Zamzam Online TV

Zamzam Online TV Zam-Zam Online TV is an educational platform that provides useful and engaging content in Arabic, Hausa, and English.

A ranar Asabar da ta gabata 11/5/2026 wanda yayi dai-dai da 21/11/1447H Makarantar Zam-Zam Islamic College dake darmawa ...
11/05/2026

A ranar Asabar da ta gabata 11/5/2026 wanda yayi dai-dai da 21/11/1447H Makarantar Zam-Zam Islamic College dake darmawa ta samu barkwancin babban Limamin Juma'a na Masallacin Sabuwar Jami'ar Bayero dake birnin Kano, Associate Professor Nuhu Abdullahi Usman Giwa.

Malam ya kawowa Makarantar ta Zam-Zam ziyara ne domin gabatar da laccar da hukumar Makarantar ta ɗauki nawin gabatarwa a duk ƙarshen wata.

Mau'du'in da Malamin ya tattauna shine; Dogaro da Allah; Maganin Wayyo Allah.

Cikakkiyar laccar tana nan tafe in sha Allah a wannan shafi.

Za aoua bibiyarmu a👇👇

:Facebook: https://www.facebook.com/share/18P1CS8GG6/Youtube: https://youtube.com/?si=U6qgvybuQTshAq3o online TV 'an

Assalamu alaikum warahmatulLahi WabarakatuH,Hukumar Makarantar Zam-Zam Islamic College tana sanar da al'umma cewa an sak...
28/04/2026

Assalamu alaikum warahmatulLahi WabarakatuH,

Hukumar Makarantar Zam-Zam Islamic College tana sanar da al'umma cewa an sake buɗe rejista (registration) na ɓangaren Koyon Yaren Larabci.

Ana gudanar da wannan karatun ne a Makarantar Zam-Zam a ranakun Asabar da Lahadi da kuma Alhamis da Juma'a.

Za'a fara karatun wannan zangon a ranar 7/5/2026 ga maza. 9/5/2026 ga mata.

Domin neman ƙarin bayani, za'a iya zuwa Makaranta Zam-Zam dake Darmanawa, Kano. Ko kuma a kira lambobin da suke ƙasa.

Sanarwa,
Hukumar Makaranta.
Mun gode.

A yau Asabar 11/Afrilu/2026 wanda ya yi dai da 23/Shawwal/1447 Sheikh Bashir Yahya Umar Al-Ifriƙiy ya ziyarce Kealejin M...
11/04/2026

A yau Asabar 11/Afrilu/2026 wanda ya yi dai da 23/Shawwal/1447 Sheikh Bashir Yahya Umar Al-Ifriƙiy ya ziyarce Kealejin Musulunci ta Zam-Zam, dake Darmanawa, Kano domin gabatar da laccar ƙarshen wata.

Malamin ya yi bayani ne akan mau'du'i mai taken: "HATSARIN GAGGAUTA ƘURUCIYA TARE DA RAINON ƳAƳA BA TARE DA HAƘURI BA".

Malamin ta taɓa ɓangarori da yawa. Ku cigaba da bibiyarmu, zamu kawo muku cikakkiyar laccar a nan gaba.

21/03/2026
21/03/2026

Hukuncin Sallar Juma'a idan ta haɗu da Sallar Musulmi.

Tare da Sheikh Huzaifa Aminu Ibrahim Daurawa

21/03/2026

Yadda Sallar Idi ƙarama ta gudana a Filin Makaratar Zam-Zam Islamic College, Darmanawa, Kano.

Wanda ya jagoranci Sallar shi ne Dr. Umar Yusuf Faki.

Allah Ya ƙarba, Ya kuma mai-maita.

18/03/2026

A ranar Lahadi 26/Ramadan/1447, wanda ya yi dai-dai da 15/3/2025 Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa; Babban Kwamandan Hisbah ta Jihar Kano ya kai ziyara gidan yara da yake Mariri domin ƙaddamar da raba musu kayan Sallah.

Kayan Sallar su haɗa da dinki mai kyau, da hulu, da takalma. Sannan malamin ya gwangwaje su da kuɗin barka da Sallah ₦500 ga kowannen su.

A jawabin Malamin, ya bayyana ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Kano, Karƙashin Eng. Alh. Abba Kabir Yusuf da ta tattaro waɗannan yara daga kan tituna na Jihar, ta killace su a wannan guri domin cigaba da kula da tarbiyyar su, da ilimin su, da abincin su, da suturar su, da gurin kwanan su, da walwalar su a sama da shekara ɗaya da s**a yi a gurin.

Malaminya rufe jawaban sa da bayyana nawin da yake kan iyaye akan ƴaƴan su, tare da tabbatarwa da yaran cewa kowannen su ya kusa ya koma ƙarƙashin kulawar iyayen shi.

# Zam-Zam Online TV
# Zam-Zam Islamic College

04/03/2026

RABON TALLAFIN KAYAN KAYAN ABINCI NA WATARAN RAMADA KASHI NA UKU.

A ranar Litinin 9/9/1447 wanda ya yi dai-dai da 24/2/2026 Gidauniyar Zam-Zam Educational initiatives ta cigaba da rabon tallafin abinci karo na Uku, a inda ake saka rana sama da mutum Dubu Biyu (2,000) za su amfana da wannan tallafi a wannan shekarar.

A madadin Jagoran Gidauniyar, Daraktan Makarantar Zam-Zam Islamic College; Sheikh Usama Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa rabon na wannan lokaci zai gudana ne ga masallatai, da makarantu, gidauniyoyi domin au dinga dafawa suna rabawa masu Azumi. Hakazalika, Ƙungiyar mata masu matsalar Ido suma za su amfana da wannan tallafi.

Abubuwan da aka raba sun haɗa da; Shinkafa bubu 5, Masara buhu 2, Gero buhu 2, Semovita guda 10, sai kuma Makaroni, da Taliya, da kayan Shayi.

Rahoto,
Zam-Zam Online TV

Address

Zam-Zam Street
Kano
700292

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zamzam Online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category