14/08/2026
Shugaban JIBWIS na ƙasa, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su mutunta addinan juna.
Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS)na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su mutunta addinan juna tare da yin aiki tare domin kare ƙasar.
Ya ce Musulmi da Kiristoci duk suna da haƙƙi da ruwa da tsaki iri ɗaya a Najeriya, kuma ya k**ata su zauna lafiya duk da bambance-bambancen addinansu.
Bala Lau ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Abuja, bayan tashin Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya (Muslim World League), Sheikh Dr Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, bayan kammala taron ƙasa da ƙasa na kwanaki biyu kan bambancin al’adu da zaman lafiya a cikin al’umma.
JIBWIS ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya, mai taken: “Bambance-bambance da Zaman Lafiyar Al’umma: Haɗin Gwiwa Domin Makoma Mai Kyau.”
HASKE TV