16/06/2025
BAYANIN YADDA AKE YIN ISTIKHARA IRIN WACCE ANNABI ﷺ YA KOYAR
:
Istikhara wata sallah ce da akeyi domin neman za'bin Allah madaukakin sarki game da wasu al'amura da bawa yake neman zabin Allah a cikin ɗaya daga cikinsu, misali k**ar a harkar neman aure dadai sauran wasu al'amuran.
Anan zamu fahimci cewa ashe ita istikhara ibadace kuma Annabi muhammadu ﷺ shine ya koyar da yadda ake yin ta, sabida haka babu inda akace kaje ayi MAKA ita inkuma kaje daya daga cikin wannan zaayi MAKA . bugun kasa ko duban taurari ko akira aljani a tmby shi shikuma ya gaya musu karya da gaskiya sukuma su gayama Allah yabamu Samar bin abinda Manson Allah ﷺ yazo mana dashi .duk wanda yayi wata istikhara ba irin wacce manzon Allah ﷺ ya koyar ba, to ya sani ba istikhara tabbatacciya yayi ba koda ma yayi babu wani tasiri da zatayi domin Allah madaukakin sarki baya karbar duk wata ibada har sai anyita a bisa koyarwar Annabi muhammadu ﷺ .
Sahabi jabir (ra) yana cewa: *MANZON ALLAH ﷺ YA KASANCE YANA KOYA MASU ISTIKHARA A CIKIN DUKKAN AL'AMURANSU KAMAR YADDA YAKE KOYA MUSU SURA DAGA CIKIN AL'KURANI.*
hadisin yana cikin *Sahihul Bukhari*
kunga wannan yake nuna mana ashe ita itikhara annabi ne ya koyar da ita bawai kowa gaban kansa zeyi kawai yaje ya aikata abinda yaga dama a matsayin istkhara ba.
Hal ila yau dai sahabi jabir yana cewa: Annabi yace: *IDAN 'DAYANKU YAYI NUFIN YIN WANI AL'AMARI TO YAYI SALLAH RAKA'A BIYU BA SALLAR FARILLAH BA SANNAN YACE*
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ-(((( وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ ))))))– خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.
Allahumma innee astakheeruka bi’ilmik, wa-astaqdiruka biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-‘azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir, wata’lamu wala a’lam ,wa-anta ‘allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta’lamu anna hazal-amr ((((say your need)))) khayrun lee fee deenee wama’ashee wa’akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in kunta ta’lamu anna hazal-amr sharrun lee fee deenee wama’ashee wa’aqibati amree fasrifhu ‘annee wasrifnee ‘anh, waqdur liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.
*Ma'ana:*
Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al’amari((((( sai ya ambaci bukata tasa ))))))alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al’amarina a wata rayuwar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa Ka kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka san wannan al’amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata da karshen al’amarina a wata ruwayar; da magaggaucin al’amarina da majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi”.
Yaku bayin Allah Wannan itace fa addu'ar istikhara wacce Annabi ﷺ ya koyar yanzu kuma za muyi bayaninta daki daki insha Allahu.
*BAYANIN YADDA AKE YIN ISTIKHARA*
Da farko dai Ita sallar istikhara bata da wani ke'bantaccen lokaci da akace dole sai a lokacin mutum zeyi a'a duk lokacin da wani al'mari ya bijirowa mutum da safe ne ko da rana da yamma ne ko da daddare dukkan waɗannan lokutan ya halatta mutum yayi sallar neman zabin Allah a cikinsu, dai sai kuma wani al'amari ya bijirowa muttm kuna yana bukatar ya nemi zabin Allah a cikin lamarin to ya halatta yayi sallar istikharar domin neman zabin Allah
:- *NIYYA* k**ar yadda muka sani a cikin shahararren hadisin Amirul muminin Sayyadin umar ɗan khad'd'ab cewa manzon Allah yace dukkan ayyuka basa yiwuwa/tabbatuwa sai da niyyoyinsu. To k**ar hakane itama sallah istikhara bata tabbatuwa sai da niyya. Bayan mutum yayi niyyar sallar istikhara sai yaje yayi alwala k**ar yadda yake sallah bata ingantuwa sai da alwala, Amma idan mutum yana da alwala a lokacin da yake son yin istikharar kawai zeyi sallar ne babu bukatar sai ya sake sabuwar al'wala.
