04/11/2025
An samu cacar baki a zauren Majalisar Dattawa tsakanin Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, da Mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin, kan yadda majalisar za ta mayar da martani ga barazanar tsohon Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, wanda ya yi ikirarin cewa za a iya kai harin soja a Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci.
Rahotanni sun nuna cewa yayin zaman majalisar a ranar Talata, Sanata Barau Jibrin ya nemi majalisar ta fitar da matsaya mai ƙarfi kan maganganun Trump, yana mai cewa dole ne majalisar ta kare mutuncin ƙasar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai Akpabio ya katse shi, yana mai cewa “batun siyasar ƙasashen waje ba na majalisar ba ne kai tsaye, kuma akwai hanyoyi na diflomasiyya da za a bi.”
Wannan kalmar ta jawo muƙabala mai zafi tsakanin shugabannin biyu, inda Barau ya dage cewa “idan majalisar dattawa ba ta nuna bakin cikinta ba, za a ɗauke mu a matsayin masu rauni a idon duniya.”
A ƙarshe, majalisar ta amince da kafa kwamitin musamman da zai tattauna da Ma’aikatar Harkokin Waje don samar da sanarwar hadin gwiwa, wacce za ta nuna matsayin Najeriya cikin natsuwa da mutunci.