15/10/2025
🚨 AN KARYA TARIHIN RONALDO! 🤯
Cristiano Ronaldo ya taba cin kwallo da bicycle kick a tsayin 2.38m (7ft8) — amma yanzu an karya wannan tarihin! 😳
🇳🇬 Paul Onuachu, ɗan wasan Najeriya da ke bugawa a Trabzonspor, ya kafa sabon tarihi bayan ya ci kwallo da kai a sama da tsayin 2.41m (7ft9) a wasan su da Fatih Karagümrük! 🔥
Onuachu yana da tsayin 6ft7 (201cm), amma duk da haka ya zarce Ronaldo da ‘yan santimita kaɗan — abin mamaki sosai! 😮💨⚽
Ko kuna ganin za a iya karya wannan sabon tarihin nan gaba? 🤔
Labaran Kwallon Kafa Hausa