Dan Kalla Crypto

Dan Kalla Crypto Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dan Kalla Crypto, Digital creator, kano, London.

🦅 Dan Kalla Crypto | DEX & Crypto Education 📊
🔍 Market Research • On-Chain Analysis • Risk Management
💡 Learn Smart • Trade Responsibly • Build Your Knowledge


https://t.me/dankalladex

23/09/2026

A Gombe 🍞 Bread yafi karfin Dalaka sai de Burodi 🤦

22/09/2026

Ajinmu na October, me ya kamata mu fi mayar da hankali a kai? 👇

🚨 Yawancin masu shiga DEX suna neman "signal"... amma ba su san ainihin abin da ke motsa kasuwa ba.Abin da kake gani a w...
22/09/2026

🚨 Yawancin masu shiga DEX suna neman "signal"... amma ba su san ainihin abin da ke motsa kasuwa ba.

Abin da kake gani a wannan bidiyon ɓangare ne na darasin da muke koyarwa a cikin ajinmu na DEX Trading. 👇

A cikin ajin, ba kawai za ka koyi yadda ake saya ko sayar da token ba—za ka fahimci yadda ake bincike, gano dama tun da wuri, da kuma kauce wa kuskuren da ke jawo asarar kuɗi.

🎓 Wannan darasi na daga cikin abubuwan da ɗalibanmu suke koya a aji.

Idan kai ma kana son koyon DEX Trading daga tushe har zuwa matakin ƙwarewa, ka yi rajista ka shiga ajinmu.

📩 Rubuta "DEX" a comment ko turo mana saƙo domin samun cikakken bayani.

🔹 Tsarin Rijiyoyin Kuɗi (Liquidity Pools): Hoton ya nuna pools daban-daban na token ɗin. Kashi na farko yana da alamar m...
22/09/2026

🔹 Tsarin Rijiyoyin Kuɗi (Liquidity Pools):

Hoton ya nuna pools daban-daban na token ɗin. Kashi na farko yana da alamar makulli wanda ke nuna cewa an kulle kashi 100% na wannan LP (Locked 100%) wanda ke ɗauke da adadin token miliyan 77.89 gami da GMEx 1,507.95.

Hakanan akwai wani pool na daban da aka haɗa da Solana (SOL) wanda ke da adadin 550,887.77 na token ɗin.

An kuma nuna sashin "Bonding" wanda adadinsa yake a sifili (0), wanda hakan ka iya nuna cewa token ɗin ya riga ya kammala tsarin bonding curve.

​🔹 Mummunar Faduwar Liquidity (The Liquidity Crash): Wannan shi ne mafi girman abin lura a jadawalin (chart) da ke tsakiyar hoton.

Layin kore ya nuna wata mummunar faɗuwa daga ranar 21 ga wata zuwa 22 ga wata. Liquidity ɗin ya karye daga kusan $19,000 ya zube kasa warwas zuwa kusan $34.84 kacal a ranar 09-22! Wannan yana nufin an yi mummunan janye kuɗaɗe a kasuwar wanda ya rusa darajar kudin gaba daya.

​🔹 Ayyukan Cire Kuɗi (Liquidity Removal Transactions): A ƙasan hoton, a sashin da ke nuna mu'amalolin baya-bayan nan, ana ganin rubutu da ja mai nuna "Remove". Wani mai walet (4u...hjv7) ya janye adadin token 27,355.87 gami da 0.373 GMEx.

Wannan yana tabbatar da cewa masu samar da liquidity ko masu riƙe da shi suna fita daga wannan kasuwar.

​💡 Darasi na Binciken Kasuwa (Market Analysis Insight):
Wannan hoton cikakken misali ne na yadda ake bibiyar bayanan kan-sarka (on-chain analysis) kafin yin ciniki. Idan liquidity yayi ƙasa sosai kamar yadda wannan jadawalin ya nuna, duk wanda ke riƙe da wannan token ɗin zai sha wahala matuka wajen sayarwa saboda babu "exit liquidity" (isasshen kuɗin dake cikin kasuwar da zai ɗauki sell orders masu yawa). Koda an nuna cewa ainihin LP ɗin a kulle yake, irin wannan zabtarewar liquidity tana nuna babbar alamar haɗari (red flag).
​Wane mataki kuke ɗauka idan kuka lura liquidity na wani token da kuke so ku saya yana raguwa? Raba ra'ayoyin ku a sashin sharhi (comments) don mu tattauna! 👇

​⚠️ Gargadi Kan Kasada (Risk Disclaimer): Kasuwancin kera-keran kudi na yanar gizo (Cryptocurrency), Decentralized Exchanges (DEX), da tsarin Web3 suna dauke da babbar kasada wadda zata iya janyo asarar dukkan jarin ka. Wannan bayanin an yi shi ne domin ilimantarwa kawai, ba shawarar zuba jari bace.

