22/08/2026
Nasiru Sule Garo Ya Ce Matsalar Tsaro da “Gazawar APC” ne s**a Tunzura Shi Shiga Takarar Sanata a Kano ta Arewa
Tsohon Wakilin Gwarzo da Kabo a Majalisar Wakilan Najeriya, kuma ɗan takarar kujerar Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa a ƙarƙashin jam’iyyar Nigerian Democratic Congress (NDC), Hon. Nasiru Sule Garo, ya ce halin da Najeriya ke ciki ne ya tunzura shi ga amince da tsayawa takarar kujerar.
Garo ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gidansa jim kaɗan bayan ƙaddamar da takararsa a wani taro da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bichi.
Ya ce matsalar tsaro da kuma abin da ya bayyana a matsayin gazawar shugabanci wajen magance matsalolin da ke addabar al’umma, musamman a Arewacin Najeriya, na daga cikin manyan dalilan da s**a sa ya yanke shawarar komawa fagen neman kujerar ta Sanata.
A cewarsa, idan ba a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tunkarar matsalar rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke fuskantar al’umma ba, akwai haɗarin da jama’a za su ci gaba da shiga cikin mawuyacin hali, tare da rasa damar rayuwa cikin walwala da mutunci.
Ya kuma soki abin da ya bayyana a matsayin yadda wasu shugabannin siyasa daga Arewa ke tafiyar da harkokin yankin, yana mai cewa bai k**ata wakilan al’umma su kasance suna yin shiru yayin da matsalolin da s**a shafi rayuwar jama’a ke ƙara ta’azzara ba.
Garo ya kuma ambaci Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da sauran shugabanni, yana me zargin cewa wasu daga cikin matakan da ake ɗauka a matakin siyasa da na gwamnati ba sa tafiya da muradun al’ummar Arewa. Ya ce wannan lamari ne da bai k**ata a yi masa kallon cewa ba shi da muhimmanci ba.
Ya bayyana cewa lokaci ya yi da al’ummar Kano da Arewa baki ɗaya za su sake duba salon siyasar da suke bi, tare da neman sabbin shugabanni da za su fifita muradun jama’a, adalci da ci gaba.
Garo ya ce babban burinsa shi ne ganin an samu sauyi mai ma’ana a siyasar Kano, Arewacin Najeriya da ƙasar baki ɗaya, yana mai kira ga jama’a da su yi amfani da damar zaɓe wajen zaɓar shugabannin da za su yi musu hidima bisa gaskiya da adalci.
A ƙarshe, ya yi kira da a jingina wannan yunƙuri ga tsoron Allah da kishin al’umma, tare da tabbatar da cewa jagoranci ya kasance bisa gaskiya, adalci da kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa.