Bmg

Bmg Professional Satellite Setup
Accurate Signal Tracking
Hausa & International Channels
Fast & Reliable Service
📞 07077127354
Muna kawo maka duniya cikin gidanka.

08/03/2026

Kana fama da matsalar NO SIGNAL a gidan ka?
Ko kuma kana buƙatar sabuwar dish amma baka san wanda zai maka aikin cikin inganci da sauƙi ba?

BMG Satellite Installation muna nan don taimaka maka!

Muna da ƙwararrun ma'aikata da gogaggun technicians waɗanda zasu taimaka maka da:

Saka sabuwar satellite dish
Dawo da tashoshin da s**a gudu
Sake daidaita dish da ta goce
Sauya LNB cikin kwarewa

Kira mu ko turo saƙo ta WhatsApp yau domin magance matsalar ka cikin sauri da sauƙi!

Muna aiki cikin sauri, tsafta, kuma muna bada garanti a duk ayyukan mu.

Ramadan na tafe… kuma shirin da kuke jira ma ya dawo!Kamar yadda Africa TV3 ta saba, za ta kawo muku shirin drama mai ci...
13/02/2026

Ramadan na tafe… kuma shirin da kuke jira ma ya dawo!

Kamar yadda Africa TV3 ta saba, za ta kawo muku shirin drama mai cike da darussa da ilmantarwa a wannan watan mai alfarma IYALINA SEASON 3.

Shin tashar ka na k**a Africa TV3 yadda ya k**ata?

Kada ka bari iyalan ka su rasa shiri mai amfani saboda matsalar signal ko rashin saitin dish daidai.

Mu a BMG Satellite Installation muna:
Saita sabuwar dish
Gyaran signal mai rauni
Saitin decoder cikin kwarewa
Warware matsalar “No Signal” ba tare da ɓata lokaci ba.

Ramadan lokaci ne na taruwa da iyali. Ka tabbatar gidanka a shirye yake kafin watan ya fara.

Ka kira mu yanzu domin booking kafin lokaci ya kure.
Ko ka aiko mana da sako kai tsaye yanzu 07077127354.

BMG Satellite Installation Muna haɗa ka da tashoshin da kake so, ba tare da tangarda ba.




when your dream is big, and your budget is small. 😁😁
19/01/2026

when your dream is big, and your budget is small. 😁😁

A kwanakin nan mun shaida wani babban sauyi a tashar Saira Movies TV, inda tashar ta tattara kayan ta daga Free To Air (...
17/01/2026

A kwanakin nan mun shaida wani babban sauyi a tashar Saira Movies TV, inda tashar ta tattara kayan ta daga Free To Air (FTA) zuwa Premium, lamarin da ya sa mutane da dama s**a rasa damar kallon tashar kyauta k**ar yadda s**a saba. Wannan sauyi ya jawo cece kuce a tsakanin masu kallo, musamman waɗanda s**a dogara da tashar wajen kallon fina-finan Hausa a kullum.

Bayan koke-koke da ra’ayoyi da dama da masu kallo s**a bayyana, kamfanin Saira Movies TV sun saurari muryar jama’a. Saboda haka s**a yanke shawarar dawo da tashar zuwa Free To Air, amma a wannan karon a sabuwar frequency, domin kowa ya samu damar ci gaba da kallon tashar ba tare da biyan kuɗi ba.

Idan ka lura tashar ta bace ko baka iya saita sabon frequency ɗin ba, kada ka damu. BMG Satellite Installation muna da gogewa a fannin dish installation da satellite setting. Muna saka sabuwar dish, muna gyara tsohuwa, sannan muna saita tashoshi cikin inganci. Kira mu yanzu a 07077127354, mu dawo da maka Saira Movies TV da sauran tashoshi lafiya 👌📡

Yadda Zaka Gyara “No Signal” da Kanka Kafin Ka Kira Mai Gyara.Yawan ganin “No Signal” a TV yana daɗa damun mutane da dam...
09/10/2025

Yadda Zaka Gyara “No Signal” da Kanka Kafin Ka Kira Mai Gyara.

Yawan ganin “No Signal” a TV yana daɗa damun mutane da dama, amma ka sani, akwai abubuwa da zaka iya dubawa da kanka kafin ka kira mai gyara. Ga matakai masu sauƙi da zaka bi:

1. Duba ko TV da decoder dinka suna kunne Wani lokaci matsalar zata iya zama mai sauƙí!

2. Tabbatar da haɗin cables.
Idan wayar LNB ko daga dish ta cire ko ta tsinke, signal ba zai shiga ba.

3. Duba ko dish ɗin ya motsa.
Idan iska ko wani abu ya jawo dish ɗinka ya motsa, to dole signal zai gudu. Ka tsaya a gefe ka duba ko dish yana kallon wajen da ya saba.

