MGC Hausa

Website

MGC Hausa Kafar yada Labarai da rahotanni, wasannin da kuma shirye-shirye masu ilmantarwa da debe kewa daga shafin MGC hausa a ko ina a fadin Duniya.

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a a Nigeria JAMB ta sanar da cewa daga zangon karatu na 2026/2027, ba za a ƙara guda...
22/06/2026

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a a Nigeria JAMB ta sanar da cewa daga zangon karatu na 2026/2027, ba za a ƙara gudanar da shirye-shiryen digiri a kwalejojin ilimi Colleges of Education masu alaƙa da jami’o’i ba.

A cewar hukumar, takardar shaidar NCE National Certificate in Education ce kawai za ta kasance hanyar shiga da karatu a kwalejojin ilimi.

Haka kuma, an dakatar da shigar ɗalibai kai tsaye zuwa matakin digiri a waɗannan cibiyoyi.

JAMB ta bayyana cewa wannan mataki zai kawo ƙarshen tsarin da kwalejojin ilimi ke amfani da haɗin gwiwa da jami’o’i wajen ba da digiri ga ɗalibai.

Sabon tsarin zai shafi dubban ɗaliban da s**a riga s**a zaɓi kwalejojin ilimi domin yin digiri a shekarar 2026.

Domin rage matsalar da sauyin zai iya haifarwa, hukumar ta ba wa ɗaliban da abin ya shafa damar sauya cibiyar karatu ba tare da biyan kuɗi ba, ko kuma a tura su zuwa jami’ar da ke da alaƙa da shirin digirin da s**a zaɓa.

Sannan za su iya sauya zaɓinsu zuwa NCE idan suna so.

JAMB ta umarci dukkan cibiyoyin ilimi, cibiyoyin jarabawar CBT da jami’anta a faɗin ƙasar su bi sabbin ƙa’idojin domin tabbatar da aiwatar da tsarin yadda ya k**ata.

Wannan sauyi na da nufin ƙarfafa tsarin horas da malamai, inda NCE zai zama muhimmin mataki kafin shiga aikin koyarwa ko ci gaba da karatu a manyan makarantu.

MGC Hausa BBC Hausa
Shamsu Lawal Maitakobi

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa ilimantar da ’ya’ya mata na daga cikin hanyoyin da s**a fi ...
22/06/2026

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa ilimantar da ’ya’ya mata na daga cikin hanyoyin da s**a fi tasiri wajen rage talauci da magance matsalolin zamantakewa da tattalin arziki a Nijeriya.

Ya ce ilimin ’ya mace yana taimakawa wajen rage mutuwar mata masu juna biyu, rashin abinci mai gina jiki da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Haka kuma yana taimakawa wajen tsara iyali da rage haihuwa ba tare da tsari ba.

Sanusi ya yi wannan bayani ne a taron kammala karatu na farko na Miva Open University da aka gudanar a Lagos.

Ya jaddada cewa ilimi haƙƙin kowa ne, ba gata ba, sannan ya shawarci waɗanda s**a kammala karatu da su mayar da hankali wajen ƙirƙirar ayyukan yi maimakon jiran gwamnati ko kamfanoni su ba su aiki.

MGC Hausa BBC Hausa
Federal Capital Territory, Nigeria
Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi ll
Sanusi Lamido Sanusi

🌹 Saƙon Addu’a da Fatan Alkhairi Na Ranar Uba Ta Duniya 🌹A wannan rana ta musamman ta Uba ta Duniya, muna taya dukkan iy...
21/06/2026

🌹 Saƙon Addu’a da Fatan Alkhairi Na Ranar Uba Ta Duniya 🌹

A wannan rana ta musamman ta Uba ta Duniya, muna taya dukkan iyaye maza murna tare da yi musu addu’ar Allah Ya ƙara musu lafiya, nisan kwana, hikima da albarka, Allah ya saka musu da alkhairi bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kula da iyalansu da tarbiyyar 'ya'yansu.

Allah ya gafarta wa iyayenmu da s**a rasu ya haskaka musu kabarinsu, ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsu, ya kuma ba waɗanda suke raye zaman lafiya, farin ciki da nasara a rayuwarsu.

Muna roƙon Allah Ya cigaba da kare dukkan iyaye daga dukkan sharri da bala’i, yasa su ga alfarmar 'ya'yansu, ya kuma albarkaci gidajensu da zaman lafiya da haɗin kai.

Barka da Ranar Uba Ta Duniya! 💐❤️ Allah Ya albarkaci dukkan iyaye ya saka musu da mafificin alkhairi. Amin. 🤲

MGC Hausa.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun taimaka wajen mayar...
21/06/2026

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun taimaka wajen mayar da iskar gas a matsayin ginshiƙin shirin bunƙasa masana'antu da tattalin arzikin Najeriya.

Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Mak**ashi Misis Olubukola Arowolo Verheijen, ce ta bayyana hakan yayin taron Ranar Mak**ashi da Ƙungiyar Kasuwanci ta Najeriya da Birtaniya ta shirya a birnin Legas.

Ta ce iskar gas na taka muhimmiyar rawa wajen samar da wutar lantarki, tafiyar da masana'antu, samar da takin zamani, harkokin sufuri da kuma fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.

