
16/04/2025
An rahoto Carlo Ancelotti zai buga salon 4-4-2 a karawarsu da Arsenal yau. Kocin yana so ƙungiyarsa ta mamaye ƙwallo, ta kuma mallake dukkan wasan tare da hana Arsenal buga salon wasan ta.
Arsenal sun fi zama hatsari ya yin da ƙwallo take a hannun su, don haka dabarar Ancelotti shine hana su mallakar ƙwallo, kuma zai iya cimma hakan da salon 4-4-2, inda zai zuba huɗu a tsakiya.
Carlo Ancelotti na fatan ƙungiyarsa ta yi daren al'ajabi yau, kuma zai yi duk mai yiyuwa domin cimma hakan.
• Fagen Wasanni