RBG Hausa

RBG Hausa Gaskiya Cikin Rahoto shine manufar mu

Jihar Kano ta samu ƙaruwar kuɗaɗen shiga daga gwamnatin tarayyaRahotanni sun nuna cewa Jihar Kano tana samun ƙaruwa a ku...
11/10/2025

Jihar Kano ta samu ƙaruwar kuɗaɗen shiga daga gwamnatin tarayya

Rahotanni sun nuna cewa Jihar Kano tana samun ƙaruwa a kuɗaɗen da ake rarrabawa daga asusun tarayya a wannan shekarar ta 2025.
Wannan yana nuna cewa ana samun cigaba a tattalin arzikin ƙasa, musamman daga kudaden da ake samu daga fannin mai da kuma waɗanda ba na mai ba.
Binciken da aka yi daga bayanan hukumomin gwamnati ya tabbatar da cewa a cikin watanni takwas na farko na shekarar 2025, gwamnatin jihar Kano da ƙananan hukumomi 44 na jihar suna samun ƙaruwar kuɗaɗen shiga daga gwamnatin tarayya.
Masana sun ce wannan al’amari yana nuna cewa Kano tana cikin wani lokaci na kwanciyar hankali a fannin kuɗi, wanda hakan na iya taimakawa wajen inganta ayyukan raya ƙasa da walwalar jama’a.
Kamar yadda alkaluma s**a nuna ƙananun hukumomin Kano sun karɓi kuɗin da yakai Naira biliyan 348.2, daga gwamnatin tarayya a cikin watanni 8.

Cc: DN24hausa

゚ ゚followers ゚viralシ

Harajin Shugaban Amurka Ya Karya Kasuwar KiriftoAn samu girgizar kasuwa bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana yi...
11/10/2025

Harajin Shugaban Amurka Ya Karya Kasuwar Kirifto

An samu girgizar kasuwa bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana yiwuwar sanya haraji kan kayayyakin China, abin da ya haifar da karyewar farashin hannayen jari da kuɗaɗen intanet na kirifto.
Farashin Bitcoin ya fadi da sama da kashi 10 cikin 100 kafin daga baya ya ɗan farfaɗo.
Haka kuma sauran kuɗaɗen kirifto kamar Ethereum da Solana suma sun shiga halin koma-baya.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin China ta sanar da tsauraran dokoki kan fitar da ma’adanan da ake amfani da su wajen ƙere-ƙeren fasahar zamani zuwa Amurka.

Cc: DN24hausa

゚ ゚followers ゚viralシ

’Yan Sanda Sun Ceto Mutane 10 da ’Yan Bindiga S**a Yi Garkuwa da Su a KadunaRundunar ’yan sanda reshen Kaduna ta tabbata...
11/10/2025

’Yan Sanda Sun Ceto Mutane 10 da ’Yan Bindiga S**a Yi Garkuwa da Su a Kaduna

Rundunar ’yan sanda reshen Kaduna ta tabbatar da cewa ta ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su tun watanni hudu da s**a gabata a ƙaramar hukumar Kagarko.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana cewa daga cikin mutanen da aka ceto akwai yara masu shekaru ɗaya, uku, da kuma 13. An sace su ne lokacin da ’yan bindiga s**a kai hari ƙauyen Kushe Makaranta s**a kuma kai su dajin da ke kusa da Rijana.
DSP Hassan ya ce aikin ceton ya samu ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin rundunar ’yan sanda, DSS, da sojojin Najeriya.

Cc: DN24hausa

゚ ゚followers ゚viralシ

FARASHIN CFAYadda farashin kasuwar bayan fage ke gudana tsakanin Sefa zuwa Naira a yau 11 ga watan Oktoba 2025.darajar c...
11/10/2025

FARASHIN CFA

Yadda farashin kasuwar bayan fage ke gudana tsakanin Sefa zuwa Naira a yau 11 ga watan Oktoba 2025.
darajar canjin kudaden;
farashin cfa f(xop) siya:::2600
siyarwa:::2700
farashin cfa f(xaf)siya:::2420
siyarwa:::2500
Farashin cfa zuwa naira na canzawa kowane sa’o’i.
Farashin musaya yana jujjuyawa, ya danganta da adadin cfa da ake da su da kuma bukatarsu.
Zaku iya samun dukkan bayanai da kuma farashin cfa zuwa naira a wannan shafi.

𝙁𝘼𝙍𝘼𝙎𝙃𝙄𝙉 𝘿𝘼𝙇𝘼Yadda farashin kasuwar bayan fage ke gudana tsakanin Dala zuwa Naira a yau 11 ga watan Oktoba 2025.Darajar ...
11/10/2025

𝙁𝘼𝙍𝘼𝙎𝙃𝙄𝙉 𝘿𝘼𝙇𝘼

Yadda farashin kasuwar bayan fage ke gudana tsakanin Dala zuwa Naira a yau 11 ga watan Oktoba 2025.
Darajar canjin kudaden;
Farashin siya ₦1,492
Farashin siyarwa ₦1,500
Dalar Amurka zuwa Naira na canzawa kowane sa’o’i.
Farashin musaya yana jujjuyawa, ya danganta da adadin daloli da ake da su da kuma bukatarsu.
Zaku iya samun dukkan bayanai da kuma farashin Dala zuwa Naira a wannan shafin, gami da farashin CBN.

