HASKE TV

HASKE TV Inda ake samun labarai masu zafi 🔥
Labaran Arewa | Najeriya | Duniya
Nishadi | Siyasa | Trending videos
📌 Ku danna follow domin sabbin updates kullum.

A tuntubemu ta WhatsApp 08122103543

https://whatsapp.com/channel/0029VbCIGT61t90XKCRWeV0y

MENENE IDO?Ido (Eye) wata muhimmiyar gaɓa ce ta jiki da ke ba mutum damar gani. Yana karɓar haske (Light) daga abubuwan ...
14/07/2026

MENENE IDO?

Ido (Eye) wata muhimmiyar gaɓa ce ta jiki da ke ba mutum damar gani. Yana karɓar haske (Light) daga abubuwan da ke kewaye da mu, sannan ya mayar da shi zuwa saƙonnin jijiya (Nerve impulses) waɗanda ake tura wa ƙwaƙwalwa (Brain) ta hanyar jijiyar ido (Optic nerve). Daga nan ne ƙwaƙwalwa ke fassara waɗannan saƙonnin zuwa hoto da muke gani.

MUHIMMANCIN IDO

Ido yana da matuƙar muhimmanci saboda yana taimakawa mutum wajen:

- Gano abubuwa da mutanen da ke kewaye da shi.
- Karatu da rubutu.
- Bambance launuka (Colours).
- Tantance nisa da kusancin abubuwa.
- Fahimtar motsi (Movement).
- Gudanar da ayyukan yau da kullum cikin aminci.

YADDA IDO YAKE AIKI A TAƘAICE

Lokacin da haske ya shiga ido, yana bi ta sassa daban-daban na ido har ya isa Retina (Bangon ido mai karɓar haske). A nan ne ake sauya hasken zuwa saƙonnin jijiya (Nerve impulses), waɗanda jijiyar ido (Optic nerve) ke kaiwa zuwa ƙwaƙwalwa (Brain) domin a fassara su zuwa hoto da muke gani.

MUHIMMIN BAYANI

- Mutum yana da idanu biyu, kuma suna aiki tare domin ba mu damar ganin abubuwa cikin tsanaki da kuma tantance tazararsu.

- Idanu suna daga cikin gaɓoɓin ji (Sense organs), tare da kunne (Ear), hanci (Nose), harshe (Tongue) da fata (Skin).

A TAƘAICE
Ido wata muhimmiyar gaɓa ce ta jiki da ke ba mutum damar gani. Yana karɓar haske daga abubuwan da ke kewaye da mu, ya mayar da shi zuwa saƙonnin jijiya, sannan ya aika su zuwa ƙwaƙwalwa ta hanyar jijiyar ido (Optic nerve) domin a fassara su zuwa hoto da muke gani. Saboda haka, kula da lafiyar ido yana da matuƙar muhimmanci domin samun ingantacciyar gani da gudanar da ayyukan yau da kullum.

Follow HASKE TV

Ribadu da jakadan Amurka sun tattauna kan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaroMai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro,...
14/07/2026

Ribadu da jakadan Amurka sun tattauna kan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya karɓi baƙuncin wata babbar tawagar gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da Afirka, Frank Garcia, domin tattauna yadda za a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Ribadu ya ce ganawar ta yi nazari kan ci gaban da aka samu ƙarƙashin kwamitin haɗin gwiwa na Najeriya da Amurka, tare da jaddada aniyar ɓangarorin biyu na ci gaba da tattaunawa da haɗin gwiwa kan batutuwan tsaro da s**a shafe su.

Garcia, wanda ya fara aiki a matsayin mataimakin sakataren harkokin Afirka a ranar 1 ga Yunin 2026, ya kai wannan ziyara ta farko a Najeriya tun bayan rantsar da shi.

Ziyarar na daga cikin rangadin da yake yi a ƙasashen yammacin Afirka, wanda ya haɗa da Najeriya, Côte d’Ivoire da Mali.

