APN HAUSA

APN HAUSA Wannan kafar yada labarai ce domin kawo muku ingantattun Labarai, Harkokin Siyasa da na Wasanni dake faruwa a Nahiyar Afrika.

‎Tambaya:‎‎A wacce shekara Annabi S.A.W ya yi hajjin bankwana?‎
12/08/2026

‎Tambaya:
‎
‎A wacce shekara Annabi S.A.W ya yi hajjin bankwana?
‎

“Jihar Kano ba ta bukatar auren gata a halin yanzu, kamata ya yi Gwamna ya magance matsalar ruwan sha da ke jefa al'umma...
12/08/2026

“Jihar Kano ba ta bukatar auren gata a halin yanzu, kamata ya yi Gwamna ya magance matsalar ruwan sha da ke jefa al'umma cikin wahala."
‎
‎Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar NDC, Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya bayyana hakanne a zantawarsa da DCL Hausa.

Sarkin Musulmi Ya Bukaci Musulmi Da Kiristocin Najeriya Su Daina Zagin Juna.‎‎Mai alfarma sarkin musulmi Muhammadu Sa’ad...
12/08/2026

Sarkin Musulmi Ya Bukaci Musulmi Da Kiristocin Najeriya Su Daina Zagin Juna.
‎
‎Mai alfarma sarkin musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga Musulmi da Kiristocin Najeriya da su daina zagin juna, yana mai cewa girmama juna da jure bambancin addini na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya.
‎
‎Sultan ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin wani taron kasa da kasa kan tsaron kasa da ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
‎
‎Ya ce babu wani dalilin da zai sa Musulmi ko Kirista ya dauki kansa a matsayin wanda ya fi wani addini daraja.
‎
‎Ya kara da cewa Allah ne Ya halicci kowa, don haka ya kamata mutane su bar hukuncin wanda ya fi wani ga Allah.
‎
‎Sultan ya bayyana wannan matsaya ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan kalaman da ke rura wutar rabuwar kawuna bisa addini a Najeriya.
‎
‎Ya ce ‘yan Najeriya za su iya rayuwa cikin zaman lafiya idan s**a girmama juna tare da kauce wa zagi da cin mutunci saboda bambancin addini.

"A tarihin siyasar jihar Kano tin daga kan Ɗan Hassan, wanda aka yi kokawa da shi 2002, babu wanda ya bar Kwankwasiyya y...
12/08/2026

"A tarihin siyasar jihar Kano tin daga kan Ɗan Hassan, wanda aka yi kokawa da shi 2002, babu wanda ya bar Kwankwasiyya ya yi Nasara."
‎
‎Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar NDC, Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya bayyana hakanne a zantawarsa da DCL Hausa.

An kai ƙarar Kangana Ranaut Kotu bisa zargin cin mutuncin ɗaliban NEET.‎‎Wani lauya daga birnin Agra a Indiya ya ce a ra...
12/08/2026

An kai ƙarar Kangana Ranaut Kotu bisa zargin cin mutuncin ɗaliban NEET.
‎
‎Wani lauya daga birnin Agra a Indiya ya ce a ranar Laraba ya shigar da ƙara kan Kangana Ranaut, wadda take 'yar majalisar wakilai ta jam’iyyar BJP kuma jaruma, bisa kalaman da ta yi tana kiran ɗaliban da s**a gudanar da zanga-zangar nuna adawa da satar tambayoyin jarabawar NEET da suna “Generation Gutter”, wato tsarar banza ko tsarar magudanar shara.
‎
‎jeidar The Times of India ta ruwaito cewa Shugaban ƙungiyar lauyoyin Rajiv Gandhi Bar Association, lauya Ramashankar Sharma, ya zargi Ranaut da “cin mutuncin” ɗaliban da iyayensu.Ya kuma zarge ta da kasancewa tana da ɗabi’ar yin irin waɗannan kalamai a lokuta daban-daban.

‎Rahotanni sun ce an shigar da ƙarar ne a wata kotu ta musamman da ke sauraron shari’o’in ‘yan majalisa, kuma ana sa ran za a saurari batun a ranar 21 ga Agusta, 2026.

12/08/2026

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranci wata ziyarar aiki a gidajen ARTV da Jaridar The Triumph, shi da Hon. Sa’adu Aminu Sa’adu, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ungogo kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar.

Yau ake Bikin Ranar Matasa ta Duniya Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware ranar 12 ga watan Agusta na kowanne shekara domi...
12/08/2026

Yau ake Bikin Ranar Matasa ta Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware ranar 12 ga watan Agusta na kowanne shekara domin bikin ranar matasa a fadin Duniya.

Ya yin bikin akan tunawa da irin muhimmiyar rawar da matasa ke takawa wajen gina al’umma da makomar kasa.

A wannan rana, muna kira ga matasa da su kasance masu neman ilimi, sana’a, zaman lafiya da kishin kasa, tare da guje wa duk wani abu da zai lalata rayuwarsu da makomarsu.

11/08/2026

"Muna kira ga mai girma gwamna da ya kara riƙe Lawan na jume hannu 2, domin ci gaban jihar Kano."

Dahiru mai Nasara, Danjam'iyyar APC.

11/08/2026

"Yau ƴan jihar Kano sun gane cewa Kwankwaso ɗan baƙin cikin su ne, domin ba kishinsu ya ke ba "

Sanusi Ahuci Gwammaja, Danjam'iyyar APC.

Hon. Nuraddeen Rabi'u Buraje dai yana ɗaya daga cikin matasan dake gwagwarmaya wajen tabbatar da nasarar Kwamared Aminu ...
11/08/2026

Hon. Nuraddeen Rabi'u Buraje dai yana ɗaya daga cikin matasan dake gwagwarmaya wajen tabbatar da nasarar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo da jam'iyyar NDC a jihar Kano da Ƙaramar Hukumar Gwale.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when APN HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share