Assalamu alaikumMasu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, barka da wannan lokaci.Da fatan kun wayi gari lafiya a wann...
11/10/2025

Assalamu alaikum
Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, barka da wannan lokaci.

Da fatan kun wayi gari lafiya a wannan rana ta Asabar 19 Rabi II 1447 wanda yayi daidai da 11/10/2025. Yanzu karfe 1:43 am agogon Nijeriya, Nijar da kamaru, Karfe nawa agogon ku a daidai wannan lokaci?
𝙆𝙐𝙉𝘼 𝙆𝘼𝙍𝙁𝘼𝙁𝘼 𝙈𝘼𝙉𝘼 𝙂𝙒𝙄𝙒𝘼 𝘿𝘼 𝘾𝙊𝙈𝙈𝙀𝙉𝙏 𝙇𝙄𝙆𝙀 𝙎𝙃𝘼𝙍𝙄𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙍𝙀 𝘿𝘼 𝘽𝙄𝘽𝙄𝙔𝘼𝙍𝙈𝙐 𝘿𝘼 𝙆𝙐𝙆𝙀 𝙔𝙄
Sai ku kasance da mu kamar koda yaushe da za mu kawo maku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
RBG HAUSA... (Gaskiya cikin Rahoto)

Ma’aikatan jami’o’i sun yi zanga-zangar rashin albashi a Kano da wasu jihohiKungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da ba malamai...
10/10/2025

Ma’aikatan jami’o’i sun yi zanga-zangar rashin albashi a Kano da wasu jihohi

Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba wato SSANU da NASU sun gudanar da zanga-zangar lumana a wasu jihohin ƙasar nan, ciki har da Kano, Kaduna da Nasarawa, don nuna rashin jin daɗinsu kan riƙe albashinsu da rashin aiwatar da yarjejeniyar 2009.
A Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Sabo Balarabe Wudil, Mataimakin Shugaban SSANU na ƙasa (Arewa maso Yamma), ya ce gwamnati ta kasa biyan buƙatun da aka dade ana nema ciki har da:
Albashin watanni biyu da aka riƙe tun lokacin yajin aikin 2022
Rashin biyan Naira biliyan 40 daga cikin Nairs biliyan 50 da aka amince a matsayin kudaden alawus na ma’aikatan.
Da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyar 2009.
Ya ƙara da cewa:
“Mun gaji da alƙawura. Wannan zanga-zanga ba ƙarshe ba ce, idan gwamnati ta yi shiru, za mu ɗauki mataki mafi tsanani.”
A ABU Zaria da Federal University Lafia (FULAFIA), ma’aikata sun fito zanga-zangar.
Shugaban SSANU na FULAFIA, Comrade Daniel Dajen, ya ce gwamnati ta saba yarjejeniya da ke buƙatar a sake tattaunawa kan albashi duk bayan shekara biyar.

Cc: DN24hausa

゚ ゚followers ゚viralシ

Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano ta bukaci jama’a su rika kai mata korafe-korafe kai tsayeHukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ...
10/10/2025

Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano ta bukaci jama’a su rika kai mata korafe-korafe kai tsaye

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta yi kira ga jama’a da su rika kai mata korafe-korafe kai tsaye domin taimakawa wajen tunkarar cin hanci da rashin gaskiya a matakai daban-daban na gwamnati da al’umma.
Shugaban hukumar, Kwamared Sa’idu Yahaya, ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025, a lokacin da ake bikin Ranar Ƙarɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Duniya, ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin ƙarfafa mutane su bayyana damuwarsu don neman adalci.
Kwamared Yahaya ya bayyana cewa hukumar tana da hanyoyi daban-daban na karɓar korafe-korafe daga jama’a, ciki har da kai tsaye a ofishin hukumar, ta waya, da kuma ta intanet. Ya ce kofar hukumar a buɗe take ga kowa ba tare da son rai ba.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da wayar da kan al’umma kan muhimmancin bayar da rahotannin gaskiya da bayyana matsaloli, domin tabbatar da adalci da kare amana a cikin al’umma.

Cc: DN24hausa

゚ ゚followers ゚viralシ

FARASHIN CFAFarashin Sefa a kasuwar bayan fageYadda farashin kasuwar bayan fage ke gudana tsakanin Sefa zuwa Naira a yau...
10/10/2025

FARASHIN CFA

Farashin Sefa a kasuwar bayan fage
Yadda farashin kasuwar bayan fage ke gudana tsakanin Sefa zuwa Naira a yau 10 ga watan Oktoba 2025.
darajar canjin kudaden;
farashin cfa f(xop) siya:::2600
siyarwa:::2700
farashin cfa f(xaf)siya:::2420
siyarwa:::2500
Farashin cfa zuwa naira na canzawa kowane sa’o’i.
Farashin musaya yana jujjuyawa, ya danganta da adadin cfa da ake da su da kuma bukatarsu.
Zaku iya samun dukkan bayanai da kuma farashin cfa zuwa naira a wannan shafi.

