08/05/2026
A Hukumance: Fede Valverde ya saki sanarwa a shafinsa na Instagram:
“Jiya na samu saɓani da wani abokin wasana lokacin da muke ɗaukar horo. Gajiya na fafatawar da muke da kuma takaicin rashin nasara ne yasa komai yayi tsamari a tsakanin mu.
A cikin ɗakin sanya tufafi, ire-iren waɗannan abubuwan suna faruwa domin yau da kullum tafi ƙarfin wasa, kuma galibi ana magance su ne a cikin gida ba tare da sun fito fili ba.
A bayyane yake cewa akwai wani a cikin mu da yake yaɗa jita-jita, kuma duba da cewa kakar wasan nan ba mu lashe kofina ba, Real Madrid tana fuskantar s**a kowanne lokaci, hakan yasa komai yake zama abun magana.
Yau ma mun sake samun rashin fahimta da wannan abokin wasan nawa. Yayin da muke cacar baki, cikin kuskure na bugi teburi, wanda hakan ya janyo min ɗan rauni a goshina wanda sai da ya buƙaci zuwa asibiti domin duba lafiyata. Babu wani lokaci da abokin wasa na ya mare ni, nima kuma ban mare shi ba, ko da yake na san sai yafi muku daɗi idan kunji cewa mun kaiwa juna hannu ko kuma da gangan hakan ta faru, amma dai hakan ba gaskiya ba ne.
Ina ba da haƙuri. Na shirya karbar dukkan wani hukunci da ƙungiyar nan ta yanke akan mu, bani da tantama cewa duk wani saɓani da zamu iya samu a wajen fili yana ƙarawa ne da zaran mun shiga filin wasa, kuma idan har akwai wanda zai kare ƙungiyar nan a cikin fili, to ni ne na farko. Bani da niyyar yin magana sai kakar wasa ta ƙare.
Na ji baƙin ciki da raɗadin shiga wannan yanayi da zai hana ni buga wasa na gaba saboda shawarar Likitoci. A kowanne lokaci ina bayar da dukkan ƙoƙarina ga ƙungiyar nan har zuwa ƙarshe, kuma hakan yana min ciwo fiye da kowa sakamakon rashin samun damar buga wasa. A shirye nake na haɗa kai da ƙungiya ta da kuma abokan wasa na kan duk wata shawara da s**a ga ya dace a ɗauka.
Na gode.”