06/12/2025
MAZAN JIYA
Alhaji Tanko yakasai (ya cika shekaru 100)
Mutumin daya shekara 100 a duniya kuma yana gabatar da rayuwarsa kamar kowa Alhaji Tanko yana Amfani da kafafen sada zumunta har yanzu K**ar yanda yayiwa bbc bayani
Waye Alhaji Tanko yakasai
Alhaji Salihu Abukakar Tanko Yakasai, OFR, Bahaushen Kano ne sannan kuma Bacambe a asali. Musulmi ne shi kuma mabiyin Ɗariƙar Ƙadiriyya. Gogagge ɗan siyasa, jajirtacce kuma cikakken ɗan kishin ƙasa,
wanda a lokacin da ake yin wannan rubutu, yana da shekaru 75 yana siyasa (1949 – 2025). Yana tsoma bakinsa Alhaji Tanko Yakasai, kamar yadda aka fi saninsa, makarancin Al-Ƙur’ani ne, sannan kuma masanin sauran fannonin addini bakin gwargwado, kuma ɗan jarida. Haka nan ma kuma a fannin karatun zamani ba a bar shi a baya ba, ya kwashi rabonsa kamar yadda wannan rubutu zai tantance.
Alhaji Tanko Yakasai, mutum ne ɗan fafutikar ƙwatar ‘yanci. Da su aka kafa jama’iyyar talakawa ta NEPU, kuma s**a zauna a cikinta daram, tun daga lokacin ƙyanƙyasarta, har zuwa ƙarshen rugujewar jamhuriyya ta farko a Najeriya, wanda hakan ne ya sabauta rugujewar dukkanin wasu jama’iyyun siyasa na wacan lokacin.
Da shi aka yi jamhuriyya ta farko, ta biyu, ta uku da kuma ta huɗu wacce yanzu (2025) ake cikinta. Ya ga juyin mulkin soja na farko, sannan kuma ya ga na ƙarshe a wannan ƙasa ta Najeriya. Yana da gogayayyar fafutikar ƙwatar ‘yanci tun daga gida Najeriya har zuwa ƙasashen ƙetare. Da shi aka samawa Najeriya ‘yanci daga hannun Turawa. Duk wanda ya san wannan suna ‘Tanko Yakasai’, a Najeriya da ƙasashen ƙetare, to a fagen fafutikar ƙwatar ‘yanci ya san shi. Haƙiƙa, akwai darrusan ɗiba a cikin rayuwar wannan bawan Allah.
Wannan tarihi na wannan bawan Allah, an ciro ne daga littafin da shi ya rubuta da hannunsa, wanda aka yiwa take da ‘Tanko Yakasai The Story of Humble Life An Auto Biography’, wanda ya ke juzu’i biyu ne; juzu’in farko yana da shafuka 527, juzu’i na biyu kuma yana da shafuka 487.
Tsawon lokacin da ya ɗauka a yana fafutikar siyasa da ƙwato ‘yancin ɗan’adam, Alhaji Tanko Yakasai ya haɗu da abubuwan da lissafo su ke da matuƙar wahala. Wahalhalu da s**a haɗa da muzantawa, musgunawa, rashin abinci da sha musamman lokacin NEPU, tafiyar ƙasa a cikin mawuyacin hali, da kuma uwa-uba ɗauri, suna daga cikin abubuwan da ya fuskanta kuma ya jure, tare kuma da jajircewa a kan abin ya saka a gaba.
Bincike ya tabbatar da cewa, kusan daga shekarar 1953 zuwa 1986, shi ne ɗan siyasar da aka fi ɗaure wa a duk faɗin Najeriya. Ya sha ɗaure-ɗaure ciki kuma har da zaman ƙiriƙiri. An ɗaure sau uku a zamanin Turawa kafin samun ‘yancin ƙasa, sau uku kuma a cikin jamhuriyya ta farko, sai kuma ɗauri biyu da ya sha a hannun gwamnatin sojoji biyu; shugaba Muhammadu Buhari da kuma shugaba Ibrahim Badamasi Babangida, abin da ya kai adadin ɗaure-ɗauren da ya sha zuwa ɗauruka takwas.
Ya rike mukaman gwamnati da dama kamar haka
1967 – 1971 ya zama kamishinan yaɗa labarai na jahar Kano.
1971 – 1972 ya zama kamishinan ma’aikatar gandun daji, raya karkara da kuma kwafarati (Forestry, Community Dev. and Cooperatives) na jahar Kano.
1972 – 1975 ya zama kamishinan ma’aikatar kuɗi ta jahar Kano.
1973 – 1975 ya zama mamba na hukumar gudanarwar babbar makarantar harkokin ƙasa-da-ƙasa (Nigerian Institute of International Affairs) ta Najeriya.
1979 – 1983 ya riƙe muƙamin mai baiwa shugaban ƙasa shawara da shiga tsakanin majalisar Najeriya.
Allah ya kara masa lafiya da tsawon rai
Mun tattaro bayanan a rumbun ilmi✍️
ULT MEDIA