17/02/2026
Sama da masu karamin karfi dari biyu ne s**a karbi tallafin kayan abinci daga wakilan al`umomin Sinawa mazauna Kano dake arewacin Najeriya albarkacin shigowar watan Azumin Ramadana wanda ya fara daga yau laraba 18 ga wata.
Kayan abincin sun kunshi Shinkafa da kuma Talilya, kuma an rabar da kayan ne a harabar gidan abincin Sinawa na Red China Restuarant a unguwar Nasarawa GRA dake birnin Kano.
A lokacin da yake rabar da kayan, mamallakin gidan abincin Mr Lok yace a duk lokacin irin wannan na shigowar watan Azumi akan bayar da wannan tallafi ga mabukata karkashin kulawar sa domin dai saukaka rayuwar mutanen da suke da karancin samu.
Yace hakika akwai magidanta da suke cikin matsanancin hali na rashin wadatar abinci tare da iyalan su, wannan ya basu kwarin gwiwar kirkiro da shirin tallafin abincin wanda ake gudanarwa tun sama da shekaru 5 da s**a gabata.
Mr Lok ya cigaba da bayanin cewa watan azumin na bana yazo dai dai da lokacin da al`ummar Sinawa a Kano dana sauran sassan duniya ke bukukuwan bikin sabuwar shekarar gargajiya, inda yace yana daga cikin al`adar bikin taimako da tausayin juna, a don haka wannan tallafin kayan abinci da aka bayar wani bangare na bukukuwan sabuwar shekarar tare da maraba da wata mai alfarma a Ramadan.