Yusif Tech

Yusif Tech FOLLOW YUSIF TECH 👑

📚 Learn how to grow your page to monetisation level ✅
🎓 Facebook Teacher & Creator Growth✅

HAR YANZU BIYAN KUƊIN FACEBOOK YANA “PROCESSING” 🤨Idan shafinka yana cikin koshin lafiya, payout ɗinka ma babu wata mats...
30/09/2026

HAR YANZU BIYAN KUƊIN FACEBOOK YANA “PROCESSING” 🤨

Idan shafinka yana cikin koshin lafiya, payout ɗinka ma babu wata matsala, amma har yanzu biyan kuɗinka yana cikin Processing, kada ka firgita.

A cewar wannan bayanin, idan Page ɗinka da Payout ɗinka suna aiki lafiya, ana sa ran Meta za ta biya kuɗin cikin wannan makon.

Idan kuma ba a biya ba har zuwa ƙarshen watan, ana iya tura kuɗin zuwa tsarin biyan kuɗin wata na gaba.

Waɗanne payouts ne ake cewa ba za a biya ba?

1. Idan Page ɗinka har yanzu yana cikin Flagged.
2. Idan an taɓa flagging Page ɗinka a June ko July, sannan daga baya ya koma Green — wannan bayanin ya ce payouts na May, June da July ba za a biya su ba bisa sabon tsarin Meta.
3. Idan akwai matsala a Payout ɗinka kamar Verification, Learn More ko Restriction.
4. Idan Page ɗinka yana da Limited Originality of Content (LOC) saboda matsalar Copyright.

Idan babu ɗaya daga cikin waɗannan matsalolin a Page ɗinka da Payout ɗinka, to ka kasance cikin haƙuri yayin da biyan kuɗin yake Processing.

KA TUNA: Kada ka firgita saboda jinkirin payout. Ka ci gaba da aiki da content ɗinka kuma ka tabbatar Page da Payout suna cikin koshin lafiya.

Ku aje mana tambayoyinku a comment section 👇 zamu tattauna InshaAllah 🤲

Like 👍 Share ↗️ Follow

👑 YUSIF TECH

ALHAMDULILLAH 🤲Facebook sai raba content monetisation yake da subscription shin kaima kasamu naka ❓Allah Ya ba mu lafiya...
29/09/2026

ALHAMDULILLAH 🤲
Facebook sai raba content monetisation yake da subscription shin kaima kasamu naka ❓

Allah Ya ba mu lafiya, kwanciyar hankali da nasara a dukkan al’amuranmu. Amin. 🤲

'a

🔥 KANA DA FOLLOWERS DA YAWA, AMMA ENGAGEMENT ƊINKA YA YI ƘASA?kar ka damu. followers kaɗai ba su isa su gina maka audien...
29/09/2026

🔥 KANA DA FOLLOWERS DA YAWA, AMMA ENGAGEMENT ƊINKA YA YI ƘASA?

kar ka damu. followers kaɗai ba su isa su gina maka audience mai ƙarfi ba.

ga abin da zaka fara yi 👇

mataki na 1: ka fara yin original content.

mataki na 2: ka daina dogaro da follow for follow (F4F).

mataki na 3: ka ƙirƙiri content da zai sa mutane su tsaya su kalla ko su karanta.

mataki na 4: ka riƙa yin magana da audience ɗinka a comments.

mataki na 5: ka kasance consistent, kada ka daina saboda views sun yi ƙasa.

ka tuna: ba yawan followers ne kawai yake da muhimmanci ba; audience mai sha'awar content ɗinka shi ne ginshiki.

me kake ganin ya fi kawo engagement: original content ko F4F? 👇

ku aje mana tambayoyinku a comment section 👇 zamu tattauna InshaAllah 🤲

like 👍 share ↗️ follow

👑 YUSIF TECH

KATARA FOLLOWERS 1,000K, 2,000K, 3,000K…Amma har yanzu babu Likes, Shares ko Comments? 😔Abin da zaka yi 👇👑 YUSIF TECH   ...
28/09/2026

KATARA FOLLOWERS 1,000K, 2,000K, 3,000K…
Amma har yanzu babu Likes, Shares ko Comments? 😔
Abin da zaka yi 👇

👑 YUSIF TECH

CONTENT CREATOR IDAN KA ƊAUKI AIKIN DA MUHIMMANCI, ZAI IYA CANZA RAYUWARKA DA TA IYALANKA.Rayuwar creator tana buƙatar k...
27/09/2026

CONTENT CREATOR IDAN KA ƊAUKI AIKIN DA MUHIMMANCI, ZAI IYA CANZA RAYUWARKA DA TA IYALANKA.

