27/09/2026
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kara mafi ƙarancin albashin ma’aikata na kasa.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa da Dabarun Yaɗa Manufofin Kwamitin Kamfen na ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi ya janyo tashin farashin kayayyaki masu muhimmanci, lamarin da ya jefa ’yan Najeriya da dama cikin mawuyacin hali.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya goyi bayan bukatar ƙungiyoyin ƙwadago na neman ƙarin albashi mai yawa, inda ya zargi gwamnatin Tinubu da jagorantar wani yanayi na matsin tattalin arziki mai tsanani, wanda a cewarsa, ma’aikata na karɓar ƙarin albashi a takarda, amma a zahiri rayuwarsu ta na ƙara yin tsauri.
Ya ce mafi ƙarancin albashin da ake biya a Najeriya a yanzu bazai wadatar da bukatun iyalai ba.