Kunya Media

Kunya Media Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kunya Media, Media/News Company, Kano.

🗞️ KUNYA MEDIA
đź“° Gidan Jaridar ku na zamani
🌍 Labarai | Siyasa | Al’umma | Nishaɗi
🎙️Tattaunawa da Sanannun Mutane
🎥 Bidiyo da Labarai Masu Zaman Kansu
âś… GASKIYA KAI TSAYE
📩 Tuntube mu ta DM Ko ‪+2349021779895‬

DA ƊUMI ƊUMI: An bayyana Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin wanda ya lashe sabon zaɓen fidda gwani na takarar gw...
29/09/2026

DA ƊUMI ƊUMI: An bayyana Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin wanda ya lashe sabon zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

29/09/2026

“Ina fatan Rarara zai ba kowa haƙƙinsa na ƙungiyar Triple R, wanda aka ce ana tarawa idan ƙarshen shekara ya yi,” in ji Mansurah Isah

🚨 SANARWAR NEMAN MUTUM 🚨Matar ta tafi Geza, kuma za ta dawo Kunya Tarikice, amma ta tsaya a wani wuri.Don Allah, duk wan...
29/09/2026

🚨 SANARWAR NEMAN MUTUM 🚨

Matar ta tafi Geza, kuma za ta dawo Kunya Tarikice, amma ta tsaya a wani wuri.

Don Allah, duk wanda ya ganta, a kira wannan lambar: 07036924125.

Ko kuma a kai ta Gidan Alhaji Miko Mai Atamfa.

🙏 Don Allah a taimaka a yaɗa wannan sanarwar.

Wasu rahotanni da ke fitowa daga Jihar Gombe na bayyana cewa Isah Ali Pantami ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar Gwam...
29/09/2026

Wasu rahotanni da ke fitowa daga Jihar Gombe na bayyana cewa Isah Ali Pantami ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar Gwamnan Jihar a jam'iyyar PDP.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, yana ...
29/09/2026

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, yana mai cewa siyasa na tasiri wajen bincike da gurfanar da wasu mutane.

Sarkin ya kuma yi magana kan shari’a da kuma ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Sanusi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV a Lagos.
Ya ce samar da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa kaɗai bai isa ba, matukar hukumomin da ke da alhakin bincike, gurfanarwa da yanke hukunci ba sa aiwatar da su yadda ya k**ata.

Ya ce an samu lokutan da aka yi watsi da wasu tuhume-tuhume na cin hanci saboda waɗanda ake zargi suna da alaƙar siyasa ko kuma goyon bayan manyan ’yan siyasa.

Sarkin ya ce irin wannan yanayi na iya sa mutane su fara tambayar ko da gaske ana yaƙi da cin hanci da rashawa ne, ko kuma ana amfani da shari’o’in wajen farautar abokan hamayyar siyasa.

Sanusi ya kawo batun tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume da s**a shafi cin hanci da rashawa da kuma halatta kuÉ—aÉ—en da ba a san asalinsu ba.

Ya ce El-Rufai ya shafe watanni bakwai a tsare ba tare da an same shi da laifi ba, yana mai cewa an ƙi bayar da shi beli.
Sanusi ya ce irin wannan lamari na iya sa jama’a su tambayi ainihin manufar da ke bayan wasu shari’o’in cin hanci da rashawa.

Ya ƙara da cewa ya k**ata ’yan siyasa da hukumomin shari’a su tabbatar da cewa ana amfani da dokoki ne bisa manufar da aka kafa su domin cimmawa.

Sanusi ya ce duba da sake fasalin dokokin yaƙi da cin hanci abu ne mai kyau, amma ya k**ata a kuma mai da hankali kan hukumomin da ke da alhakin aiwatar da waɗannan dokoki.

Ya ce idan ba a gyara yadda hukumomin da ke aiwatar da dokokin suke aiki ba, mutanen da ke da kyakkyawar alaƙar siyasa na iya ci gaba da tsallake wasu matakai na shari’a.

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta k**a wasu mutane biyar bisa zargin sanya T-shirts ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go” ...
29/09/2026

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta k**a wasu mutane biyar bisa zargin sanya T-shirts ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go” a Maiduguri.

A cewar wata takardar ’yan sanda da Sahara Reporters ta wallafa, ana zargin mutanen da haɗa baki wajen buga T-shirts ɗin da nufin haddasa rikicin zaman lafiya a yankin West End Roundabout da ke Maiduguri.

’Yan sandan sun tuhume su da laifukan haɗa baki, tunzura jama’a, haddasa tashin hankali da kuma tayar da zaune tsaye.

Rahoton ya ce an gurfanar da mutanen gaban kotu, sannan aka tura su gidan yari yayin da shari’ar ke ci gaba.

Amurka ta sanar da shirin janye sojojinta daga sansanoninsu na ƙarshe a Iraƙi zuwa ranar Laraba, matakin da Iran da ƙawa...
29/09/2026

Amurka ta sanar da shirin janye sojojinta daga sansanoninsu na ƙarshe a Iraƙi zuwa ranar Laraba, matakin da Iran da ƙawayenta ke ɗauka a matsayin wata nasara, a ƙasar da sojojin Amurka 4,500 s**a mutu cikin sama da shekaru 20 na yaƙi.

Wani sabon hasashe ya nuna cewa matsanancin zafin da ake dangantawa da yanayin El Niño na iya haddasa ƙarin mutuwar muta...
29/09/2026

Wani sabon hasashe ya nuna cewa matsanancin zafin da ake dangantawa da yanayin El Niño na iya haddasa ƙarin mutuwar mutane kusan dubu 67 a yankin Sahel cikin watanni shida masu zuwa, inda ake sa ran Najeriya ce za ta fi kowace ƙasa a duniya fuskantar adadin mace-macen da ke da alaƙa da zafi.

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, a halin yanzu yana jagorantar taron farko na Kwamitin Zartarwa na Hukumar B...
29/09/2026

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, a halin yanzu yana jagorantar taron farko na Kwamitin Zartarwa na Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA Exco).

29/09/2026

Malam Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi bankwana da al’ummar yankin Pantami District, bayan kammala ƙidayar ƙuri’u a zaɓen cike gurbi.

An ga yadda jama’a s**a taru domin yi masa bankwana—abin da ya sake haifar da cece-kuce da tambayoyi kan makomar siyasar yankin. 👀🔥

Me kuke tunani, wannan bankwana ne kawai ko akwai wani abu da ke tafe? 🤔

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kunya Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share