Follow HASKE TV

Da shugabannin mu zasu rike yin ƙarshe irin na Ganduje hakika da sun magance matsalolin mu masu tarin yawa -Sheikh Lawan...
14/07/2026

Da shugabannin mu zasu rike yin ƙarshe irin na Ganduje hakika da sun magance matsalolin mu masu tarin yawa -

Sheikh Lawan Triumph

Follow HASKE TV

Meke Faruwa a Mashigar Hurmuz, bayan Amurka ta tilasta jirgin Dubai bi ta Mashigar Hurmuz?Iran ta ce sojojin Amurka ne s...
14/07/2026

Meke Faruwa a Mashigar Hurmuz, bayan Amurka ta tilasta jirgin Dubai bi ta Mashigar Hurmuz?

Iran ta ce sojojin Amurka ne s**a ƙarfafa wasu manyan jiragen dakon danyen mai guda biyu su bi wata hanya da ba a amince da ita ba a mashigar Hormuz, kafin daga bisani jiragen s**a fuskanci hare-hare daga rundunar juyin juya halin Iran.

➜ A baya dai, Ma'aikatar Tsaron Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta bayyana cewa makamai masu linzami na ƙasar Iran sun kai hari kan jiragen dakon mai biyu na UAE yayin da suke tafiya ta hanyar jiragen ruwa da ke kudancin mashigar Hormuz, a cikin ruwan yankin Oman.

➜ Wani ma'aikacin jirgin ɗan ƙasar Indiya ya rasu, yayin da wasu takwas s**a jikkata, ciki har da huɗu da s**a samu munanan raunuka. Daga baya kuma an samu nasarar shawo kan gobarar da ta tashi a cikin jiragen biyu.

Follow HASKE TV

🔴 Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC): ta bayyana cewa ta kai Hari Muhimman wurare 3A cewar sanarwar...
14/07/2026

🔴 Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC): ta bayyana cewa ta kai Hari Muhimman wurare 3

A cewar sanarwar “Mun kai hare-hare kan rumbunan ajiyar kayan tallafin aikin soja, da cibiyar sadarwa ta tauraron ɗan adam, da kuma ginin da sojojin Amurka ke zama a ƙasar Bahrain.

Follow HASKE TV

AN KASHE MAI SANA'AR SAYAR DA INDOMIE A KANOWani matashi mai sana'ar sayar da Indomie, Yahaya Hassan (Yahaya Mai Indomie...
13/07/2026

AN KASHE MAI SANA'AR SAYAR DA INDOMIE A KANO

Wani matashi mai sana'ar sayar da Indomie, Yahaya Hassan (Yahaya Mai Indomie), ya rasa ransa bayan da wasu da ake zargin masu fashi da makami s**a tare shi a Kofar Nasarawa da ke kan titin Zaria Road a Kano.

Rahotanni sun ce maharan sun kwace mashinsa tare da kai masa mummunan hari, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsa.

Lamarin ya sake jawo kira ga gwamnatin Kano da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma tare da kamo waɗanda s**a aikata wannan ɗanyen aiki. Allah Ya jikansa da rahama. Ameen.

Follow HASKE TV

Tinubu Ya Taba Alƙawarin Biyan Kuɗin WAEC ga Dukkan Ɗaliban Najeriya Idan Ya Zama Shugaban ƘasaShugaban Ƙasa Bola Ahmed ...
13/07/2026

Tinubu Ya Taba Alƙawarin Biyan Kuɗin WAEC ga Dukkan Ɗaliban Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Ƙasa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taɓa yin alƙawarin cewa zai biya kuɗin jarabawar WAEC ga dukkan ɗaliban Najeriya idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da aka yaÉ—a a ranar 19 ga Janairu, inda ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa babu wani yaro da zai rasa damar rubuta jarabawar kammala sakandare saboda rashin kuÉ—i.

A halin yanzu, Tinubu shi ne shugaban ƙasar Najeriya, lamarin da ya sa wannan tsohon alƙawari ya sake jan hankalin jama'a yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan kuɗaɗen jarabawar WAEC a ƙasar nan.

