
08/07/2025
An gudnaar da taron Facebook Connect na matasan ƙaramar hukumar Birni da kewaye na jihar Kano don bunƙasa haɗin kai da sada zumunta.
A wara sanarwa da shugaban kwamitin shirya taron Mukhtar Idrees Bature Maisalati, ya fitar ya ce taron na bana ya yi armashi matuƙa.
Ya ce kwamitin ya samu ci gaba sosai cikin shekara guda, ciki har da koyar da matasa 33 ilimin fasahar AI da samar da guraben aiki, da kuma horas da mata 44 a sana’o’in hannu k**ar haɗa takalma, jaka da dinka zanin gado.
Shugaban ya kuma miƙa godiya ga abokan haɗin gwiwa da shugabannin da s**a ba da gudunmawa, tare da tabbatar da cewa za a ci gaba da shirya irin waɗannan tarurruka domin tallafa wa matasa da ci gaban al’umma.
Ya kuma jinjinawa mahalarta taron kan haɗin kai da goyon bayan da s**a nuna.