21/06/2025
MAZAJE KU SAURARE NI DA KYAU....
KAINE KAYIWA KANKA DA KANKA ASIRI 🤌
Na dade inaso inyi magana akan wannan abun da yake faruwa da samarin mu na yanzu a kasuwa. Amma dai yau dole tasa sai nayi. Sai kaga saurayi matashi ya fara zuwa kasuwa kokuma ya daɗe a kasuwa amma daga zarar tauraruwar sa ta fara haskawa sai komai ya rushe ya lalace. MEYASA ⁉️⁉️
NOTE: RUBUTUN YANA DA TSAYI KUMA BA DOLE NE SAI KA KARANTA BA.
Bayan nayi bincike dakuma nazari akan irin waɗannan matsaloli na fita da sak**ako masu yawa. To amma kuma akwai wani babban dalilin da yafi kowanne ƙarfi, saboda haka akan shi zanyi magana yanzu.
Da farko dai burin duk wani matashi ne yaga cewa an yaye shi a shagon da yake shima an zuba masa jari domin ya tunkari rayuwar shi ya gina ta. To amma fa ba anan gizo yake yin saƙar ba. Matsalar ba daga ƙin yaye shi bane ba kokuma ƙin zuba masa jari. A'a matsalar daga wajen shi ne bayan an zuba masa jarin.
Da farko yaro zai ta taka tsantsan wajen sarrafa kuɗin shi bayan an sallame shi a shago. Amma da zarar ance yau an yaye shi sannan ga jari an zuba masa to fa sai LAHAULA. Shi mai gidan ya zuba masa jari domin a dinga yin lissafi duk shekara kokuma rabin shekara amma shi kuwa ya laƙume jarin cikin ƙasa da wata 5.
BARI NA BAKU LABARIN ƊAYA DAGA CIKIN WANDA NAYI BINCIKE AKANSU DOMIN FITO MAKA DA ABUN FILI.
Yaro ne aka yaye shi daga shago aka buɗe masa nasa sannan aka zuba masa jari ta yadda duk shekara za'a zo ayi lissafi bayan sallamar shi ta kullum da aka yanke adadin da zai ɗauka koda anyi ciniki ko ba'a yi ba.
Farat ɗaya aka ga yaro kasuwa ta buɗe alhamdulillah. Aka ga canji a jikin fatar sa. Yan gidan su na ta murna musamman mahaifansa don ganin ɗan su ya tasa shima yanzu ya fara zama mutum.
Cikin ƙasa da wata 3 yaro ya canja wayar da yake riƙewa ya koma babbar harka. Bayan wata 4 yaro ya ɓaro sabon babur (HAOJUE UD). Kafin wannan lokacin kuma dama tuni yayi juyen baƙin mai na tufafin sa, daga shadda mai tsada sai yadi mai tsada. Kowa yana ta san barka. Masu hassada s**a fara. Masu burin zama k**ar shi s**a fara. A takaice dai ni'ima ta buɗe ta ko ina.
Ashe ashe.
Ashe ashe kallon KITSE ake yiwa ROGO. Yaro yabi takan dukiyar uban gidan sa ne ba'a sani ba. Sai bayan anzo lissafi aka ga abinda bashi ne ba. Uban gidan nasa yace ya haƙura dashi bazai iya ba. Saboda haka ya bar masa shago. Cikin ₦12,000,000 da aka zuba masa, daƙyar aka samu ₦3,200,000. Turƙashi.
Kwana biyu rayuwa ta fara canjawa. Duk abubuwan da yake yi yanzu bazai iya ba. Ya siyar da babur ɗin nashi. Ya dawo saka kaya babu guga. Daga ƙarshe ma wayar tashi bata tsira ba ya siyar. Me zai faru?? Kowa ya dinga cewa ai asiri aka yi masa. Ai ƴan baƙin ciki ne s**a sako shi a gaba saboda anga ya fara ci gaba. ASHE?
Case irin wannan gashi nan a kasuwanni birjik.
Wanene yayi masa ASIRI?
Ka riƙe gaskiya a koda yaushe.
Akwai abubuwa dayawa a gaban ka.
Ka rayu cikin aminci.
Ibrahim reco kano