Verheijen ta bayyana cewa Najeriya na da tabbatattun ma'adanan iskar gas da s**a haura tiriliyan 215 na cubic feet, lamarin da ke nuna irin dimbin albarkatun da ƙasar ke da su a wannan fanni.

Ta kuma ce amincewar masu zuba jari a harkar mai da gas ta ƙaru sosai sak**akon sauye-sauyen da gwamnati ta aiwatar.

A cewarta, yawan masu amfani da na'urorin auna wutar lantarki ya kai kusan kashi 57 cikin 100 a faɗin ƙasar, yayin da kusan kashi 45 cikin 100 na kasuwar wutar lantarki ke aiki a ƙarƙashin tsarin kuɗin wuta da ya dace da irin sabis ɗin da ake bayarwa.

Masana da shugabannin harkokin mak**ashi da s**a halarci taron sun jaddada muhimmancin amfani da albarkatun iskar gas da ake da su a cikin gida domin bunƙasa tattalin arziki, haɓaka masana'antu, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa tsaron mak**ashi.

Sun bayyana cewa harkar gas na daga cikin muhimman ginshiƙan da za su taimaka wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da wadata ga Najeriya a nan gaba.

MGC Hausa BBC Hausa
DCL HAUSA
Shamsu Lawal Maitakobi
Federal Capital Territory, Nigeria

Gwamnatin Tarayya ta amince da sakin naira miliyan 21.2 ga kowace jiha a faɗin ƙasar nan domin ƙarfafa shirye-shiryen ka...
21/06/2026

Gwamnatin Tarayya ta amince da sakin naira miliyan 21.2 ga kowace jiha a faɗin ƙasar nan domin ƙarfafa shirye-shiryen kariya da kuma gaggawar ɗaukar matakai kan cutar Ebola da sauran barazanar da ka iya tasowa a fannin lafiyar jama'a.

Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama'a na Ƙasa Farfesa Muhammad Ali Pate, ya umarci Hukumar Dakile da Yaɗuwar Cututtuka ta Najeriya NCDC da ta gaggauta fitar da kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen Asusun Bincike da Yaki da Barkewar Cututtuka da aka ware wa jihohi.

Ma'aikatar Lafiya ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ƙara ƙarfafa tsarin sa ido kan cututtuka, shirye-shiryen tunkarar gaggawa da kuma tsarin mayar da martani cikin sauri idan wata annoba ta ɓarke a ko'ina cikin ƙasar.

Ta ce duk da cewa a halin yanzu ba a samu ko da mutum ɗaya da aka tabbatar yana ɗauke da cutar Ebola a Najeriya ba, gwamnati na ɗaukar matakan kariya tun kafin wata barazana ta taso domin kare lafiyar al'umma.

Haka Zalika, Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkan jihohi da su gabatar da cikakken bayanin yadda s**a kashe kuɗaɗen da aka saki a baya da kuma waɗanda za a sake fitarwa yanzu cikin watanni shida masu zuwa.

Gwamnatin ta jaddada muhimmancin gaskiya riƙon amana da bin ƙa'idojin gudanar da kuɗaɗen jama'a, tana mai cewa dole ne a tabbatar da cewa an yi amfani da waɗannan kuɗaɗe yadda ya k**ata domin kare lafiyar 'yan Najeriya.

MGC Hausa BBC Hausa
Mınna, Nıger State
DCL HAUSA Ebola
Federal Capital Territory, Nigeria

Hukumar Tsaro da Kariya ta Farin Kaya ta Najeriya NSCDC reshen Jihar Neja, ta ce ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu harkar...
21/06/2026

Hukumar Tsaro da Kariya ta Farin Kaya ta Najeriya NSCDC reshen Jihar Neja, ta ce ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu harkar haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a yankin M.I. Wushishi da ke Minna.

A cewar hukumar, jami'anta na rundunar musamman mai kula da harkokin ma'adanai sun gudanar da wani samame da sanyin safiyar ranar Lahadi bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan da ake zargin ana yi ba bisa doka ba a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa an k**a wasu mutane da ake zargi da saye, sayarwa da kuma safarar zinari da sauran albarkatun ma'adanai ba tare da lasisin da doka ta tanada ba.

Kwamandan NSCDC na Jihar Neja Suberu Siyaka Aniviye, ya bayyana cewa haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba na barazana ga tsaron ƙasa tattalin arziki da kuma muhalli.

Ya ce irin waɗannan ayyuka na haifar da asarar kuɗaɗen shiga ga gwamnati tare da jefa rayuka da dukiyoyi cikin haɗari.

Ya sake jaddada aniyar hukumar na tabbatar da bin dokokin da s**a shafi harkokin ma'adanai, tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a ayyukan da s**a saɓa wa doka.

Hukumar ta kuma tabbatar wa al'ummar jihar cewa za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki domin kare albarkatun ma'adanan Najeriya da tabbatar da cewa ana amfana da su ta hanyar da ta dace da doka.

MGC Hausa BBC Hausa DCL HAUSA (Readers) Nigeria Security and Civil Defence Corps
Shamsu Lawal Maitakobi
Mınna, Nıger State

Address

Kano Municipal
Kano
11

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MGC Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share