𝙁𝘼𝙍𝘼𝙎𝙃𝙄𝙉 𝘿𝘼𝙇𝘼Yadda farashin kasuwar bayan fage ke gudana tsakanin Dala zuwa Naira a yau 10 ga watan Oktoba 2025.Darajar ...
10/10/2025

𝙁𝘼𝙍𝘼𝙎𝙃𝙄𝙉 𝘿𝘼𝙇𝘼

Yadda farashin kasuwar bayan fage ke gudana tsakanin Dala zuwa Naira a yau 10 ga watan Oktoba 2025.
Darajar canjin kudaden;
Farashin siya ₦1,495
Farashin siyarwa ₦1,500
Dalar Amurka zuwa Naira na canzawa kowane sa’o’i.
Farashin musaya yana jujjuyawa, ya danganta da adadin daloli da ake da su da kuma bukatarsu.
Zaku iya samun dukkan bayanai da kuma farashin Dala zuwa Naira a wannan shafin, gami da farashin CBN.

Assalamu alaikumMasu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, barka da wannan lokaci.Da fatan kun wayi gari lafiya a wann...
10/10/2025

Assalamu alaikum
Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, barka da wannan lokaci.

Da fatan kun wayi gari lafiya a wannan rana ta Jummaa 18 Rabi II 1447 wanda yayi daidai da 10/10/2025. Yanzu karfe 7:08 am agogon Nijeriya, Nijar da kamaru, Karfe nawa agogon ku a daidai wannan lokaci?
𝙆𝙐𝙉𝘼 𝙆𝘼𝙍𝙁𝘼𝙁𝘼 𝙈𝘼𝙉𝘼 𝙂𝙒𝙄𝙒𝘼 𝘿𝘼 𝘾𝙊𝙈𝙈𝙀𝙉𝙏 𝙇𝙄𝙆𝙀 𝙎𝙃𝘼𝙍𝙄𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙍𝙀 𝘿𝘼 𝘽𝙄𝘽𝙄𝙔𝘼𝙍𝙈𝙐 𝘿𝘼 𝙆𝙐𝙆𝙀 𝙔𝙄
Sai ku kasance da mu kamar koda yaushe da za mu kawo maku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
RBG HAUSA... (Gaskiya cikin Rahoto)

Gyaran tattalin arziƙin Tinubu bai amfanar da talakawa ba–Bankin DuniyaGyaran tattalin arziƙin Tinubu bai amfanar da tal...
09/10/2025

Gyaran tattalin arziƙin Tinubu bai amfanar da talakawa ba–Bankin Duniya

Gyaran tattalin arziƙin Tinubu bai amfanar da talakawa ba–Bankin Duniya
Bankin Duniya ya bayyana cewa duk da irin gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin Najeriya ke aiwatarwa, mafi yawan ’yan ƙasa har yanzu ba su ji sauyi a rayuwarsu ba, inda kimanin mutane miliyan 139 ke ci gaba da rayuwa cikin talauci.
Wakilin Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rahoton irin cigaban da ake samu a ƙasar a birnin Abuja.
Ya ce Najeriya ta samu ci gaba wajen daidaita musayar kuɗi, rage bashi da kuma sauƙaƙe hauhawar farashi, amma wadannan nasarorin basu kai ga inganta rayuwar jama’a ba.
Verghis ya kara da cewa hauhawar farashin abinci, raguwar ƙarfin siye da rashin daidaito wajen rabon albarkatu, na daga cikin manyan abubuwan da ke jefa mutane cikin ƙuncin tattalin arziki.
A cewarsa, talauci ya ƙaru tun daga shekarar 2019 sakamakon wasu manufofi marasa kyau da kuma tasirin annobar COVID-19, lamarin da ya ci gaba duk da sabon tsarin kudi da gwamnati ta aiwatar.
Shi ma Samer Matta, babban masani kan tattalin arziki na Bankin Duniya a Najeriya, ya bayyana cewa duk da ƙarin kudaden shiga da ake samu cikin 2025, akwai matsala wajen yawan cire kuɗaɗe daga hukumomin tattara haraji, wanda ke rage tasirin gyare-gyaren tattalin arzikin ga al’umma.
Ya bukaci gwamnati ta tabbatar da cewa kuɗaɗen da ake samu suna zuwa ga ayyukan da zasu inganta rayuwar ’yan ƙasa kai tsaye.

Cc: DN24hausa

゚ ゚followers ゚viralシ

Address

Kano-Nigeria
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when RBG Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share