Yi cikakken binciken ka (DYOR - Do Your Own Research) kafin shiga kowace irin kasuwa.

​

ATIKU KADAI YA RAGE MANA? 🇳🇬Idan ana magana ne kan siyasar tarayyar Najeriya, akwai masu ganin cewa Atiku Abubakar na da...
22/09/2026

ATIKU KADAI YA RAGE MANA? 🇳🇬

Idan ana magana ne kan siyasar tarayyar Najeriya, akwai masu ganin cewa Atiku Abubakar na daga cikin fitattun ‘yan siyasar Arewa da ke ci gaba da yin adawa da gwamnatin tarayya a fili.

Hatta Rabiu Kwankwaso, wanda mutane da dama ke kallonsa a matsayin babban ɗan siyasar Arewa, yanzu yana cikin masu bambanta matsayinsu da na Atiku a fagen siyasa. Hakan ya sa ake ganin cewa adawar siyasar Arewa ta samu sabon yanayi.

A gefe guda kuma, sau da dama fadar shugaban ƙasa tana mayar da martani ga kalaman Atiku Abubakar. Wannan ya sa Atiku ya kasance ɗaya daga cikin ‘yan siyasar da ake yawan jin muryarsu wajen s**ar manufofin gwamnatin tarayya.

Hatta a baya-bayan nan, Atiku ya yi tambaya kan wanda ke gudanar da harkokin ƙasa a lokacin da Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa ba sa cikin ƙasar. Maimakon a bar tambayar haka, lamarin ya jawo martani daga ɓangaren gwamnati, har aka yi amfani da kalmar “irresponsible” wajen bayyana matakin.

Tambayar ita ce:
Wane babban ɗan siyasa daga Arewa ne a yanzu yake yin irin wannan adawa a fili, musamman kan batutuwan da s**a shafi talakawa da tafiyar da ƙasar?

A ƙarshe, abin da ya fi muhimmanci shi ne a saurari muhawarar, a duba hujjojin ɓangarorin biyu, sannan ‘yan Najeriya su yanke shawarar abin da s**a ga ya dace da su.

Taron Crypto da ba a tabayin irinsa ba a Bauchi 🙄 Don haka saida Safe 👀
21/09/2026

Taron Crypto da ba a tabayin irinsa ba a Bauchi 🙄

Don haka saida Safe 👀

🔥 KADA KA RASA WANNAN LIVE! 🚨Anjima zan yi LIVE a Telegram channel — Dan Kalla DEX.🎯 Abubuwan da za mu tattauna:📌 FOMO: ...
21/09/2026

🔥 KADA KA RASA WANNAN LIVE! 🚨

Anjima zan yi LIVE a Telegram channel — Dan Kalla DEX.

🎯 Abubuwan da za mu tattauna:
📌 FOMO: Yadda Fear of Missing Out ke sa mutane su shiga trade ko investment cikin gaggawa saboda tsoron rasa damar samun riba — da yadda za ka gane FOMO kafin ya rinjaye ka.

📌 FUD: Menene Fear, Uncertainty & Doubt, da yadda yake shafar decision-making a kasuwa.

⏰ 8:30 PM

🔥 Ka kasance online — za mu shiga cikin details!

Kuji Share ga Sunan kuna sawa zai fito 👇

Dan Kalla Crypto

21/09/2026

Ai Yanzu duk Taro sai an tabo siyasa ko ance na Yan Crypto ne

‎Jiya da safe, ina tafiya a wani Keke Napep, sai wata ƙaramar yarinya ta tsayar damu, ta kalli driver tace:‎‎“Mai Keke, ...
21/09/2026

