Mashayar Imani

Mashayar Imani Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mashayar Imani, Broadcasting & media production company, Darussunnah Foundation, Kano.

16/06/2025
TAIMAKO DA AIKIN GAYYA 1. Ma’anar TaimakoTaimako na nufin bada gudunmawa ko agaji ga wani da ke cikin buƙata – zai iya k...
12/06/2025

TAIMAKO DA AIKIN GAYYA

1. Ma’anar Taimako

Taimako na nufin bada gudunmawa ko agaji ga wani da ke cikin buƙata – zai iya kasancewa na kudi, lokaci, ilimi, shawarwari, ko wasu kayan amfani.

2. Nau'o'in Taimako

Taimakon kudi: Kamar bayar da zakka, sadaka, tallafi ga mabukata.

Taimakon ilimi: Koyar da wasu, bayar da littattafai, bada horo.

Taimakon aiki: Aikin sa-kai (volunteering), taimakawa wajen aikin jama’a.

Taimakon tunani: Shawara mai kyau ko karfafa gwiwa.

3. Tasarar Taimako Wajan Gina Al’umma

a) Karuwar haɗin kai da soyayya

Taimako yana haifar da zumunci da soyayya tsakanin mambobin al’umma, yana rage kiyayya da kishi.

b) Inganta rayuwar marasa ƙarfi

Yana sa waɗanda ba su da halin kansu su samu damar cigaba da rayuwa cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.

c) Hana aikata laifi da tashin hankali

Mutane da ke cikin ƙuncin rayuwa idan sun samu taimako, hakan na hana su fadawa cikin ayyukan barna kamar sata ko ta’addanci.

d) Ƙarfafa ci gaban tattalin arziki

Taimakon ilimi ko jari ga matasa ko mata na iya haifar da sababbin sana’o’i da kasuwanci, wanda ke habaka tattalin arzikin al’umma.

e) Gina kyakkyawar al'umma mai adalci

Taimako yana nuni da al'umma da ke da tausayi da adalci, inda kowa ke da dama da kariya.

RASHIN TAIMAKO

1. Yana haifar da ƙiyayya da hassada.

2. Yana ƙara talauci da yunwa

3. Yana haifar da tabarbarewar tsaro da zaman Lafiya.

Allah ya ƙara mana kishin addinin mu da ƙasar mu.

SOYAYYA TSAKANIN AL'UMMA.Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce:  “Ba ku da cikakken imani har sai kun ƙaunaci j...
10/06/2025

SOYAYYA TSAKANIN AL'UMMA.

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce:

“Ba ku da cikakken imani har sai kun ƙaunaci juna.”

ولا تؤمنو حتى تحابوا

1. Soyayya wata ƙima ce da daraja da ke cikin zuciyar ɗan Adam wadda Allah ya halitta don ta kasance asalin dangantaka mai kyau a tsakanin mutane.

Duk inda soyayya ta tabbata, to sai zaman lafiya ya bunƙasa, haɗin kai ya ƙaru, da fahimtar juna ta wanzu.

2. Soyayya ita ce ginshiƙin da zamantakewa ke ɗoruwa a kai.

3. Soyayya ita ce ƙaunar da mutum ke yi wa wani ko wasu da zuciya ɗaya, ba tare da ya sa wata manufa ta cutarwa ba. Soyayya na nufin:

Tausayi,

Jinƙai,

Kulawa,

Girmamawa,

Da kuma karɓar juna duk da bambance-bambance.

Akwai nau’o’in soyayya da s**a haɗa da:

5. Soyayyar iyali: tsakanin ma’aurata, iyaye da ’ya’ya.

6. Soyayyar zumunta: tsakanin ’yan’uwa da abokai.

7. Soyayyar al’umma: tsakanin ƴan ƙasa ɗaya ko ƙabila ɗaya.

8. Soyayyar ɗan’adam gaba ɗaya: wanda ya wuce iyakar yare da addini , ita ce ta dabi'a.

Idan mutane na ƙaunar juna, zai yi sauƙin warware rikice-rikice ta hanyar tattaunawa ba tare da tashin hankali ba. Soyayya tana sa mutum ya saurari wanda ke da sabani da shi cikin natsuwa.

9. Soyayya tana sa mutum ya damu da halin da ɗan uwansa ke ciki, ta hanyar ba shi taimako, ƙarfafawa da goyon baya. Wannan na rage fushi da kiyayya a cikin al’umma.

10. Ƙarfafa Haƙuri da Juriya

Soyayya tana koya wa mutum ya rinƙa hakuri da jure halin wasu, musamman a lokacin da ya ji ciwo ko kuma aka saba masa. Wannan yana da tasiri wajen hana yaduwar rigima da rikici.

11. . Rage damuwa da Hasala

Idan soyayya ta mamaye zukata, mutane za su daina aikata miyagun ayyuka kamar faɗa,da hassada ,cin mutunci, zagi, ƙiyayya, da yawan korafi – waɗanda ke haddasa zaman dar-dar.

12. Soyayya na taimaka wajen gina al’umma wadda ke kallon juna a matsayin ‘yan’uwa ba tare da bambanci ba. Wannan yana ƙarfafa haɗin kai da jin daɗin rayuwa.

