 54 da ba a san su ba, cikin jerin gawarwaki 165 da Isra’ila ta mayar tun daga ranar 14 ga Oktoba bisa yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ofishin yada labarai na gwamnatin Falasdinawa a Gaza, ta bayyana cewa an gano alamun azabtarwa a jikin gawarwakin, ciki har da alamun ratayewa, da harbin bindiga a jikinsu,
inda wasu gawarwaki s**a nuna shaidar an taka su da tankokin yaki.

TIRKASHI: Yanda Ake Azabtar Da Falasdinawa A Gidan Yarin Isra'ila Wannan gidan yari, wanda shi ne mafi girma a Isra’ila,...
23/10/2025

TIRKASHI: Yanda Ake Azabtar Da Falasdinawa A Gidan Yarin Isra'ila

Wannan gidan yari, wanda shi ne mafi girma a Isra’ila, ya dade yana fuskantar s**a daga kungiyoyin kare hakkin ɗan adam saboda irin cin zarafi, cunkoso, da rashin tsafta da ake fuskanta a cikinsa.

Wasu daga cikin waɗanda aka k**a, musamman a lokacin mamayar da sojojin Isra’ila s**a yi a yankin Gaza, sun ruwaito cewa ana tsare su cikin wahala, ana hana su samun abinci mai kyau da magani, har zuwa mintuna na ƙarshe kafin a sake su bisa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a farkon wannan watan.

Kungiyoyin kare hakkin ɗan adam na ci gaba da kira ga Isra’ila da ta daina cin zarafin Falasɗinawa tare da bin ƙa’idar ƙasa da ƙasa wajen kula da waɗanda take tsare.

Rundunar sojojin Nijar ta janyewa daga rundunar yaki da ta'addanci a yankin tafkin ChadiA jamhuriyyar Nijar, rundunar so...
31/03/2025

Rundunar sojojin Nijar ta janyewa daga rundunar yaki da ta'addanci a yankin tafkin Chadi
A jamhuriyyar Nijar, rundunar sojojin kasar ce ta sanar a ranar jiya Lahadi 30 ga watan Maris din shekarar 2025 daga kawancen rundunar kasa da kasa FMM dake yaki da ta'addanci a yankin tafkin Chadi, bayan kafuwarta a shekarar 2015 tare da kasashen Najeriya, K**aru, Chadi, Bénin domin yaki da kungiyoyin ta'addanci k**ar Boko Haram da Iswap.
Daga birnin Yamai abokin Usman Hassan ya aikomana da wannan rahoton.

Naja’atu Muhammad ta yi wannan bayani ne cikin wata hira da Premier Radio, wacce aka wallafa a shafin Facebook, kan doka...
30/03/2025

Naja’atu Muhammad ta yi wannan bayani ne cikin wata hira da Premier Radio, wacce aka wallafa a shafin Facebook, kan dokar ta-baci da dakatar da gwamnatin jihar Ribas da Tinubu ya yi. Ta bayyana cewa akwai jihohin da gwamnatin tarayya ke ganin dole sai ta mamaye su domin bai wa Bola Ahmed Tinubu damar ci gaba da mulkin kasar nan. Naja’atu ta zargi Tinubu da hararar jihohi. Hajiya Naja’atu Muhammad ta zargi gwamnatin tarayya da kokarin kakaba dokar ta-baci a jihar Kano a kwanakin baya. Naja'atu ta nemi a takawa Tinubu burki. Ta ce: "Kano ma abin da s**a so su yi ke nan. Shi ya sa s**a sa akwai Sarkin jihar Kano, akwai Sarkin gwamnatin tarayya." "Idan ka na jin labarin yadda ake zuzuta rigima a kan sarakuna, waye ke tayar da rigima? Waye ke tayar da hankula? Waye ya damu, alhalin mutanen Kano suna harkar cinikayyar su, suna neman kudinsu?"
Gwamna ya maida martanin barazanar dakatar da shi k**ar yadda aka yi a Ribas Naja’atu ta fadi dabarar gwamnati a Kano Ta kara da cewa gwamnatin tarayya na kokarin ruruta rikicin masarautar Kano saboda wata manufa ta siyasa da ke da alaka da Tinubu. Naja’atu ta ce: "Abin da zai faru shi ne, yawancin ‘yan siyasar mu dama can mutanen banza ne. Ba su da wata akida ta alheri ga talaka. Mafi yawansu babu ruwansu da talaka." Ta yi zargin cewa ana iya yin amfani da karfin gwamnati wajen kwace iko da wasu jihohi k**ar Kano domin bai wa shugaban kasa damar samun karfi a nan gaba. Baya ga Kano, ta ce akwai yiwuwar a tsige sanatoci da sauran masu rike da zababbun muk**ai domin cimma wani shiri na sake gudanar da zabe.

kbc News Hausa📡

Shafin Haramain ya bayyana ganin jaririn watan shawwal,gobe lahadi zata kasance sallah karama.
29/03/2025

Shafin Haramain ya bayyana ganin jaririn watan shawwal,gobe lahadi zata kasance sallah karama.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa ba za a yi Hawan Sallah ba a Kano.Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ...
28/03/2025

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa ba za a yi Hawan Sallah ba a Kano.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na Facebook, tare da hoton da Kwamishinan ‘Yan Sanda da Daraktan Hukumar DSS da Kwamanda na Barikin Sojoji da Kwamandan Rundunar Sojin Sama da ke jihar s**a ɗauka tare a yayin sanarwar.

Dakarun Sojoji Na Musamman Sun K**a 'Yan Ta'adda Yayin Da Suke Kokarin Dasa Bam A Zamfara..Dakarun musamman na Operation...
28/03/2025

Dakarun Sojoji Na Musamman Sun K**a 'Yan Ta'adda Yayin Da Suke Kokarin Dasa Bam A Zamfara..

Dakarun musamman na Operation FANSAN YANMA sun k**a wasu ‘yan ta’adda da suke yunkurin tayar da bama-bamai a wata hanya mai mahimmanci a dajin Gando da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.

Wata majiya ta shaida cewa dakarun da ke aiki a karkashin Operation TSAFTA DAJI III Phase 3, sun kai harin kwantan bauna a lokacin da s**a ci karo da wasu gungun ‘yan ta’adda da suke ajiye bama-bamai.

Da ganin dakarun da ke tahowa, ‘yan ta’addan sun gudu zuwa cikin dajin karkashin duhu, inda s**a yi watsi da ababen fashewa da kayan aikinsu.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da: Babur daya, jerikan lita 25 guda uku cike da kayan aikin IED, igiyar sapper mai tsawon mita 300, abun fashewar wutar lantarki DET 33 daya da farat daya da ake amfani da su wajen dasa abubuwan fashewa.

Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da kai farmaki kan ‘yan ta’adda da masu aikata miyagun laifuka a jihar Zamfara, inda rundunar Operation FANSAN YANMA da Operation TSAFTA DAJI III s**a kai hari a maboyar ‘yan ta’adda a fadin Anka, Bagega, da Bukkuyum.

DefenceInfo NG
HQ Nigerian army

Ƙarfafuwar alaƙa tsakanin Rasha da China na barazana ga Amurka.
27/03/2025

Ƙarfafuwar alaƙa tsakanin Rasha da China na barazana ga Amurka.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KBC News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share