:- *SALLAH* Mutum zeyi Sallah Raka'a biyu.
:- *LOKACIN DA AKE YIN ADDU'AR:*
Ana karanta addu'ar istikharan Bayan an idar da sallah, sannan kuma mutum ze iya karanta addu'ar istikharar bayan ya gama karatun tahiya lokacin daya kammala salatul ibrahim kafin ya yiya sallama.
:- *KAFIN MUTUM YA FARA ADDU'A* Zai fara da yabo da kirari ga Allah madaukakin sarki, Sannan sai yayi salatul ibrahim daga nan sai yayi addu'ar istikharar bayan ya kammala addu'ar sai ya rufe addu'ar da Salati ga Manzon Allah ﷺ Salatul ibrahim mutum zeyi.
:- *IDAN MUTUM YANA HALIN TSARKI* to ya jira har sai ya samu tsarki k**ar me haila, jinin haihuwa dasauransu. baya halatta ayi sallar sai ana da cikakken tsarki. Amma idan ana tsoron Abinda za'ayi istikharar akan sa zai ku'bucewa kuma ana halin rashin tsarki to adaidai lokacin sai a nemi zabin Allah ta hanyar yin Addu'ar kawai ba tare da anyi sallar ba.
:- *IDAN MUTUM BE HADDACE ADDU'AR BA* Babu laifi ya rubuta a wani abin yana Kallon addu'ar yana karantawa Amma a haddace addu'ar shine yafi.
:- *IDAN MUTUM BE IYA KARANTA RUBUTUN LARABCIN BA* Babu laifi ya karanta addu'ar da hausa Amma a karanta da larabcin shine yafi.
:- *KASKANTAR DA KAI WAJEN NEMAN ZABIN ALLAH* ana so mutum ya dukufar da kansa wajen neman zabin ubangijinsa ya ajiye zabin zuciyarsa kada ya rinjayar da abinda yafi so yayin istikharar.
:- *SANYA YAQINI* ana so mutum ya sanya yaqini cewa lallai ubangiji zai datar dashi akan abinda shine mafi alkhairi a gare shi.
:- *TATTARA ZUCIYARSA YAYIN ADDU'AR* ana so mutum ya tattara zuciyarsa a lokacin fara addu'ar tare da tadabburin (hakaito ma'anonin) abin da addu'ar ta kumsa.
:- *HANYAR DA MUTUM ZAI GANE ZABIN ALLAH* mutum zaiji ɗaya daga cikin al'amuran da yayi istikharar yafi kwanta masa a cikin ransa kuma za'a iya daukan dan lokaci kafin yaji hakan, sabida haka Ba mafarki mutum zeyi a nuna masa zabin nasa ba Kamar yadda wasu suke faɗa, a'a kawai abin da yake shine mafi alkhairi mutum zaiji yafi kwanta masa a ransa zaiji yafi nutsuwa daga cikin abubuwan daya nemi zabin, misali idan yaji abin ya fice a ransa bayan yayi addu'ar to kawai sai abar al'amarin, idan kuma yaji abin yayi matukar kwanta masa a cikin ransa shikenan sai ya rinjarayar da abin. idan kuma beji ya karkata a ɗaya daga cikin abubuwan biyu ba Sai ya sake istikharar haka zai tayi har zuwa lokcin da zabin mahaliccinsa ya bayyana agareshi.
:- *BABU LAIFI MUTUM YAYI ISTIKHARA SAMA DA SAU ƊAYA* Babu laifi a maimaita istikhara fiye da sau ɗaya idan yayi istikharar kuma be samu tabbaci a cikin zuciyar tasa ba, babu wani adadi da shari'a ta iyakance da ake yin istikhara.
Sannan yaku yan uwa kusani soyayyar manzon Allah ﷺ
Baa iya baki takeba dole said munyi koyi dashi. Munyi aiki da abnda y koyar
ﷺ
allah. Ya datar damu akan sunnah annabi ﷺ
Wallahu A'alam
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ , ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.