03/09/2025
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna yiwuwar samar da ‘yan sandan jihohi don magance matsalolin tsaro tare da ƙara bai wa masu gadin dazuka kayan aiki na zamani.
Ya koka da yadda ake siyasantar da batun, yana mai cewa jihohi da ke fama da matsalar tsaro na buƙatar rundunar da ta fahimci al’adu da yanayin yankin. Haka kuma ya bayyana amincewa da ƙarin siyan jirage marasa matuka don inganta tsaro.
Sai dai har yanzu batun ‘yan sandan jihohi na cigaba da jan lokaci a tattaunawar gwamnati, duk da cewa mafi yawan jihohi sun nuna goyon baya tun bara.