02/10/2026
Dokar da ta hana hawan Dawakai a Kano tana nan Daram.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa dokar hana hawan dawakai a jihar Kano tana nan daram.
Kwamishinan ya ce gwamnatin Jihar Kano ce ta sanya dokar ne bayan tuntubar hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da zaman lafiya da kiyaye doka da oda a jihar.
Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro za su tabbatar da bin dokar yadda ya kamata.