JMC HAUSA TV

JMC HAUSA TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from JMC HAUSA TV, Broadcasting & media production company, Kano.

Shirye-Shiryenmu ya ta'allaka ne kan:

Wayar da kan al'umma * Shawarwari kan aure da dangantaka *Gina zaman lafiya a iyali * Tarbiyya da haɓaka ɗabi'u * Lafiyar tunani da walwalar iyali *

Zaku iya tuntubar mu 08032323361

16/08/2026

Wanda ya fita zakka wato Black Sheep yana aikata wasu dabi'u da iyayensa s**a so aikatawa a baya ta hanyar kwayoyin halittar gado.

13/08/2026
13/08/2026

Bambancin damuwa tsakanin maza da mata

12/08/2026

Meyasa Idan mutum ya razana yake jin bayan gida ko fitsari ?

12/08/2026

Dabi'ar ji-ji da kai

12/08/2026

Hanyoyin guras da bacin rai da fushi.

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da rabon takardun mallakar filaye ga matasa 1,000 da s**a fito daga kananan hukumomi 44...
12/08/2026

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da rabon takardun mallakar filaye ga matasa 1,000 da s**a fito daga kananan hukumomi 44 na jihar, domin ba su damar mallakar kadarori da kuma samun wata hanya ta gina makomar rayuwarsu.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ya wakilta, ya jaddada muhimmancin matasa wajen ci gaban al'umma da tabbatar da dorewar gwamnati.

Gwamnan ya bayyana cewa rabon filayen wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na samar wa matasa damarmaki, tare da karfafa musu gwiwar dogaro da kansu da kuma zuba jari wajen makomarsu.

Shi kuwa Kwamishinan Kasa da Tsare-tsare na Jihar Kano, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ya ce shirin na daga cikin hanyoyin da gwamnatin jihar ke bi wajen inganta tsarin rabon filaye da dakile matsalar karbar fili ba bisa ka'ida ba, wadda ake kira “Awon-igiya”.

Kwamishinan ya bukaci wadanda s**a amfana da shirin da su kiyaye filayen da aka ba su, tare da kauce wa sayar da su cikin gaggawa. Ya ce ya kamata su mayar da wannan dama zuwa wata hanya ta samar da ingantacciyar makoma.

Ya kuma bayyana cewa filayen da aka ware suna karkashin ikon gwamnati, kuma an tsara rabonsu ne bisa tsarin kwararru, inda aka tanadi wuraren da za a iya samar da makarantu, asibitoci da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.

09/08/2026

Tasirin kwarin gwiwa confidence

Cikin kyawawan ɗabi'un Professor Isa Ali Ibrahim Pantami da na sani, kuma al'umma ke yabonsa a kai, shi ne taimaka wa mu...
06/08/2026

Cikin kyawawan ɗabi'un Professor Isa Ali Ibrahim Pantami da na sani, kuma al'umma ke yabonsa a kai, shi ne taimaka wa mutane ba tare da nuna fifiko ba.

A lokacin da yake Minista, na aiko masa da saƙon neman sahalewa ta hanyar email. Duk da cewa bai san ni ba, da kansa ya ɗauki email ɗina, ya ba da umarni a nemo ni.

Wannan abin alfahari ne a gare ni, kuma lamari ne da ba zan taɓa mantawa da shi ba.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when JMC HAUSA TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share