‎Jiya da safe, ina tafiya a wani Keke Napep, sai wata ƙaramar yarinya ta tsayar damu, ta kalli driver tace:
‎
‎“Mai Keke, ina kwana?”
‎
‎Yace: “Lafiya ƙalau, yakike?”
‎
‎Tace: “Alhamdulillah.”
‎
‎Yace: “Ina za ki je?”
‎
‎Tace: “School gate. Za ka kai ni? Nawa ne kudin?”
‎
‎Yace mata: “₦300.”
‎
‎Sai tayi shiru kamar ba za ta ce komai ba. Sai na ga ta sunkuyar da kanta ƙasa, idanunta sun yi ja kamar za ta yi kuka. Sai tace:
‎
‎“Mai Keke Napep, ina da naira ɗari. Za ka ɗauke ni?”
‎
‎Saiyace: “A’a, ba zan ɗauke ki ba gaskiya, sai kin bani ₦300.”
‎
‎Sai tace: “To shikenan, ka tafi kawai. Idan ma ka ɗauke ni, ban san waye zai dawo da ni ba. Dama wannan naira ɗarin ita kaɗai ce mamarmu ta bani.”
‎
‎Kuma saida na ce mata: “Ba za a ɗaukeni ba.”
‎‎Tace: “In yi haƙuri in tafi, ba ta da kuɗi.”
‎“wai nayi tawakkali ga Allah. Mutanen kirki ba su ƙarewa. Akwai masoya Manzon Allah. Idan wani bai ɗauke ni ba, wani zai ɗauke ni.”
‎
‎Sai driver yace: “To shikenan, ki riƙe ɗarinki, na bar miki hawo mu tafi.”
‎
‎Sai da muka tafi, saina kalleta nace mata:
‎
‎“Babanki yana nan ko ya rasu?”
‎
‎Sai tace: “Babanta sojane. Idan ya tafi, yana ɗaukar lokaci mai tsawo bai dawo ba.”
‎
‎Saina ƙara tambayarta:
‎
‎“Waye yake baki kuɗin hawa mashin kullum idan za ki zo school?”
‎
‎Tace: “Babantane yake tura musu kuɗi duk ƙarshen wata. Idan s**a sayi kayan abinci, sai a rage kuɗin da ake bata domin zuwa school.”
‎
‎Again saina kara tambayarta:
‎
‎“To yanzu kuɗin sun ƙare ne, ko ya aka yi?”
‎
‎Sai tace:
‎
‎“Ai mamartace tayi rashin lafiya, aka kaita asibiti. Aka yi mata ƙarin ruwa, da ƙarin jini. Aka kira babansu aka sanar da shi, yace wallahi ba shi da kuɗi saboda yanzu wata yayi nisa.”
‎
‎“Sai dai s**a sayar da kayan abincin da s**a siya, s**a haɗa da kuɗin Keke Napep da ake bata domin zuwa school, s**a biya kuɗin maganiYanzu ma Koko Tasha tataho school.”
‎
‎Ni dai inata yimata tambaya cikin tausayi kamar nayi hawaye🥲 sai nace:
‎
‎“Kinayin Islamiyya?”
‎
‎Tace: “Eh. A Kano tana zuwa Islamiyya, amma tun da s**a dawo Abuja ba a sanya ta ba. Sai dai kullum mamarta tana koya mata karatun Al-Qur’ani cikin gida.”
‎
‎
‎Duk tambayar da nayi mata, sai in ji ta bada amsa daidai da tambayar. Ni kaina sai da nayi mamaki ganin ƙaramar yarinya kamar wannan, amma tana da ilmi sosai da hankali.
‎
‎Har muka zo bakin gate ɗin makarantar, Inada 1500 a aljihuna Zambia 500 kufin keke napep sai na dauko 1000 zan bata,
‎
‎Bayan tasauka za ta tafi, sai driver yace naji duk abunda kuke magana akai saboda haka kabar dubu ɗayanka 1k dinka,
mutumin ya kirata ta dawo.
‎
‎Ya zaro ₦7,000 ya bata yace:
‎
‎“Ki ɓoye su da kyau kada su ɓace. Idan kin koma gida, ki ba mamanki, kice ta siya muku abinci na ₦5,000, A'ajiye miki ₦2,000, A riƙa baki kuɗin Keke Napep daga nan kafin a yi wa babanku albashi. Idan kin je, kicewa mamamki masoyin Manzon Allah ne ya baku.”
‎
‎Sannan ya zaro ₦500 ya bata yace:
‎
‎“Ki riƙe wannan, ki haɗa da ɗarin da ke gurinki. Ki yi breakfast da ₦300, ki ajiye ₦300 ki biya Keke Napep idan an tashi ki koma gida,

sai bayan yarinyar Tatafi nakalli mutumin nace Amma bawan Allah kaima sojane kodai wani ma'aikacin gomnati?

yakalleni yayi dariya yace a'ah babu ko daya wllh shi kayan Miya yake siyarwa yanzu haka ma kasuwa yanufa,

duk abunda yayimata yayimatane saboda Allah da arzikin Manzon Allah kamar yarda mahaifiyarta tanunamata,

saikuma ganin yarinyar tanada kokari sosai Gameda addinin musulunchi shiyasa yabata kudin.

Allah ubangiji kakaramana soyayyar Annabi Mohammed s.a.w
‎
‎ True life story:::

Copied

🚨 SHEIKH BALA LAU YA ƘARA KAURACEWA TALLAR TINUBU!A karo na biyu, Sheikh Bala Lau ya bayyana matsayinsa kan halin da al’...
21/09/2026

🚨 SHEIKH BALA LAU YA ƘARA KAURACEWA TALLAR TINUBU!

A karo na biyu, Sheikh Bala Lau ya bayyana matsayinsa kan halin da al’umma ke ciki.

Al’umma na fama da matsalar tsaro, yunwa, matsin lambar rayuwa, rashin aikin yi, da mummunan talauci.

Saboda haka, abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne a samar wa al’umma mafita da za ta rage musu wannan ƙunci.

Address

Kano
London

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dan Kalla Crypto posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dan Kalla Crypto:

Shortcuts

Share