11/03/2026
"Ni Musa Kazaure, a matsayina na tsohon Minista a Najeriya, na cancanci a gārkame ni a gidan yāri.
Duk ‘yan siyasar da s**a rike madafun iko tun daga shekarar 1999 sun gaza wa Najeriya.
Matakin sātar da aka yi a Najeriya ya yi yawa kwarai, kuma talakawa ne abin ya shafa.
Ni Ibrahim Musa Kazaure, mun yaudari Najeriya da talakawanta; don in fada muku gaskiya, dukanmu daya muke.
Ba wannan gwamnatin kadai ba, dukkanmu ba abin da muka tsināna. Da ace mun yi wani abu, da Najeriya ba ta kasance a yadda take yau ba."