07/10/2025
An bukaci mutan da aka dorawa alhakin rage kudin aikin Hajjin shekarar 2026 da suduba yuwuar rage kudin zuwa miliyan hudu kwatankwacin rabin kudin kujerar da a aka ambata a baya.
Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya bukaci hakan a zantawarsa da manema labarai a jihar Kano.
Acewarsa hakan zai bayar da dama ga alummar Musulmi masu shirin zuwa kasar Saudiyya domin yin ibadar aikin Hajjin na shekarar 2026.
Hakan ya biyo bayan umarnin da shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar ga Hukumar Kula da Aikin Hajii ta Najeriya NAHCON kan rage kudin kujerar aikin Hajjin shekarar 2026 da ta sanar da ya kai sama da Naira Miliya Takwas.
Tijjani Bala yace rage kudin zuwa miliyan hudu zai taimaki alummar Musulmi sanan zai bayar da damar kara samun yawan alhazai a wannan shekara fiye da shekarar da ta gabata.
Idan za a iya tunawa Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya taba yin kira ga shugaban Kasa Tinubu kan ya kan ya rage kudin kujerar da kaso hamsin kamar yadda ya yi ga mabiya addinin Kirista.