Romo Liberty Voice TV

Romo Liberty  Voice TV The voice of people

📰 RIGIMA TA ƘUNNO KAI TSAKANIN  .     DA F.C. RØMØ UNITEDInna lillahi wa inna ilaihi raji’un.Rigima ta ɓarke tsakanin  ....
02/04/2026

📰 RIGIMA TA ƘUNNO KAI TSAKANIN . DA F.C. RØMØ UNITED

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.

Rigima ta ɓarke tsakanin . da ƙungiyar F.C. RØMØ United bayan da ƙungiyar ta nemi taimakonsa sakamakon wata bukata da ta taso a gare su.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan ƙungiyar sun roƙi a rage musu wasu kuɗaɗe domin samun sauƙi, musamman duba da cewa suna da magoya baya da za su je domin ƙarfafa musu gwiwa wajen neman nasara.

Sai dai Hon. ya shawarce su da su tsaya da ƙafafunsu, lamarin da ya jawo rashin jituwa tare da ɓullar da cece-kuce a tsakanin ɓangarorin biyu. Wannan mataki ya haddasa fusata a cikin matasan ƙungiyar, inda wasu s**a fara zanga-zanga, yayin da wasu kuma s**a fara wallafa hotuna da saƙonni a shafukan sada zumunta domin nuna rashin jin daɗinsu.

A wani ɓangare kuma, wasu magoya bayan Hon. #*Magaji Sule sun yi zargin cewa ya taba sayawa matasa kayan wasa, ciki har da ƙwallo kan kuɗi kimanin ₦35,000 da kuma rigunan wasa da ake kiyasin darajarsu ta kai ₦94,500. Sai dai ƙungiyar F.C. RØMØ United ta fito fili ta karyata wannan zargi, tana mai cewa ba su da wata masaniya a kan hakan.

Ƙungiyar ta bayyana cewa duk wani tallafi ko gudummawa da aka bayar gare su ana bayyana shi a fili, tare da sunan wanda ya bayar, ko a jikin kayan wasa ko kuma a sanarwa. Saboda haka, sun jaddada cewa babu wani ɗan wasa ko ƙungiya da aka bai wa ƙwallo ko wani tallafi na kuɗin da aka ambata.

Duk da haka, ‘yan ƙungiyar ba su hakura ba. Sun ƙara kira ga . da ya ƙara kula da amanar da aka ɗora masa, musamman dangane da aikin gadar da aka fara amma yake tafiya a hankali.

Sun nuna damuwa cewa aikin ya tsaya cak har tsawon makonni biyu, lamarin da ka iya janyo tsaiko, musamman da yake damina na gabatowa. A cewarsu, matasa ne s**a nemo wannan aiki domin ci gaban al’umma, amma rashin kulawa na iya lalata komai.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa idan har ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, za su cire tsoro su kai ƙorafinsu har zuwa sakatariya, tare da fara fallasa lamarin a bainar jama’a kan zargin cin amanar jama’a.

A ƙarshe, sun jaddada cewa:

“Sauyi dole ne, In sha Allah.”

13/03/2026
23/01/2026

🕌 Saukar Haddar Al-Qur’ani Mai Girma – Romo
📍 Central Primary School, Romo
📅 24/01/2026 | ⏰ 9:00am
📖 Hafizai & ’Yan Sauka
✨ Kar a bari a ba ka labari

08/01/2026

T🤣🤣🤣

Pls da gaske dan Allah Banda kry
21/10/2025

Pls da gaske dan Allah Banda kry

28/08/2025

*ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH WABARAKATUHU

WATO WANNAN AIKI DA KUKE GANI AIKI NE WANDA NE YA BAYAR A KARAMAR HUKUMAR BAGWAI DAKE GARIN WANDA MU MUNA GANIN CEWA AKWAI GYARA CIKIN AIKIN SABODA DUK WANDA YASAN T**I YASAN WANNE KALAR KWALBATI AKE YI
ANA YIN KWALBATI WANDA ZAI KWARI DOMIN KADARUWA YA SHIGO TO WANNAN YA KUKA GA YACCE YAKE YAMUKU K**A DA WANDA RUWA ZAI KYALE . DAN HAKA DAN ALLAH MUNA KIRA DA DAN KWAN GILA NA WANNAN AIKI YAYI KOKARIN KAWO GYARA CIKIN AIKIN NAN IN KUMA LAIFIN INJINIYA NE A CANZA SHI MANA KO A ACE YA GYARA AIKIN SA TINDA YASAN DAIDAI TINDA BIYAN SA ZA,AI TIN DA ANYI TOTAL DIN KUDIN NAN HAR WANDA ZAKA SAMU TO KAI MA KA DAURE KAYI MAIKYAU MANA DOMIN KASAMU WATA KWAN GILAR GABA YANZU IN AN BARKA KAI A HAKA KA CUCI GWAMNATI KUMA KA CUCI AL,UMAR YANKIN KUMA KA DAWO DA GWAMNATI BAYA KUMA KACI HARAMUN.
DAN HAKA DAN ALLAH MU GYARA
HA, INCI BA ABUNYI BANE DOMIN SHI ALLAH BA RUWAN SA DA GWAMNATI
KA CUTA DOLE SAI AN TAMBAYE KA WAYASA KACI
DAN HAKA MUNA SANAR DA DUK WANDA YASAN YANA DA RUWA DA TSAKI NA WANNAN AIKI YAYI BIN CIKE DAN GANIN YA FITA DAGA CIKIN WANNAN MATSALAR ANYIWA MUTANAN YAN KINNAN AIKI MAI KTAU. ✍🏼
————————
BY __________________

ROMO LIBERTY 🗽 VOICE TV 📺

Address

Kano
0234

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Romo Liberty Voice TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share