Follow HASKE TV

Kuɗin Iran yana ɗaya daga cikin kuɗaɗen ƙasashe 10 waɗanda s**a fi ko wanne lalacewa a duniya. Naira 1,000 ta Naira daid...
13/07/2026

Kuɗin Iran yana ɗaya daga cikin kuɗaɗen ƙasashe 10 waɗanda s**a fi ko wanne lalacewa a duniya.

Naira 1,000 ta Naira daidai take da Naira dubu 30 a ƙasar Iran. Idan baka gane ba ina nufin idan ka ɗauki 1k ta kuɗin Najeriya sannan ka tafi da ita zuwa ƙasar Iran to ta zama 30K a can.

Idan mutum ya baka kyautar Miliyan 100 a kuɗin Iran, kana shigowa Najeriya ta zama Miliyan 3 da dubu 300 duk wannan lalacewar kuɗin namu. Amma duk da irin wannan lalacewar kuɗin nasu a hakan sun wuce shafin duk wani abu da ɗan ƙasa yake buƙata

at basic level tun daga kan Ilimi, lafiya, tituna, makarantu, cibiyar samar da wutar lantarki, tsaro da technological advancement iri daban-daban beyond any singular imagination. Wai fa a hakan ƙasar Iran suna cikin takunkumi (sanctions) sama da shekara 40 a duniya. A hakan fa kusan kaso 60% na ƙasashen duniya duk sun yanke alaƙar kasuwanci dasu sama da Shekaru 40 da s**a gabata.
‎
‎Sama da shekara 40 ƙasar Iran sai da s**a zama saniyar ware a Middle East, Europe, Asia ga kuma uwa-uba Amurka amma hakan ne kashe musu gwuiwa ba.

Follow HASKE TV

Da Dumi-Dumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin da ya hana INEC amincewa da tarukan zaɓen shugabannin jihohi na...
13/07/2026

Da Dumi-Dumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin da ya hana INEC amincewa da tarukan zaɓen shugabannin jihohi na ADC.

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin da ya hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) amincewa ko kuma shiga cikin duk wani taron zaɓen shugabannin jihohi (state congresses) da shugabancin ADC ƙarƙashin jagorancin David Mark ya shirya.

A hukuncin da aka yanke da rinjayen alkalai biyu kan ɗaya, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta tabbatar a ranar Litinin da hukuncin da Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 29 ga Afrilu, 2026.

Wannan ya ƙara tabbatar da nasarar jam'iyyar ADC matsayin babbar jam'iyyar adawa a Najeriya.

Domin samun ingantattun labarai kuyi following HASKE TV

Dangote Ya Kaddamar da Fasahar Bibiyar Motoci Domin Dakile Satar KayaKamfanin Dangote Industries Limited (DIL) ya bayyan...
13/07/2026

Dangote Ya Kaddamar da Fasahar Bibiyar Motoci Domin Dakile Satar Kaya

Kamfanin Dangote Industries Limited (DIL) ya bayyana cewa ya fara amfani da sabon tsarin sa ido da bibiyar motocinsa domin kare kayayyakin kamfanin, tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin sufuri, tare da ƙara inganta tsaro da ingancin ayyuka.

Kamfanin ya ce tsarin zai ba shi damar bibiyar motocinsa a kowane lokaci, gano duk wani karkacewa daga hanyar da aka tsara, hana satar kaya da kuma tabbatar da cewa ana isar da kayayyaki cikin aminci da kan lokaci. Haka kuma, tsarin zai taimaka wajen inganta yadda direbobi ke aiki da kuma rage haÉ—urran hanya.

Dangote Industries ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na dabarunsa na amfani da fasahar zamani wajen inganta ayyukan kamfanin, kare kadarorinsa da kuma tabbatar da cewa harkokin sufuri suna gudana cikin gaskiya, inganci da amana.

Follow HASKE TV

Address

Kano
713281

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HASKE TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share