4. Sake duba signal bar.
Je zuwa settings na decoder dinka ka shiga Signal Information domin ganin ko signal na zuwa ko a'a.

5. Sake scanning Idan ka rasa wasu tashoshi kawai, ka iya yin auto scan don dawo da su.

Idan ka bi waɗannan matakai, sau da dama matsalar zata warware. Amma idan ba ta gyaru ba, to ka kira kwararre domin a tabbatar da matsalar da take damun dish ɗin ka.

Ni kuma a shirye nake domin taimaka maka a kowane lokaci!

Muna da ƙwarewa sosai a fannin sawa da gyaran satellite dish. Idan kuna buƙatar saka sabuwar dish a gidan ku, ko kuma ku...
08/10/2025

Muna da ƙwarewa sosai a fannin sawa da gyaran satellite dish. Idan kuna buƙatar saka sabuwar dish a gidan ku, ko kuma kuna fuskantar matsala da wadda kuke da ita, ko kuma kuna so ku ƙara tashoshi masu ban sha'awa domin jin iyalinku, mu ne wanda kuke buƙata. Mun san yadda ake saita kowane irin dish don samun kyakykyawan signal.

Idan dish ɗinka ba a daure shi da kyau ba, iska na iya motsa shi ko da kaɗan. Wannan motsin da baka gani da ido shi ya k...
07/10/2025

Idan dish ɗinka ba a daure shi da kyau ba, iska na iya motsa shi ko da kaɗan. Wannan motsin da baka gani da ido shi ya ke sa decoder ɗin ka ta rasa frequency ɗin wasu tashoshi. Kafin matsalar ta yi yawa, ka duba ko dish ɗinka yana ɗauru da kyau, kuma a ƙarfafa mazaunin LNB ɗin domin samun signal mai ƙarfi da tashoshi masu yawa.

Muna amfani da kayan aikin zamani da ƙwarewa don tabbatar da cewa kowane dish da na saka yana aiki da kyau. Ba saka sate...
06/10/2025

Muna amfani da kayan aikin zamani da ƙwarewa don tabbatar da cewa kowane dish da na saka yana aiki da kyau. Ba saka satellite dish bane kawai, ina tabbatar signal ɗinka yana da stability, babu zancen kame kame. Ka kira ni ko ka tura saƙo, zan zo in duba maka dish ɗinka.

Kana tunanin sai ka saka dish biyu don kayi kallo a ɗakuna biyu? A'a, hakan ba lallai ba ne!Wasu suna zaton dole sai sun...
05/10/2025

Kana tunanin sai ka saka dish biyu don kayi kallo a ɗakuna biyu?

A'a, hakan ba lallai ba ne!

Wasu suna zaton dole sai sun sayi dish guda biyu idan suna son yin kallo a ɗakuna biyu ko uku. Amma gaskiyar magana ita ce, dish guda ɗaya na iya baiwa dekoda biyu ko uku signal idan an haɗa shi da kyau.

Wato dai, dish ɗaya + decoder biyu = kallo a ɗakuna biyu ba tare da wahala ba 😁😁.
Ka jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan!

Idan kana da sha'awar irin wannan haɗin, ina nan a shirye na taimaka maka da installation mai inganci da kwanciyar hankali.

Tuntuɓe mu a yau domin shawarwari ko aiki.

Idan hotonka yana yin freezing, yana rawa ko kuma ka ga yana scratch, ba lallai bane laifin TV ɗin ka ne. Yawancin lokut...
03/10/2025

Idan hotonka yana yin freezing, yana rawa ko kuma ka ga yana scratch, ba lallai bane laifin TV ɗin ka ne. Yawancin lokuta, matsalar tana faruwa ne daga dish ɗin ka ko LNB da ke sama. Don samun tashoshi masu kyau da hotuna HD, ana buƙatar saiti na musamman daidai da daidai da kuma waya mai inganci. Rashin daidaita signal ko amfani da kayan aiki marasa inganci na iya hana ka jin daɗin kallon ƙwallo ko fina-finai. Kira ni Sadiq Jaafar Bello , domin in daidaita maka komai yadda ya k**ata, ta yadda za ka sami damar kallon tashoshi da hotuna ingantattu, ba tare da wata matsala ba.

Address

Dala
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bmg posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share