
16/07/2025
DA DUMI-DUMI: Wata kungiyar ta'addanci mai suna Fethullah (FETO) ta bulla a Najeriya - Kasar Turkiyya ta gargaɗi Gwamnatin Tinubu
Gwamnatin Turkiyya ta yi gargadi sosai cewa akwai mambobin ƙungiyar ta’addanci da ake kira Fethullah Terrorist Organization (FETO) a Najeriya, wanda k*ma ke gudanar da ayyukanta a wasu ƙasashe.
Jakadan Turkiyya a Najeriya, Mehmet Poroy, ya bayyana wannan ne a Abuja a ranar Talata, yayin liyafar tunawa da “Ranar Dimokuradiyya da hadin kan kasa”, domin tuna juyin mulkin 2016 da aka yi ƙoƙarin yi a Turkiyya wanda ya jawo asarar dumbin rayuka a kasar.
Poroy ya gargaɗi Gwamnatin Najeriya cewa "ta yi hattara da duk wani tallafi a fannin ilimi da lafiya daga kasashen waje, domin tanan ne kungiyar FETO ke shigo da wannan muguwar akida"
Madogara Jaridar A Yau