04/06/2026
Majalisar dattawan Nijeriya ta fara aiwatar da matakan da za su ba da damar kafa ‘yansandan jihohi, inda ta yi alƙawarin samar da duk wani goyon bayan doka da ake buƙata domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar da kuma daƙile ta’azzarar matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.
Shugaban kwamitin majalisar kan yaɗa labarai da harkokin jama’a, Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Punch.
Kuyi Following Din Jaridar Arewa Point News yanzu don cigaba da samun Sahihan Labarai Akan Lokaci