13. Soyayya na aiki da sauƙaƙe fahimta da haɗin kai, komai bambancin harshe ko fahimta a cikin addini.

14. Soyayya ga ƙasa da al’umma na sa mutane su yi ƙoƙari wajen bunƙasa ƙasarsu ta hanyar aiki tukuru da zaman lafiya.

15. Soyayya tana ɗaukar matasa a matsayin ginshiƙai na gaba, ta hanyar horar da su da karantar da su zaman lafiya da haɗin Kai.

Hausawa sun ce: “Soyayya gishirin zumunci ce.”

Wani karin magana na cewa: “Wanda ya ƙaunace ka, ba zai cutar da kai ba.

Misalan Soyayya a Tarihi

A zamanin Manzon Allah (SAW), lokacin da sahabbai ke rayuwa cikin ƙauna, suna rabon abinci da muhalli, hakan ya kawo zaman lafiya a Madina.

A tarihin Hausawa, akwai lokaci da dangantaka ta soyayya da auratayya a tsakanin ƙabilu ta warware matsaloli da dama na yaki da rashin fahimta.

16. Soyayya ita ce ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kai. Ita ce gishirin dangantaka, jigon fahimta, da tushen ƙarfafa al’umma. Duk inda soyayya ta wanzu, to rashin jituwa da rikici ba sa samun wuri. Saboda haka, wajibi ne a ɗora gwiwa da gwiwa wajen yada ƙauna da soyayya a cikin gidaje, makarantu, masallatai, da kuma dukan al’amuran yau da kullum.

Shawara: Ya dace hukumomi, malamai da shugabanni su riƙa koyar da jama’a muhimmancin soyayya da gina al’umma mai fahimta da haɗin kai, domin hakan ne zai taimaka wajen kawar da rikice-rikice da nuna bambanci da ya addabi al’umma.

Allah ya sa mu so juna don Allah.

(Daga Madinah)

31/05/2025
AIYUKAN HISBAH A TAƘAICE 1. AL-IHTISAB A FANNIN  IMANI . Yin wa’azi da umarni da kyakkyawan aiki a bangaren koyar da ruk...
25/05/2025

AIYUKAN HISBAH A TAƘAICE

1. AL-IHTISAB A FANNIN IMANI .

Yin wa’azi da umarni da kyakkyawan aiki a bangaren koyar da rukunan addini da imani.

2. AL-IHTISAB a FANNIN IBADU .

Kula da tsarkakewa da gyara a fannin ibadu kamar sallah, azumi, zakka, da sauran ayyukan ibada.

3. AL-IHTISAB A FANNIN MU’AMALATU.

Kula da halaltacciyar mu’amala a cikin kasuwanci, ciniki, da huldar yau da kullum.

4. AL-IHTISAB A FANNIN HALAYE. Yi wa mutane nasiha don gyaran dabi’u da kyautata halaye kamar gaskiya, aminci, da ladabi.

5. AL-IHTISAB A FANNIN HUKUNCI.

Kula da adalci da bin dokokin shari’a a yayin aiwatar da hukunci.

6. AL-IHTISAB A FANNIN GYARA. Gudanar da ayyuka don gyaran al’umma da kawar da barna da munanan dabi’u.

7. AL-IHTISAB TSAKANIN SASSA NA AL’UMMAR MUSULMI

Samar da tsari mai kyau na hada kan sassa daban-daban na al’umma ta hanyar umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummunan aiki.

8. AL-IHTISAB A KAN SHUGABANNI DA MASU IKO.

Kula da shugabanni da yi musu nasiha da basu shawara don tabbatar da adalci da bin dokokin shari’a.

9. AL-IHTISAB A KAN MALAMAI

Jawo hankalin malamai akan karantawa da wa'azi da tsage gaskiya cikin hikma ba tare da tsoro ko kwaɗayiba.

10. AL-IHTISAB A KAN MASU KUƊI.

Jawo hankalin masu wadata da arziki wajan taimakon addini da al'umma, wajan gina tattalin arziki mai Albarka da inganci da halacci bisa koyarwar addinin Musulunci.

11. AL-IHTISAB A KAN MA’AIKATA . Bibiyar ayyukan ma’aikata don tabbatar da kula da aiki da gaskiya da aminci.

12. AL-IHTISAB A KAN JAMI'AN TSARO.

Haɗa kai da jami'an tsaro don tabbatar da zaman lafiya, adalci da kare hakkin jama’a.

13. AL-IHTISAB A KAN WADANDA AKE ZARGI DA LAIFI DA MASU AIKATA LAIFIN

Yi musu nasiha da tsoratar da su fushin Allah, da jawo su a jiki don nuna musu hatsarin karya dokar Allah da abin da hakan zai jawo a duniya da lahira, Kula da su don tabbatar da an hukunta su bisa doka da kuma basu damar gyara halayensu.

14. AL-IHTISAB A KAN TALAKAWA. Yin nasiha da wa’azi ga talakawa don inganta zamantakewar al’umma da kuma kare kyawawan dabi’u.

15. AL-IHTISAB A KAN ƊAN HISBAH,

Jawo hankalin ma'aikatan Hisbah wajan kiyaye mutuncin aikin Hisbah da biyayya ga dokoki da tsoran Allah, da Haɗin kai.

Address

Darussunnah Foundation
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mashayar Imani posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share