07/10/2025
Kwamishinan Shari’a na Kano Ya Kafa Kwamitin Gaggawa Don Duba Shari’o’in da S**a Dade Ba a Kammala ba
Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Barr. Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, a yammacin yau Talata, 7 ga Oktoba, 2025, ya kafa kwamitin gaggawa domin ganowa da kuma duba dukkan shari’o’in da suke makale ko ba a kai kotu ba a cikin gidajen gyaran hali da kotunan jihar Kano.
A cewar Kwamishinan, wannan mataki na daga cikin kokarin tabbatar da adalci ta hanyar magance shari’o’in da s**a dade ba a kai kotu ba, batutuwan da aka rasa fayil din shari’a, da kuma wadanda s**a samu tsaiko ba bisa ka’ida ba.
Kwamitin yana karkashin jagorancin Barr. Rabi’at Sa’ad, Babbar Lauya a Ma’aikatar Shari’a, yayin da Barr. Khalifa Auwal Hashim, zai kasance a matsayin sakatare. Sauran mambobi sun hada da Barr. Garzali Maigari Bichi, Barr. Maryam Muhammad Jibril, Barr. Umar Yakubu, Barr. Nafi’u Kabiru Muhammad, da Barr. Maryam Abdullah Fulani.
Barr. Maude ya umurci kwamitin da ya mika rahotonsa nan da Talata, 14 ga Oktoba, 2025, tare da cikakken bayani da shawarwari masu amfani domin tabbatar da gudanar da shari’a cikin adalci da gaggawa.
“Jinkirin hukunci tamkar rashin adalci ne,” in ji Kwamishinan Shari’a. “Mun kuduri aniyar ganin cewa babu wanda zai cigaba da zama a gidan yari ba tare da bin ka’idar doka ba, kuma kowace shari’a ta samu kulawar da ta dace.”
A nata jawabin, Shugabar Kwamitin, Barr. Rabi’at Sa’ad, ta gode wa Kwamishinan Shari’ar bisa zabo su da ya yi domin yakinin da yake da shi a kan su, sannan ta tabbatar da cewa kwamitin zai kammala aikinsa cikin lokacin da aka ware kuma zai yi fiye da tsammani wajen tallafawa shirin sauye-sauyen da Ma’aikatar ke aiwatarwa.
Manufar kwamitin ta hada da gano fursunonin da s**a daɗe a gidan yari ba tare da gurfanar da su a kotu ba, gano fayils din shari’a da s**a bace, da kuma tantance yadda kotuna ke bin ka’idojin doka. Haka kuma, kwamitin zai gabatar da shawarwari don inganta hadin kai tsakanin masu gabatar da kara, hukumomin gyaran hali, da kuma bangaren shari’a.
Barr. Maude ya sake nanata kudirin Ma’aikatar na tabbatar da adalci, gaskiya, da nuna amana wajen gudanar da shari’a a jihar Kano. Ya kuma yi kira ga alkalai, lauyoyi, da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren shari’a da su ba kwamitin hadin kai domin tabbatar da cewa an gudanar da adalci yadda ya kamata.
📸 Amir Abdullahi Kima
Senior Special Reporter Ministry of Justice Kano State.