29/06/2026
Wata malamar makaranta mai shekara 22, Maryam Usman, wadda ke koyarwa a Makarantar Brains Minds Nursery and Primary School da ke Ugbamaka-Igah a Ƙaramar Hukumar Olamaboro ta Jihar Kogi, ta rasu bayan da ake zargin mahaifin ɗaya daga cikin ɗalibanta ya jagoranci dukan ta saboda ta hukunta ɗansa.
Lamarin ya fara ne a ranar 17 ga Yuni, lokacin da Maryam ta hukunta ɗalibin bisa laifin rashin ɗa’a a makaranta. A yayin hakan, ana zargin yaron ya faɗi ƙasa kuma ya ji rauni a hannunsa.
Bayan faruwar lamarin, mahaifin yaron, mai suna Ishaq Abdullahi, tare da wasu mutum biyu, ana zargin sun je gidan Maryam inda s**a kai mata hari a ranar. An kuma ce daga baya an sake kai mata hari yayin da take kan hanyarta ta zuwa masallaci.
A cewar ɗan’uwan marigayiyar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, an sake kai wa Maryam hari a ranar 18 ga Yuni tare da wasu ƙarin mutane, lamarin da ya jikkata ta sosai har ta suma.
Ya ce: “Da farko an kai ta wani ƙaramin asibiti, daga bisani aka mayar da ita wani asibiti a garin Okpo. Sai dai duk da ƙoƙarin ceto rayuwarta, lafiyarta ta ci gaba da tabarbarewa har ta rasu da misalin ƙarfe 5:00 na safiyar ranar 25 ga Yuni, 2026.”
Ya yi kira ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da cewa an hukunta duk waɗanda ke da hannu a lamarin.
Wani dattijon al’ummar yankin mai suna Drisu ya shaida cewa marigayiyar da iyalan ɗalibin dangin juna ne. Ya ƙara da cewa iyalan biyu sun gudanar da tarurruka da dama domin sasanta lamarin.