21/05/2026
Yan uwana matasan Arewa, mu fa da gaske muna da ƙarfi sosai a harkar Social Media. Don Allah mu riƙa amfani da ita wajen yaɗa alkhairi domin mu amfanar da kanmu da sauran mutane a duniya da lahira. Mu daina yaɗa sharri, batsa da abubuwan da ba su da amfani face tara mana zunubi.
Abin takaici, da yawa daga cikinmu ba ma ɗaukar Social Media da muhimmanci, alhali kuwa babbar hanya ce ta samun alkhairi da ci gaba.
Social Media tana ba ka damar isar da saƙonka zuwa ko’ina cikin sauƙi ba tare da ka fita kana neman wanda zai kai maka saƙo ba.
Za ka iya samun kuɗi ka taimaki kanka da iyalanka cikin halal.
Wasu ma suna samun kuɗi ba tare da sun saya ko sun sayar da kaya ba 😅
Za ka haɗu da abokai nagari masu anfani a rayuwa.
Hanya ce mai ƙarfi wajen taimakon addini da yaɗa ilimi.
Turawa sun mayar da Social Media gonarsu ta samun kuɗi da ci gaba ba tare da wahala mai yawa ba.
Toh mu ma me zai hana mu yi amfani da ita wajen yaɗa manufofinmu masu kyau? Mu nuna cewa mun haɗa ilimin Boko da na Addini wajen anfani da fasaha ta hanya mai kyau.
Ka tuna: duk abin da ka wallafa, ko alkhairi ne ko sharri, yana iya zama hujja a gare ka ranar gobe.
Don haka mu zaɓi abin da zai amfani rayuwarmu da lahirarmu. 🤝