Jaridar yanci

Jaridar yanci gidan watsa labaran duniya hadi Dana wasanni.

YANZU-YANZU: Hukumar EFCC reshen Kano ta k**a jarumar Kannywood, Samha Inuwa kan zargin wulakanta kuɗin Naira.
04/02/2026

YANZU-YANZU: Hukumar EFCC reshen Kano ta k**a jarumar Kannywood, Samha Inuwa kan zargin wulakanta kuɗin Naira.

Ko shaguɓe ba zan iya yi wa Kwankwaso ba - Hon. Khatimu Ibrahim Kul-kul
04/02/2026

Ko shaguɓe ba zan iya yi wa Kwankwaso ba - Hon. Khatimu Ibrahim Kul-kul

29/10/2025

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba ta tabbatar da shirye-shiryenta na tabbatar da tsaro a yayin zaɓen kananan hukumomi da za a gudanar a ranar 8 ga Nuwamba 2025.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, ASP Ishaku Victor Mshelizah, ya fitar a madadin Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Taraba, Betty Enekpen Isokpan Otimenyin.

Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta ɗauki tsauraran matakan tsaro domin tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, tare da bai wa jami’an tsaro umarni su nuna ƙwarewa da taka-tsantsan a yayin aikin.

Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su fito su yi amfani da haƙƙinsu na zaɓe cikin lumana, tare da bai wa jamiʼan tsaro haɗin kai.

Haka kuma, ta gargadi duk wanda ke shirin kawo rikici ko tada fitina a lokacin zaɓe da ya janye, domin za a gudanar da bincike don gano masu tada hankali, kuma duk wanda aka k**a zai fuskanci hukunci mai tsanani.

29/10/2025

JARIDAR YANCI

Gwamnatin Kano ta amince da kashe Naira biliyan 14 akan ayyukan raya ƙasaMajalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da k...
08/08/2025

Gwamnatin Kano ta amince da kashe Naira biliyan 14 akan ayyukan raya ƙasa

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 14.8 domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a sassan jihar.

Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Ibrahim Waiya, ne ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a ranar Juma’a a Kano.

Ya ce an ware Naira miliyan 364 domin gyaran asibitin haihuwa na Sabo Bakin Zuwo da ke unguwar Jakara.

A cewarsa, an kuma ware Naira miliyan 294 domin gyaran manyan gine-ginen da ake da su a Makarantar Koyar da Fasahar Lafiya ta Bebeji.

Kwamishinan ya bayyana cewa an ware Naira miliyan 113 domin samar da da kuma girka na’urorin hasken rana a asibitoci guda biyar na haihuwa a fadin jihar.

“Za mu kashe sama da Naira miliyan 112 domin samar da magunguna da kayan amfani a asibitocin Hasiya Bayero, Murtala Muhammad, da Yadakunya,” in ji shi.

Ya ce an kuma ware Naira miliyan 272 domin gyara da sabunta wani gida da aka saya a unguwar Zango domin amfanin Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad.

Haka kuma, an ware Naira miliyan 128 domin samar da kayan aiki ga dakunan asibiti guda biyu da aka gyara a Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase.

Waiya ya ce za a kashe Naira miliyan 379 domin gyaran ginin cibiyar kiwon lafiya ta farko a Zakirai tare da ƙara sabon gini a wurin.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gyaran ƙananan madatsun ruwa guda biyar a Madobi, Gwarzo, Garun Malam, Kibiya da Ajingi zai ci Naira miliyan 169.

Jaridar yanci

21/07/2025

Jaridar yanci

Mai bankado labarai da dumi duminsu.

21/07/2025

Hahhhhh

21/07/2025

CHIRM

21/07/2025

Allah ya kiyaye gaba

Kano ta zama jagaba wajen yawan masu yin rijistar katin dan kasaJihar Kano ta yi rajistar sabbin masu katin dan kasa na ...
12/07/2025

Kano ta zama jagaba wajen yawan masu yin rijistar katin dan kasa

Jihar Kano ta yi rajistar sabbin masu katin dan kasa na NIN sama da miliyan 1 tsakanin Janairu zuwa Yuni 2025

Ga adadin mutane da s**a yi rijistar a jihohi a tsawon lokacin.

1. Kano: 1.01m

2. Legas: 412.22k

3. Kaduna: 309.62k

4. Adamawa: 217.65k

5. Borno: 209.50k

6. Babban Birnin Tarayya (FCT): 209.24k

7. Kebbi: 192.05k

8. Ogun: 187.49k

9. Oyo: 183.60k

10. Akwa Ibom: 176.85k

11. Katsina: 171.97k

12. Jigawa: 170.83k

13. Sakkwato: 147.01k

14. Ribas: 141.02k

15. Delta: 123.91k

16. Taraba: 122.19k

17. Abia: 114.68k

18. Benue: 111.77k

19. Anambra: 108.19k

20. Bauchi: 102.25k

21. Edo: 97.56k

22. Neja: 87.06k

23. Enugu: 82.22k

24. Yobe: 81.10k

25. Imo: 79.41k

26. Nasarawa: 78.12k

27. Kwara: 61.32k

28. Filato: 56.13k

29. Osun: 55.00k

30. Zamfara: 50.80k

31. Bayelsa: 46.47k

32. Gombe: 42.34k

33. Ondo: 39.00k

34. Ebonyi: 36.28k

35. Cross River: 27.21k

36. Ekiti: 26.64k

37. Kogi: 26.04k

’Yan Najeriya mazauna ƙasashen waje : 49.95k

Address

Gwangwazo
Kano
100101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar yanci posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share