24/03/2026
Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rade-radin da ke cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya daina sanya jan hula, alamar tafiyar Kwankwasiyya.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa babu wani umarni da aka bayar ga magoya baya su daina sanya jan hula ko fararen kaya da ke nuna tafiyar Kwankwasiyya.