08/05/2026
KE DUNIYA....
Rahotanni daga garin Azare na cewa jami’an Hisbah sun cafke wasu magidanta bisa zargin aikata wani ɗabi’a mai matuƙar muni da ya sa jama’a cikin mamaki.
Ana zargin mutanen da yin musayar matansu a tsakaninsu domin biyan buƙatun zuciya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce da tofin Allah tsine a tsakanin al’umma.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa waɗanda ake zargin tare da matansu sun amsa cewa irin hakan na faruwa a tsakaninsu.
Allah Ya tsare mana tarbiyya da mutuncin al’umma, Ya kuma kawo ƙarshen duk wani abu mara kyau a cikin rayuwarmu. 🤲💔