Rayuwar creator tana buƙatar ka zama mutum mai:

• Sauraro — ka saurari masu baka shawara da masu ƙwarewa.
• Karatu (Reading) — ka ci gaba da koyon sababbin abubuwa.
• Lissafi — ka san yadda kake tafiyar da lokacinka da abin da kake samu.
• Haƙuri da juriya — kada ka karaya idan sakamako bai zo da wuri ba.
• Creativity — ka riƙa tunanin sababbin hanyoyin ƙirƙirar abun kallo.
• Editing — ka inganta kwarewarka wajen gyara content ɗinka.

Amma kada ka manta da kanka. ❤️

Ka riƙa ba kanka hutu, ka ci abinci mai gina jiki, ka yi training/ motsa jiki, sannan ka yi bacci da wuri domin jikinka da kwakwalwarka su samu damar hutawa.

Idan ka tashi cikin dare, ka samu damar yin nafila 🤲 ka roƙi Allah Ya sanya albarka a cikin aikinka.

Kuma sama da komai, ka gode wa Allah da Ya baka lafiya, Ya baka damar aiki, Ya baka basira da damar ƙirƙirar abun da mutane za su amfana da shi.

KA TUNA:
Content creation ba gudu ba ne. Tafiya ce mai buƙatar ilimi, haƙuri, lafiya da juriya.

Tambaya: Wanne daga cikin waɗannan abubuwa kake ganin ya fi taimaka wa creator wajen samun nasara? 👇

Ku aje mana ra'ayoyinku a comment section 👇 zamu tattauna InshaAllah 🤲

Like 👍 Share ↗️ Follow

👑 YUSIF TECH

RAYUWAR CREATOR DA HAƘURITabbas, rayuwar creator ba hanya ce ta gaggawa ba. Tana buƙatar haƙuri, dagewa da fahimtar cewa...
27/09/2026

RAYUWAR CREATOR DA HAƘURI

Tabbas, rayuwar creator ba hanya ce ta gaggawa ba. Tana buƙatar haƙuri, dagewa da fahimtar cewa sakamako ba ya zuwa kullum a lokacin da muke so.

A farkon tafiyarka, kana iya yin bidiyo ka ga mutane kaɗan ne s**a kalla. Wani lokaci kuma zaka yi post da dukkan ƙoƙarinka, amma engagement ɗin ya yi ƙasa.

Wannan ba yana nufin ba ka da basira ba ne.

Creator na gaskiya yana koyon haƙuri.

Ka fahimci cewa:

• Ba kowane bidiyo ne zai yi viral ba.
• Ba kowane post ne zai kawo followers da yawa ba.
• Ba kowane wata ne zaka ga babban canji ba.
• Wani lokaci kana shuka ne yau, amma sakamakon zai bayyana bayan lokaci.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka ci gaba da inganta kanka.

Ka koyi editing, ka inganta yadda kake magana, ka binciki abin da audience ɗinka ke so, ka samar da content mai amfani, sannan ka guji kwatanta farkon tafiyarka da shekarun wani creator.

KA TUNA: Achievement ba kawai lokacin da mutane s**a fara ganinka ba ne.

Lokacin da kake koyon sabon skill, gyara kuskuranka, da dagewa duk da rashin sakamako — kana cikin gina nasararka.

Kada ka bari jinkirin sakamako ya sa ka daina.

Haƙuri ba yana nufin ka zauna babu aiki ba; yana nufin ka ci gaba da aiki yayin da kake jiran lokacin sakamako.

Allah yana ganin ƙoƙarinka. Ka yi aikinka da gaskiya, ka nemi ilimi, ka yi haƙuri, sannan ka bar sakamakon ga Allah. 🤲

Daga yanzu zan riƙa wayar muku da kai kan abubuwan da s**a shafi creator: yadda zaku iya samun kuɗi daga content ɗinku, yadda zaku bi dokokin Facebook, da yadda zaku kare account ɗinku da monetisation ɗinku daga matsalolin da ka iya jefa ku cikin haɗari.

Ina so mu gina wannan tafiya tare — mu koyi abubuwa, mu guji kuskure, kuma mu ƙara fahimtar yadda creator zai iya amfani da Facebook cikin tsari mai kyau.

Kada ku manta:

Like 👍 Share ↗️ Comment 💬

Ku danna FOLLOW domin kasancewa tare da 👑 YUSIF TECH.

TAMBAYA: A matsayinka na creator, wanne ne ya fi maka wahala: rashin views, rashin followers, ko rashin motivation? 👇

Ku aje mana ra'ayinku a comment section 👇 zamu tattauna InshaAllah 🤲

👑 YUSIF TECH

Address

Gwammaja Layin Musa Utca A. C
Kano
700221

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yusif Tech posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share